Sashe 50
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
nata ya sake kalla, kawai a take sai ta ga ya nufota gadan-gadan zai kamota zuwa garesa wanda hakan ya sanya ta jaa baya sosai sai kuma ta durk ushe a wajen da sauri da niyyar k ame jikinta waje guda sai dai bata samu damar yin hakan ba ta mik e tsaye zumbur! Sakamokon chakar gefen mararta da tsinin kan wuk ar ya yi a take kuwa jini ya fito ya zirara k asa har cikin pant d inta. Sai a lokacin ta tuna abunda ya kawo ta dan haka ta yi ta maza ta kawar da tsoro ta zaro wuk ar ta yi kansa. Da mamaki yake kallonta dan ko rik e wuk ar ma ba ta iya yi ba. Bai ankara ba ya ji ta kawo masa sara tana tangad i sarar da ya tabbata ko b era idan ka yiwa ita to dole ya yi maka gwalo ya gudu dan ba ka isa ka same shi ba yayinda ita kuma a nata b angaren k arshen bajintar kwarewarta kenan. Dan a zuciye take matuk Hannunta kawai ya rik e ya matse ya tsaya yana binta da wani irin kallo kamar zai cinyeta d anya. Azaba da fin k arfi suka sanya wuk ar ta fad i daga hannunta amma still bai cikata ba sai ma janyota da ya yi izuwa jikinsa ya rungume wai ko zai samu sassauchin abunda yake ji. Sai dai kuma hakan da yayi sai ya zame masa kamar ya barbad a gishiri ne a kan gyambo. Ihun da ta tsala sai da ya Isar masa har dodon kunnesa rau! Ya dira a tsakiyar kansa amma sam ba shi da niyyar cikata dan zuwa yanzu ya fara rasa hankalinsa ma sakamokon laushin jikinta wanda yake nan kamar na mage da ya taimaka matuk a wajen hautsina masa dukkan lissafinsa. ofar gidan ya ji an yi ba tare da ya san me yake yi ba kawai ta ga ya mik a hannu zai bud esu a hakan ba tare da ya cikata ba sai ma sake ruk ota da ya yi k am! Da hannu d aya. Dukkanin k arfinta ta saka wanda kwayar da ke yawo a jikinsa da mutuwar da jikinsa ya yi suka taimaka mata ta samu damar ingijesa kawai ta afka cikin d akin dai-dai Tiger ya turo k ofar. Tabbas ihu ya ji yanzu kuma ya ga Mallan Idi yana lek e a jikin k ofar sai dai yanzun shi kad ai ya gani. Kallon da ya ga yana yi masa ne ya sanya kawai ya juya ya fita ya koma chaan lungu inda ya baro ya ci gaba da zaman gadinsa har zuwa lokacin da zai fito. Shiruuu ya yi dan ya fi mintuna uku dafe da kansa kafin chaan ya yi tsaki kawai ya juya ya nufi cikin d akin nasa. Yana tura k ofar ya ja ya tsaya sakamokon hangota da ya yi wanwar a tsakiyar d akin dan tunda ta shigo ciki kanta ya juye ta nemi hanyar fita ta rasa kwayar ta fara yi mata rawar disco a ka gashi an kawo wuta fanka ta sake rura wutar d akin ya sake yin turnuk Shi kansa yana shigowa cikin d akin abun ya ci k arfinsa, duk yadda ya so tab uka wani abun kasawa ya yi a take ya tafi ya zube ya fad a a gefenta sangalalin k afarsa ya bugu da nata sosai. Maman Sagir tana zaune a d akinta ita kad ai tun d azu duk cases d in da ake yi ta k i fitowa. Ta ci kuka har ta gaji ta godewa Allah...A ko da yaushe idan ta runtse ido Iyya kawai take gani d azu da safe da take ce mata Allah ya d aurawa Kamal irin k addarar Sagir! Hankalinki ya kwanta yanzu? Ji take kamar ta binne kanta dan ta san har abada Iyya ba zata tab a mantawa da ita ba. Tana zaune ta ji hayaniya ta fara tashi sama-sama sai kuma gidan ya hautsine gaba d aya. Sai da ta fito tukunna ta fahimci wai ashe Dije ake nema, itama zuwa yanzu duk ta yi laushi dan haka ta shiga aka dinga neman da ita Sune har k arfe goma sha biyun dare suna zagaye unguwa uku amma babu Dije babu dalilinta! Idan ka ga Inna sai ka yi mata kuka duk rashin tausayinka dan kamar wata tab iya haka ta koma, wannan dalili ya sanya bayan an sanar da y an sanda sun fara binciken neman Dije da Aminu su Maman fati suka bita asibiti wajen Ya Muhammad suka kwana da ita dan ita kanta patient ce ballantana ace zata ji da wani. Da ikon Allah a daren Ya Muhammad ya bud e idonsa sai dai bai kai ga fara gane mutane ba gashi Likitansa ya fad a ya sake fad a tabbas kar a d aga masa hankali ko a b ata masa rai. Ba dan asibiti ta so ba sai dan babu taimakon da za su iya yi musu dan ba su da ko sisi, kuma kud in komai ya k are hakan ya sanya aka sallamo su washegari da sassafe suka dawo gida da shi, wanda da Kaka ta ji sallamarsu sai da ta kusan had iyar zuciya ta mutu dan ita Addu arta kar Inna ta dawo duk da dama ce mata akayi idan ta fita da fushi ko da niyyar Yaji ko barin garin ne to ta tafi har abada amma sai da ta saka ran Allah ya sa wannan fitar da ta yi ta jiya ta zamana ba za ta dawo d in ba. Sai gashi da ikon Allah sun dawo da sassafe kuma har da Ya Muhammad. Ba su dad e da zama ba aka aiko ana sallama da Mallan. agowa Inna ta yi ta kalli d an aiken kafin ta ce masa je ka ce baya nan, ya yi tafiya. Fitar Yaron da kamar minti uku sai ga Babansu Fati ya shigo tare da Mallan Idi. Zuba masa ido duk suka yi suna ji kamar su rufesa da duka, amma ganinsa tare da Baban Fati ya sanya suka d aga k afa kawai suna jira su ji me ke tafe da shi amma fa bayan sun gama ji tabbas sai sun yi masa walmukalifatu yau idan ba su sumar da shi ba kenan! Da gudu Umar ya fito daga cikin d akinsu jin muryar Mahaifin nasa. Bayan ya gama yi masa oyoyo ya bashi jakarsa ya ce ya kai masa d aki ya dawo ya d auki jakar bakkon da ya zo da ita itama ya kai masa ita ciki. Hakan kuwa aka yi sai da Yara da y an matan suka gama yi masa sannu da zuwa tukunna ya kalli tsakar gidan ya sallami duk wani Yaro har su Rakiya duk ya ce su shiga ciki sannan ya kalli su Inna ya ce Ya muka ji da hak uri? A take kamar masu jira duk suka fashe da kuka dan ya tab o musu inda yake yi musu k ayi. Sai da ya barsu suka d an rage nauyin dake a zuciyoyinsu ya yi musu ta aziyya tukunna ya juya ya kalli Mallan idi ya ce masa ilaika! Sunkuyar da kai Mallan Idi ya yi sai kuma ya fashe da kukan da tun shigowarsa bai yi sa ba sai yanzu. Tsaki Asabe ta yi ta mik e za ta bar wajen ta ji ya fad i maganar da ta sanya ta ja ta tsaya babu shiri. Tabbas zarginku gaskiya ne. Ina mai baku hak uri d ana shine ya aikata duk abunda kuke zargi, d azu na ji yana waya Dan Allah ku yi hak uri Allah ya ji k an waenda suka rasu. Shiruuu duk suka yi har Kaka wadda ta fito da niyyar korarsa. Sai kuma suka hau kallon-kallo ita da Asabe kafin su mayar da hankalinsu ga Mallan Idi kacokam. Durk usawa ya yi a kan guiwowinsa yana kuka ya had e hannuwansa waje guda ya ce da ni da Mahaifiyarsa muna yin iyaka bakin k arinmu amman abun ya fi k arfinmu ne, tamu k addarar kenan, ni kaina yanzu haka wasar y ar b uya nake yi da shi saboda Mahaifiyarsa ce kad ai ta sanya ya barni da rai na dan tun wani fad a da muka tab a yi da shi lokacin yana Yaro shikenan tun daga nan ya k ullace ni yanzu kuwa da babu idonta na san kashe ni abu mai sauk i ne a wajensa dan ya ci alwashin yin hakan. Yanzu ma garin zan bari tunda Allah ya sa na warke har zuwa lokacin da Allah zai tashi kafad unta tukunna in dawo, amma sai na ga bai kamata in wuce haka nan ba tare da na zo na sanar da ku abunda idanuna suka gane min kunnuwana suka jiye mini ba. Sai da ya koma ya gyara zama ya jaa numfashi ya fesar tukunna ya ce Na san kuna ta neman y ar ku Khadija wadda yake ta faman kashe-kashe saboda ita ko? A take hankalin kowa ya sake karkata garesa yayinda k irjin Inna ya shiga dukan uku-uku numfashinta ya fara kakkatsewa ta shiga addu ar Allah ya tsare ta da mugun ji da mugun gani dan tabbas ba ta jiyo k amshin alkhairi a tattare da maganar da Mallan Idi ya kwaso ba. Sai dai a yi hak uri Halima dan mai afkuwa ta riga ta afku Muryar Mallan Idi ta dirar mata kamar dirar Mikiya a k ahon zuciyarta. Tsoro da tashin hankalin rashin jin k arshen zancensa ne suka sanya kawai ta fashe da kuka, cike da fargaba Ramma ta ce ka ga dalla chan Mallan idan zaka yi magana kanka tsaye ka bar kwana-kwana to ka yi! Haba mana..ka zo sai ja mana rai kake yi bayan ka san halin da muke a ciki so kake yi zuciyoyinmu su buga kafin ka gaya mana me ke faruwa? Wani kalar kallo Baban Fati ya yi mata wanda hakan ya sanya ta kawar da fuska tana ta faman harare-harare. Fashewa da kuka Mallan Idi ya yi sannan ya ce in da ace ina da ikon kwatar Yarinyar nan