← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 59

Sashe 4

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

arya da sharri har da cewa da Ma a ya janyo Dije sai da ya rungumeta ya shafa mata k ugu tukunna da kyar ya Aminu ya finciketa daga jikinsa Wata y ar budurwa tsarar Dijen ce a wajen ta ce Anya kuwa A bu wannan ba k arya kike yi ba? Nan kuwa ta hau rantse rantse matan gidan suna tayata da cewa Ai A bu ba ta k arya, tunda ta fad a to an yi hakan Babu wanda ya ga tahowar Dije sai ingije jama ar wajen da ta ke ta faman yi wajen k arin ganin ta isa ga A bu ne ya fargar da wasu. Kafin su ankare kuwa har ta isa ta finciko wuyan rigar A bu! Bata yi wata wata ba ta d auketa da Mari ji kake tasss!!! Dama a zuciye take ranta a b ace yake. Cike da masifa uwar A bu wadda take wajen ta fara zaginta tana kai mata duka sai dai cunkoson mutanen wajen bai sanya dukan ya shafeta ba. Cikin lokaci k alilan waje ya hautsine dan Dije ta damk i wuyan A bu kamar mai shirin aikata lahira tana danna mata ashar ta uwa ta uba tana kiranta da mak aryaciya tsinanniya Wata uwar tsawa aka daka Dije!!! Wanda hakan ya sanya kowa ya sha jinin jikinsa yayinda wasu kuma suka hau k uni musamman mahaifiyar A Da mugun k arfi Dije ta runtse idanunta dan bata so Allah ya kawo mai raba ta da A bu ba a yau d in nan! Yarinyar ta sha k ulla mata munafurci kala kala dama tun ba yau ba. Ita babban abunda ya fi k ular da ita ma shine shafa mata k ugun da aka ce wai Ma a ya yi! Mutumin da ta tsana kamar mutuwarta Za ki cikata ko sai na k araso??? Shiruu haka wajen ya d auka baka jin k arar komai sai na sheshshek ar kukan A bu wadda hatta bakinta ya fashe. Tana haki tana huci zuciyarta a wuya ta cika ta ta d an ja baya ta sunkuyar ta kanta k asa tana k arin hana kanta kuka dan kwata kwata dukan da ta yiwa Abu bai gamsar da ita ba. Wuce ki tafi d Ya ce da ita idanunsa a kanta. Allah gafarta Mallan gaskiya yau dai sai an bi mana hakkin mu Mahaifiyar Zainab ta fad a tana kallon gefe tana harare harare. Ba tare da ya kula ta ko ya kalli inda take ba ya juya ya bar wajen ya nufi k ofar d akinsa dake a soro. Ido ta had a da Ya Muhammad tsaye a gefen Ya Kamal wanda ya rakota gidan duk sai ta ji babu dad i. Mallan yana wucewa Ya Muhammad shima ya juya ya bi bayansa yayinda Ya Kamal ya k araso wajen ya ce Inna bata da lafiya haka Minu shima kuma duk a ta sanadiyyar ki ne amma kalli abunda kika sake aikatawa. A harzuk e Mahaifiyar Zainab ta ce yo ai gada ta yi! Ka ga laifinta? Ai ta san tana da d aurin gindi ta ko wanne b angare ne shiyasa take abunda ta ga dama, to dai gashi maza sun fara latsata kuma gashi ba a son laifinta dan haka ban san yaya zata kaya ba! Mu dai Allah kiyaye mu da ganin abun kunya. Cikin fushi Dije ta ce uwark. Da sauri Ya Kamal ya ce Au Allah??? Da k arfi cikin katseta sannan ya ce wuce ki tafi kafin in yi ball da ke a wajen nan wallahi. Ba dan ta so ba ta juya ta wuce cikin d akinsu inda Inna take jinya amma wallahi ta ci alwashi sai ta mayar wa da Asabe martani tunda ita dai bata san ya kamata ba Haka nan ta shige d akin tana jinsu ita da y an koron ta suna ta yayata maganar suna sake assasa abun. Turuss!! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido biyu da ta yi da Inna a zaune Anty Sakina tana yi mata allurar jijiya. Da sassarfa ta Isa gareta tana duddubawa kafin ta d ago idanunta da har sun d an sake kad awa ta ce Inna jikin dai? Sannu. Jinjina mata kai kawai Inna ta yi tana mai sauraren zage zage da d ibar albarkar da Asabe take zubawa har yanzu, gashi sai aibanta Dije take yi ana ta mayar da magana ana cewa a ya rungumeta ya shashshafeta yau d ita kuma tana sake rurawa abun wuta tana sake d abbaka zancen. Ya Muhammad ne ya shigo cikin d akin hannunsa d auke da wani kwano wanda Mallan ya gama tofi a cikinsa yanzun ya ce ya kawowa Inna ta sha. A gabanta ya durk usa sannan ya mik a mata ya ce gashi in ji Mallan. Jinjina kai ta yi ta ce ya ake ciki da al amarin Aminun? Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauk e kafin ya ce ban je ba tukunna, ki kwantar da hankalin ki zai samu lafiya in sha Allah. Jinjina kai kawai ta yi dai dai nan Sakina ta gama juye mata ruwan allurar a cikin jijiyar ta ta zare sannan ta fara k arin tattare kayanta, sai da ta had a komai tsaff tukunna ta sake yiwa Inna jaje tare da addu ar neman sauk i daga nan ta mik e ta fita. Tunda ya Muhammad ya shigo cikin d akin Dije take ta faman sunne kai kamar wata ta kirki. Sakina tana fita ya zuba mata manyan idanuwansa farare k all kawai yana kallonta ba tare da ya ce mata komai ba. Kusan minti d aya suka kwashe a haka ganin bashi da niyyar yin magana ya sanya ta magantu da kanta, ta ce dan Allah ka yi hak uri, Inna ku yi hak uri ba zan sake ba Ba zaki sake me ba? Ya jefo mata tambayar idanunsa a kanta. Inda inda ta fara yi kafin ta ce duka biyun. Ajiyar zuciya ya sauk e sannan ya ce jiya jiya aka gama case d inki da Kaka, damuwa ta haifarwa da Inna ciwo amma kalli yau ma issue har biyu Dije duk a kanki ke kad ai? Idan an yi magana ki ce kina son mu kina tausayinmu, an ya kuwa Dije?? Hawaye ne suka shiga sintiri akan fuskarta da kyar cikin jan hanci ta ce sune fa suke tsokanata uraa mata ido ya yi na y an mintuna kafin chaan ya ce ko da wasa kar in sake ganinki a nesa da Ma a ma ballantana kusa da shi! A hankali ta ce Yaya shine fa ya tare min Shiiii ya ce da ita yana mai d aura hannunsa a kan lips d insa kafin ya ce abunda na fad a kenan Daga haka ya fara k arin mik ewa yana mai cewa Inna bari in je wajen Minu. Duk sai a lokacin suka lura da yadda sam hankalinta baya a kansu kwata kwata. Lumshe idanuwa ya Muhammad ya yi ya bud e kafin ya ce Inna dan Allah ki rabu da su kar maganar su ya dame ki Ai dama kina ganin yadda take kumbura kwana biyun nan kin san akwai dalili! Shegiyar Yarinya ashe latseta ake yi bamu sani ba! Ta fito tana ta juya mana mazaunai ita nan ga mai diri nan kuwa ba na Allah da Annabi bane ba Muryar Asabe ta ratsa kunnuwansu. Zurufff! Inna ta yi ta mik e tsaye, da sauri ya Muhammad ya runtse idanuwansa, kafin ka ce kwabo har ta fice waje BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 02. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Inna tana fitowa wasu suka yi shiru yayinda Asabe ta ci gaba da magana kanta tsaye tana aibanta Dije. Cikin mad aukakin b acin rai Inna ta ce sannu tambad iya wadda ba ta san ya kamata ba! Yanzu ke abinda kike yi tarbiyyar kenan? Kin tara Yara da muna manyan cikin gida sai zancen batsa kuke yi a gaban Yara k ananu, haka ake tarbiyyar a garin ubanki? Da sauri Asabe ta ce a kul d inki Halimatu! Wallahi a k ul d in ki!! Kar ki kuskura ki sake ambato mini iyaye da k azamin bakinki, sannan ai gara mu zancen batsa da iskancin muka yi ba aikata shi muka yi da jikinmu ba. Daff da ita Inna ta matsa sosai ta ce waye ya aikata iskancin? Waye d an iskan??? Ta yi mata tambayar cikin tsattsareta da manyan idanuwanta tana huci dama tun jiya take neman wanda zata sauk ema takaicin Kaka a ka. Duk tsageranci irin na Asabe tana shakkar Inna, ta san sarai yanzun sai ta lakad a mata dukan mutuwa ba k aramin aiki ta bane ba yin hakan, dan haka sam sai ta gagara ambatar sunan Dije kamar yadda ta yi niyya taketa kuma fad a tun d azun. Sai kawai ta yi tsaki ta juya ta shige cikin d akinta zuciyarta fal takaici, ga abunda Mallan ya yi mata a kan Dijen yanzun sannan gashi ita da kanta ta yada kanta a gaban mutanen gidan ta sake bawa Halima girma a idanunsu tunda dai gashi k iri k iri ta gagara tanka mata. Ki dawo ki tanka mana! K aramar marar kunya k aramar munafuka. Ku kuma y an koronta munafukai mu zuba da ni da ku a cikin gidan nan kar ku fasa fita daga harkata ni da y ana wallahi wahala za ku sha Da sauri wata y ar kyamurmurar mata (Maman Fati) ta ce Wane mutum! Ai ko giwa ta fad i ta fi k arfin kiyasai su ja gawarta. Su Maman Sagir ne dai y an koronta amma mu ai mun san dai dai mun kuma san gaibu. aya bayan d aya aka fara watsewa bayan kusan rabin matan da suke tsakar gidan sun taru sun taushi Inna sun nuna mata su babu ruwansu kamar ba da su aka gama gutsiri tsoma a tsakar gidan yanzun nan ba. Asabe tana ciki tana ta kwafa tana lissafa mutanen da suke ta bawa Inna hak uri suna cewa ta rabu da Asabe ba sa ar ta bace ba, kar ta bari ranta ya b aci saboda Asabe Tana aiyyana kalar yadda
Chapter 4 · 0% Book details