Sashe 22
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai kuwa sai gashi ya turo mata message Akan yana neman yardarta zai kwan a chan, Minu ba zai iya rik e Ya Muhammad shi kad ai ba, yanzu haka fama ake yi, gashi Ya Kamal ba ya kusa yau d in ballanta ya yi tunanin zai ce za su kwan tare. Idan har ba ta amince ba to ta sanar masa da wuri ya san abinyi. akin Kaka ta je ta kai mata k orafi dan haka a take suka gama yanke hukunci. Dare yana yi ta shirya tsaf da ikon Allah ta wuce zuwa asibiti. Minu yana zaune Mallan yana yi masa fad a akan abunda ya ji labari ance ya yi a gida d azu Ya Muhammad kuma yana bacci kawai suka ga Asabe a kansu. Da farko Mallan ya d auka dubiya ta zo sai kuma ya ga yanayin lokaci da yanayin fuskarta dan haka ya san ba alkhairi ne ya kawota ba, gabansa ne ya yanke ya fad i a lokaci guda kuma ransa ya b aci a lokacin da kwakwalwarsa ta bashi watak ila shirunta ba yana nufin ta amince bane ba, dan shi har ga Allah ya yi tunanin ta amince ne tunda ya ce idan bata yarda ta yi magana da wuri sannan ya san in da ace Asabe ba ta amince ba to da tuni ta kirasa ta ce ya riga ya san halin abarsa, to amma kuma gata yanzun ta zo masa dan haka sai kawai ya tsaya ya ga ikon Allah. Da kyar ta iya gaishesa ciki-ciki dan Kaka ta ce mata kar ta kuskura ta raga masa, ko gaisuwar Minu ba ta amsa masa ba ta ce bamu guri. A hankali ya mik e ya fice daga wajen shima yana mai mamakin al amarin. Kunya ce ta lullub e Mallan tashi d aya had e da b acin rai, gani yake yi kamar duk jama ar d akin sun san dalilin zuwan Asaben tunda dai ta yi k anta ace ita ce Mahaifiyar Ya Muhammad. Saboda Allah meye na biyosa har asibiti abunda ya kamata a Muryarta ce ta katse shi gashi ta fad i haka tana mai mik o masa wayarta. Sunan Kaka ya gani b aro-b aro a kan screen d in wayar ga timer yana tafiya alamun ita ce a kan wayar. Ajiyar zuciya ya sauk e ya saka hannu ya karb a cikin sanyin murya ya ce Assalam alaiki Ameen kawai ta ce daga haka ta d aura da Ga Asabe nan zata taya ka jinyar! Dan na ga take taken Halima da y ayanta waenda ciwonsu ba ya tashi sai ranar kwanan Asabe tsaff idan aka biyesu sai sun haramta mata keb ewa da kai! Ka tafi asibiti baka sanar da ita zaka dawo ko bazaka dawo ba Yarinya tana ta jiranka salon ka ja mata magana da gori a cikin gida, shiyasa na ce mata ta shirya ta biyoka ku yi jinyar tare idan kwanakinta suka k are sai ta dawo kuma wallahi idan na ji ka yi mata ko da kallon banza ne za mu had u da kai! Sannan magana ta biyu yau Halima har sunana ta ambata ta gaggaya min magana kuma ta yi mini tsaki duk a kan y anta, da farko na shirya ne akan zan tafi amma sai na ga idan na yi hakan ita ce da riba dan haka kana dawowa gobe ka san abun yi y ar nan tata da take hauka saboda ita wallahi sai ta bar gidanka idan kuma ba haka ba to wallahi Allah sai na tsine maka, ka ji dai rantsuwar musulmi Da k arfi Mallan ya runtse idanuwansa ita kuma tana gama fad in haka ta kashe wayarta Daren ranar Mallan bai runtsa ba dan ya shiga tsaka mai wuya matuk a ga y arsa ga Mahaifiyarsa ga kuma matarsa wadda yake tsanani so da tattali dan ya san korar Dije a gidansa dai-dai yake da rabuwar sa da Halima. Kafin asuba shima sai da aka jona masa nashi drip d in sakamokon jininsa da ya yi mugun hawa, dole haka aka kira Minu wanda aka cewa ya tafi gida jiya, ya dawo yana jinyar su su biyu Asabe kuma tana kallonsu kawai dan ko wanka ta k i ta je gida ta yi so take sai rana ta take kowa ya hallara a gidan tukunna za ta shiga dan kowa ya gani ya shaida a asibiti ta kwana wajen Mallan, kuma a tsakar gidan zata shaidawa Halima Mallan d in bashi da lafiya duk dan dai a ga darajarta tunda Mallan d in bai gaya mata ba sai a bakinta za ta ji, dan ta ci sa a wayar Minu ta mutu tun da ya zo da asuba babu chaji kuma asibitin babu wuta, ita kuma ta d auke wayar Mallan d in tana ganin kiran Haliman ta dinga rejecting ta ga kuma message d inta Assalam barka da asuba ya jikin Muhammad an ce kai ka kira Minu d azu ya taho Allah ya sa dai lafiya shima ta na gama karantawa ta goge. Tun sassafe ya tashi yau sab anin yadda yake kullum dan a k aidarsa idan ya dawo daga sallar asuba komawa yake yi ya kwanta sai 11 tukunna ya ke tashi. Tana kitchen ta ga ya shigo cikin gidan daga d akinsa wanda yake a soro, sai da ya sake gaida ita tukunna ya shiga kitchen d in ya sauk e mata tukunyar da take k arin sauk ewa, wanda tunda ya kama tukunyar take ta cewa a fa! Amma sai da ya ajjiyeta a k asan tiles d in kitchen d in. Ajiyar zuciya ta sauk e sannan ta ce ni dai na san kai ba sharifi bane ba amma ban san tayaya kake iya shanye zafi ba. Wani murmushi ya yi wanda ya tsaya a iyaka k irjinsa sai kuma hucinsa da ya fito amma ko yanayin fuskarsa ba ta nuna ba, cikin muryarsa wadda ta ke a nutse sannan cike da izza ko da yaushe ya ce ba wai zafin ne ba na ji ba, Ina ji! Kawai dai na kasance mutum mai iya had iye abu tun zamanin mugun ubana. Turuss! Ta yi ta tsaya daga k arin bud e kantar kitchen d in da take yi. Sun d an jima a haka ita bata juyo ba shi ma kuma bai sake cewa komai ba kafin a hankali ta juyo ta zuba masa ido, itan yake kallo yana karantar yanayinta a hankali ya ji ta ce ba zan gaji da baka hak uri ba Ma aruf! Rashin saka idon da na yi yana daga cikin abubuwan da suka bayarda gudunmawa wajen Da sauri ya k araso inda take ya d aura yatsansa guda d aya a kan bakinta ya ce shiiii, Uwa ba ta laifi, sannan k addarata a rubuce ta ke Maama, ba ki da wayon da zaki kub utar da ni daga abunda Allah ya riga ya k addara zai same ni, a haka k addarata ta zo dan haka dole duk wayon mu sai na bi ta hakan Ajiyar zuciya ta sauk e za ta sake yin magana ya ce ki manta da abunda ya faru ya wuce Yau zan fara sana a ki saka min albarka sannan akwai abunda nake ta so in gaya miki Sake mayar da gaba d aya hankalinta ta yi garesa ta ce Allah ya sa ka fara a sa a, dan Allah a kula banda fad ace-fad ace sannan yadda na ga sauyin nan a tattare da kai dan Allah ka zauna a haka Ma aruf ka daina wachchar rayuwar ka barta har abada hakan sai ya fi komai saka ni farinciki. Shiruu ya yi kafin a hankali ya runtse idanuwansa dan yau d innnan ma yana da operation d in da ba zai tab in yi ba, kamar dole yake a wajensa kuma ya san definitely sai an zubar da jini kacha-kacha ma kuwa sannan in ba da kyar ba a buge zai dawo mata gidan dan ya san babu ta yadda zai yi ya iya yin nasara a aikin dole sai ya sha wani abun Wacce maganace kake so ka yi da ni??? Muryarta ta katse masa tunani. Kansa yana a k asa sosai ya sunkuyar, sai da ya daidaita yanayinsa tukunna da kyar ya d ago ya d anyi murmushi dan zancen nata ya taimaka wajen sanyaya masa ransa. Kamar an fisgi maganar daga bakinsa ya ce aure na ke so in yi in sha Allah Ya san cewa wannan ita ce kalma mafi soyuwa da Maama take burin ta ji ya ce mata amma dukda haka sai da ya yi mamakin yadda ta rushe masa da kukan farin ciki lokaci guda. Murmushi ya yi mai sauti a hankali ya matasa sosai gareta ya rungumeta zamewa ta yi ta saita gabas ta yi sujjada tukunna ta mik e ta kamo hannuwansa ta rik e ta ce Allah ya sa matar ka ce har a gidan Aljannah a hankali ya ce ameen ta sake cewa Allah ya sa albarka da alkhairi a tarayyarku sosai ya yi murmushi ya sake cewa Ameen Cike da zumud in son jin kwakwaf Mallan Idi wanda shigowarsa kenan ya ce Ahh ma sha Allah suruka muka yi ne? A take annurin da ke a fuskar Ma a ya d auke lokaci guda, a hankali ya zame hannunsa da ke a cikin na Maama ya juya ya fice daga kitchen d in gaba d aya. akinsa ya koma ya d auki bokiti ya fito ya zo bakin tap ya d ebi ruwa dan ruwan band akin sa ya lalace tun shigar Oscar da ya yi a gigice ya lalata fanfon da shower, ya daina zuwa, dai-dai Mallan idi ya tsare Maama yana ta jero mata tambayoyi akan a ina Yarinyar ta ke shi kuma Ma a ya fito d ibar ruwan. Kallo d aya kawai Ma a ya yi masa ya d auke kai tun daga nan ya sha jinin jikinsa har Ma a ya fito daga wanka ya zo ya ci abinci ya fita Mallan idi bai sake cewa komai ba. Tun k arfe bakwai su Oscar suke tsaye a k ofar gidan