← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 59

Sashe 18

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Astaghfirullah har yanzu ban ga wani chanji a tattare da kai ba Ma aruf Ta yi maganar tana mai dag owa ta kallesa sosai shima itan yake kallo da taimakon hasken kwan fitilar solar da ya mamaye koina a cikin d akin. Ya jima yana kallonta haka itama kafin chaan ya furzar da huci ya d auke idanuwansa daga gareta ya ce a shirye nake, Allah ne bai baki ikon kallona ta fuska mai kyau ba! A ko da yaushe a baibai kike kallona Maama Ya k arashe maganar yana mai mayar da dubansa gareta. Wanne kallo kake tunanin zan yiwa mutum irinka? Ma aruf kalli jikinka! Kalli yanayin rayuwar da ka zab arwa kanka kalli mutanen da kake huld a da su sannan duk fa yawancin fad an da ya shafi siyasa sai an ganka a wajen kuma har da kashe-kashe abun yake k unsa ka kuwa san makomarka Ma aruf? Ta yi maganar muryarta na rawa alamun gab take da fashewa da kuka. Mugu d an daba kawai!!! Muryar Dije ta yi flashin cikin kwanya da kunnuwansa kamar yanzun take fad Cikin rauni d aci da jin zafin abinda za ta furta d in ta ce A ko da yaushe idan na tuna abubuwan da ka yi kuma na tuna ba ka da mafita ko wayon kare kanka a gaban Ubangiji tare da nauyi da girman zunubin ina shiga cikin matsanancin tashin hankali Ma aruf! Ka ce min ba ka da laifin komai in yarda da kai na zab i in yarda da kai d in sai dai kuma ba ni da hujjar da zan ce gata saboda ita na yarda da kai, Ina ganin kaina ne kawai a matsayin uwa mai tsananin son kai wadda son kanta zai kaita ga halaka saboda ba kai kad ai ba hatta ni inada nawa kamashon Maganar tata ce ta mak ale sakamokon kukan da ya ci k arfinta. A hankali ya sauk e ajiyar zuciya yana jin wani zafi yana taso masa, da kyar ya iya d aga d aya hannunsa ya sakata a jikinsa ya rungume, cikin sigar lallashi yake bubbuga bayanta Sun d an jima a haka kafin chaan! Ya sauk e wani nannauyan numfashi ya ce ga balangu nan, na wajen Ganaye, wanda kika fi so. Ya k arashe maganar da d an murmushi a kan fuskarsa. Ta riga ta san maganar ce baya so kuma tunda ya sako wata to an bar wacchan kenan har abada. Kallon ledar da ya mik o mata ta yi kamar kullum ta ce a ina ka samu kud Murmushi ya yi kafin ya ce ta hanyar halal, doyata dana gaya miki mun noma a Niger ita aka siyar Cikin tarar numfashinsa ta ce an dad e fa ana baka kud in doyar nan Ma aruf Numfashi ya fesar sannan ya ce sun kusan k arewa saura kad an bai kai dubu ashirin ba ma Daga nan ya yi shiru kamar mai tauna abin da zai fad a kafin ya ce Sana a zan fara da kud in da wanda na baki ajiya, in sha Allah Wani irin zabura ta yi sai kuma ta fara murmushi mai had e da dariya kafin ta gyara zamanta tukunna ta yi sujjada. Murmushi sosai shima ya yi wanda idan ba yana tare da ita d in ba to ba za ka tab a gani ya yi ba. Bayan ta d ago ta gyara zamanta cike da farin ciki ta kamo hannunsa ta ce Allah ya dafa maka Allah ya taimake ka Allah ya sa ka fara a sa A hankali ya ce Ameen Ana fitowa daga masallacin sallar asubah Mallan da Minu da wasu samari a gidan guda biyu Ya Kamal da Ya Musa suka tafi kai Ya Muhammad asibiti dan zuwa wannan lokacin jikin nashi ya yi tsanani sosai. Tunda suka tafi Inna take kuka gashi ta cewa Dije ko inda ta ke kar ta kalla ballanta ta yi mata magana .sosai ta bawa mutanen gidan tausayi yayinda wasu suke ta jin dad i kar ma Kaka da Asabe su ji labari. Sai wajajen k arfe goma tukunna Mallan ya amsa wayar Inna ya ce mata jikin da sauk i an d an samu kansa yanzu haka an yi masa allurar barci baccin yake yi, ga Minu za su dawo tare da su Ya Kamal, ta bashi karin kumallo ya kai akwai maganin da dole sai ya ci abinci tukunna zai sha ta amsa tana ta jera hamdala ta mik e ta nufi kitchen, tana shiga ta tarar da Dije tanata jefa d anwake. Yi ta yi kamar ba ta ganta ba kawai ta juya ta fice a kitchen d A hankali kwalla ta shiga zirya saman kyakkyawar fuskarta dan idan akwai abinda bata so a duniyar nan to shine Inna ta yi fushi da ita, gaba d aya ji take yi duniyar ta tsaya mata chak .Inna bata saba yin fushi da ita ba shiyasa a duk lokacin da ta yi take jin jiki. Sai da ta gama jefa d anwaken tass tukunna ta d an zuba mai a kasko ta rufe ta ajjiye roba ta je ta d ebo ruwa shima ta ajjiye tana jira ya gama ta kwashe. Ganin zai d auki lokaci ya sanya ta mik e ta fita ta wuce d akinsu domin ta je ta d auko albaasa yadda tana sauk an waken sai ta d aura man, dan rushon gawayin su ya samu matsala, da abin girki d aya suke amfani kwana biyu. Tana fita dede Asabe tana fitowa daga band aki, ita Asaben ta ganta amma sam Dije ba ta ganta ba da yake baya ta bata. Kwafa Asabe ta yi dai-dai Dije ta shige d akinsu, ta san ta tsani Halima kuma tana kishinta amma zuwa yanzu tabbas tsanar Dije tana shirin kere ta Halima a cikin zuciyarta, sosai take jin zafin Yarinyar tana k arasa fitowa tsakar gidan idanunta suka sauk a a dede wajen da ta zo ta tarar da gawar akuyarta wanda Maman Fati ta tabbatar musu aikin Dijen ne, wani irin tuk i ne ta ji yana taso mata..Kaka ta ce kar ta yi mata magana zata yi maganinta ta hanyar sakawa a koreta a gidan amma shiru yau ma gashi har ta kwana ta hantse babu alamun zata bar gidan!.. Kitchen d in ta juya ta kalla ta ga tukunyarsu a kan murhunsu wuta tana ta ci, ba ta yi wata-wata ba ta afka cikin kitchen d in zuciya tana cinta ta shiga ta lek a cikin tukunyar urawa d anwaken da yake ta tafasa ido ta yi, tana cikin tunanin me zata yi masa ta lalatashi idanunta suka sauk a a kan uban ruwa k anwa kusan cikin babban kofin sha biyu a cikin wata babbar roba, da sauri ta d auka ta juye duka a ciki har da k asa k asar ba ta rage komai ba, hankalinta bai kwanta ba ta sake d aukar gishiri shima ta juye a ciki ta saka ludaye ta juya sasai kamar mai burge miya sannan ta mik e ta juya za ta fita suka ci karo da Dije. Wani Irin tururin wutar bala i ce take taso mata amma ta danne da mugun kyar dan ko saboda Ya Muhammad ba zata yarda ta kula kowa a gidan ba yau! Tsaki Asabe ta yi tana jira Dije ta tanka ta ita kuma ta tada bala in da kowa sai ya ji ko dan a sake aibanta Dijen amma ga mamakinta sai ta ga Yarinyar ta wuceta ta d auko tsumma ta d auki tukunyar d anwaken nata ta fice ta nufi bakin rijiya. Da kyar ta samu kaso biyu a cikin ukun d anwaken da ta jefe shima kuma duk ya yi laushi, dan kanwar mai k arfi ce sosai hakan ya sanya d anwaken zagwanyewa Tana cikin wankewa Minu ya yi sallama, ya k arasa ya ce mata ta yi sauri ta had a abincin y an asibiti yanzu zai juya Musa yana wajen yana jiransa a napep d insa. ta amsa ta koma kitchen d in da sauri ta d aura mai sannan ta d auko flask ta fito ta ci gaba da had a kan d anwaken. Sai da ta gama tukunna ta nufi kitchen d in domin ta zuba mai ta kammala komai. A kitchen d in ta samu Sagir da Kubra yana tayata tsintar wake suna hira suna dariya, ba ta ko kalli inda suke ba dan ta tsani Sagir tun ba yau ha tunda ta fahimci d an iska ne ya fice mata a rai gashi uwarsa ba ta son laifinsa. Mahaifiyar Kubran ce ta kirata dan haka ta tashi da sauri tana cewa ta fice daga cikin kitchen d in. Tsaki Dije ta yi ta rasa dalilin da ya sa ba za a kafa dokar hana maza shigowa kitchen d in gidan ba fisabilillahi da hijab mutum zai ji ko da zafin kitchen d in da ko windo d aya babu, musamman ma da rana idan kowa ya kunna murhunsa kitchen d in sai ka ji kamar oven ga uban hayak i na masifa! So take yi ta koma d aki ta d auko hijab d inta amma kuma ta ji ya Aminu ya ce ta yi sauri gashi ba ta so ta sake yi musu wani laifin dan haka kawai sai ta ware d ankwalin kanta ta d an yane jikinta da shi dan ta lura Sagir d in bashi da niyyar fita kuma dukda bata juya ba tana jin yadda idanuwansa suke yawo a jikinta. Rigar bacci ce a jikinta amma cotton kuma hannunta d an dogo ne dan ya kusan rufe guiwar hannunta ma, sai zani da ta d aura a kan rigar baccin nata da d ankwalinsa, rigar baccin loose ce amma da ikon Allah ta fito da albarkatun k irjinta sosai haka nan shima zanin normal ta d aura shi amma k ugunta ya fito sosai tubarkallah. Tsabar yadda Sagir yake sake lek ata yana kallonta har d an zillo yake yi daga nan zaune kan kujerar inda yake idanunsa kamar zasu fad asa, ga ta dai a gabansa amma da ikon Allah lek e yake yi ko mai
Chapter 18 · 0% Book details