Sashe 30
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
fara wani irin zafii ga ife-ife suna jiyowa a waje ga result d in ya Muhammad sam bai yi kyau ba, duk k ari da dauriya irin tashi bai san lokacin da hawaye suka zoba masa ba shaaa Da sauri ya kawar da kansa yayinda Iyya ta yi saurin barin wajen dan ya fiye mata ta shiga d aki ta yiwa Kamalunta addu a akan dai ta tsaya ganin wannan kayan k uncin. Iyya ta na wucewa Kaka ta ce Wallahi tallahi ka ji dai na rantse maka ko kukan jini za ka yi yau sai ka zab a musamman ma wannan tsinanniyar Yarinyar wallahi na gama ganinta a cikin gidannan. Kalli abunda ta yiwa Kubra ma jiya babu kyan gani! Yarinya gaba d aya ta addabi kowa! Ta yi maganar tana mai finciko Kubra sannan ta cillo musu ita da idonta guda d aya (d ayan ya yi kacha kacha yana ruwa) da saman goshinta a fashe wadda Mamanta ce ta kai k ara jiya Kaka kuma ta ce kar su kulata su barta da su za ta yi maganin Dijen da zarar Mallan ya dawo. Tun ranar Kuburar take jinya sai yau ne da suka ji muryar Mallan uwarta ta fincikota suka fito dan ta ci alwashin ba zata bari wannan Abu ya tafi a banza ba wallahi. A hankali a karo na biyu Inna ta sake ce masa matsa in wuce Kuka Dije ta saka ta zo ta rungumeta ta baya ta k ame, a hankali Inna ta saka hannu ta b areta daga jikinta ta ce kar ki damu za ki dinga gani na, ni zan tafi ke kam ki yi zamanki a nan dan babu wanda ya Isa ya kore ki daga gidan ubanki! Wata uwar gud a Asabe ta rangad a kamar ba ta san halin da ake ciki a Unguwar ba, ta ce ai kuwa yau za ki ga wanda zai koreta dan sai ta fita! A zuciye Inna take sannan a fusace gata cikin tashin hankali kuma dama a k ule take da Asaben wannan dalilin ya sanya ta juyo a fusace ta d auketa da wani kalar rikitaccen Mari! Da sauri Kaka ta yi kanta Mallan ya yi saurin shiga tsakani wanda hakan ya bata damar nufar k ofa da hanzari wanda ba dan Kawu Isa yana a bakin k ofar ba da tuni ta fice Wani kalar ashar Asabe take dannawa Inna ana rirrik eta tana fiffisgewa wanda inda ace daga ita sai Innar ne a wajen ta san k aryarta ba ta isa ta yi mata hakan ba, ganin su Mallan ta san ba za su bari abun ya yi k arfi ba ya sanya yau d in take huce takaicin da ta dad e tana nad Runtse ido Inna ta yi da k arfi ta ce ka bud e min in fita na ce!!! Cikin rarrashi kawu Isa ya ce idan kika fita Ina za ki je?? Duk yadda ta so rik e hawayenta kasawa ta yi da kyar ta iya ce masa kar ka sake yi min magana kamar wanda yake magana da wadda ba ta da wani gata sai naku Yo kinada wani gatan ne bayan namu? Shegiya butulu tsintacciyar mage mabaraciya!!! Cewar Kaka. Da sauri Mallan ya k arasa ya jaa hannun Inna suka bar soron! Ya so ya sakata a d akinta amma ta k Cikin b acin rai abunda bai tab a faruwa ba ya kalli Kaka wadda ta biyosu ya ce A matsayinki na Mahaifiyata na zab i in yi miki biyayya Dije y ata ce ba zai yiu in koreta ba dan amana ce Ubangijina ya bani, ke kuma gashi kina ik irarin tsinantaka a kaina dan haka na kira Isa na shaida masa, da ni da shi mun yanke akan za mu aurar da ita ranar Juma ar nan in sha Allahu ga Yusufa d an wajen Isa daga nan ba zaki sake ganinta ba za ta tafi ta bar miki gidan nan! Sannan magana ta biyu Kaka ki daina sheganta mini y a dan girman Allah, na yi abunda kike so na yi miki biyayya dan haka kema ki daure ki daina yin abubuwan da suke tab a ni ko dan lafiyata. Yana gama fad in haka ya juya ya wuce cikin d akinsa ya rufo k ofar Sai da Inna ta yi da gaske tukunna ta iya janyo numfashinta ya dawo jikinta, yayinda Asabe ta kwashe da dariya k asa-k asa ta ce shegiyar Yarinya dama k auyen ce ta kamace ki!!! Sai in ga ta Ina za ki zama barister Daga haka ta juya da sauri ta koma d akinta dan ta ga babu Mallan a wajen tsaff Inna zata yo kanta. Da kyar Inna ta dedeta kanta daga haka ta fara k arin fita daga cikin gidan kawai!!! Wannan karon kuma haukace musu ta yi ta ce wallahi ko ta tsiya sai ta fita!!! Gashi k auri da ife-ifen waje sai k aruwa yake yi. Kopa d in nan ce ta yi sauri ta afka d akin su ya Muhammad ta shiga ta hau neman madarar bacci a kayan Usssy dan ta san ba zai rasata ba saboda ita ce favorite d insa, ai kuwa ta samota, ta fito da gudu ta zo ta bayan Inna ta toshe mata hanci da ita, a take ta tafi ta sulale ta zube a wajen tana mai jin duniyar gaba d aya ta koma mata upsidedown! A take ta fara ganin mutanen wajen da su da muryoyinsu kamar slomo cartoon dan overdose Racheal d in ta yi mata. Duk cikinsu babu wanda yake cikin haiyyacinsu shiyasa suka gagara yiwa Racheal d in fad an abunda ta yi wanda ita take ganin dai-dai ne. Sosai kunnuwansu suke jiye musu masifa da tashin hankalin da yake wakana a waje Inna kuwa bayan slomo gaba d aya komai juya mata yake yi gashi ta yi luuuuu amma kuma ba bacci ta yi ba sai dai hatta d akinta sai kinkimarta suka yi suka kai ta suka ajjiye Dije tana biye da su kawai tana wani irin kuka abun tausayi. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 14. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Ba a dad e da shiga da Inna cikin d akinta ba jiniyar y an sanda da ta y an kwana-kwana suka karad e unguwar. Da gudu su Ya Kamal suka shishshigo gida dan har da sojoji aka zo kuma suna zuwa suka fara sakin harsashi suna kakkama jama a, babu ruwansu da wanne b angaren kake kawai danna duk wanda suka samu da makami suke yi cikin mota. Ya Kamal a k afarsa ya ji ciwo kawai, yayinda aka yanki Minu a hannu, Ussy kam sai da suka janyo sa da kyar suka afko cikin gidan tare da shi dan a buge yake kuma shima an sare sa. Ya Musa shima a hannu ne amma ba wani sosai ba, ya wuce gidansa, Sagir kuwa babu shi babu alamarsa wanda hakan ya sa Mahaifiyarsa ta zube a wajen ta shiga kururuwa gashi babu damar sake fita dan duk wanda ya bari sojojin nan suka kama shi to kafin a wanke ka a karb o ka ma aiki ne dan ba wanda ma ya san waye ya kirawo su. akin Inna Minu ya shiga yana shiga ya gansu Dije ta kama mata kai tana yi mata tofi Da sauri duk suka kallesa sai kuma Dije ta mik e da sauri ta je ta fad a jikinsa ta saki kuka sai kuma ta cika shi cikin hanzari ta wuce ta je ta d auko wani clean d ankwalinta wankakke ta zo ta fara nad e masa hannunsa da shi wanda har yanzun yake d igar jini. Inna kam babu damar motsi sai binsu kawai da take ta yi da idanu. Ganin yadda ta kasa motsi ya sanya ya nufeta a gigice yana tambayar Dijen mai ya sameta Biyosa ta yi ta sake kama hannun nasa ta ci gaba da nad e masa dan ta tsorata da yankar, tukunna ta shiga gaya masa duk abunda ya faru Runtse idanuwansa ya yi da masifar k arfi zuciyarsa tana wani irin tafarfasa Da kyar ya d an yi controlling kansa sai kuma kawai ya kalleta cikin dakakkiyar murya ya ce mai ya faru aka ce an yi garkuwa da ke garin yaya kika dawo har da allurar k arin ruwa a hannunki?? Kuka ta fashe da shi tana mai ci gaba da d aure masa hannnun da ta gagara kammalawa har yanzun, sai da ya sake ce mata eh!! Tukunna ta fara labarta masa komai. A yadda Inna ta ke kwance ta fahimci komai kuma a take lissafin nata ya bata tabbas akwai wani abun game da Dije k unshe a zuciyar Ma ah, Minu kuwa fad a ya rufeta da shi kamar zai cinyeta d anya, fad an da shi kanshi bai san dalilin yi mata shi ba! Cikin kuka sosai ta ce Ya Aminu dan Allah kar ka bari a aura mini Yusufa, bai yi karatu ba fa kuma k auye za a kaini! Tsaki ya yi, cikin d acin zuciya ya ce Dalla malama ki daina kuka! Allah na tuba hauka ake yi da za a aura miki mai mata har biyu? Karatun naki kuma fa! Shiruu ya d an yi daga haka kuma kawai sai ya mik e ya juya ya fita fuuuu kamar wanda zai tashi sama, wallahi idan Kaka bata yi gaggawar gyara halinta ta fita sabgar Mahaifiyarsa da k anwarsa ba tabbas sai ya illatata sai dai duk abunda zai faru ya faru!! Saboda ita haka nan kurum sai a cire Yarinya kamar Dije daga makaranta a aurar da ita a k auye? Saboda tsabar cin zali! Inaa wallahi ba zai yiu ba! Sai dai su bar gidan har da shi da Ya Muhammad. Direct d akin Mallan ya nufa amma bugun duniya ya k i bud ewa, Kawu Isa ma a d akinsu ya yi masauk i wanda Minun yake ji kamar ya rufesa da duka! Dududu fa d an nasa ko sa an Ya Muhammad bai kai ba amma har yana shirin yin ta uku tsabar kankanba shi kuma kalli da gani farin ciki