Sashe 41
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
amma ya san ko sayar da kansa zai yi bai Isa ya samu kud in ba Kai muke jira, na ji ka yi shiru Mallan Bashir, yanzunnan kafin mu shigo wajen ka muka rabu da mai unguwa kuma shima maganarsa irin tamu ce indai har ta tabbata akwai alak a tsakanin Ma aruf da Khadija to a ce muku ku bar Unguwar ko kuma ka aura masa ita a zauna lafiya amma mu a ganinmu gara kawai ko da ace za ka aura masa ita d in ku tafi d in kawai saboda tana budurwa ma an kalleta ya yi kisa ballanta ta zama tasa? Gashin kuma kanku zama da ku had ari ne. Ko da ace Ya kamal bai san komai game da halinda ake ciki da Kaka na case d in barinsu gidan ba ya san wasu abubuwan. Dan haka ya yi shiruuu tausayin Mallan wanda ya gagara furta komai jikinsa har ya fara karkarwa yana dad a lullub esa. Chaan ya d ago a hankali ya kalli mutumin ya ce Har yanzu ba mu da tabbacin cewa Ma ah ne ya ke kashesu fa, Hatta Sagir d in da kuke magana akai waenda abun ya faru a kan idanunsu ta inda suka bayarda da shedar Scorpion ne ya kashesa, Shi kuma Mallan Manniru Allah ya ji k ansa kun dai sanshi da cin bashi satin baya tabbas ya karb i bashi a wajen wasu y an Fagge dan ko shekaran jiya da kyar muka rabashi da su d ayan yana ta ik irarin sai ya kashesa. Ku dinga yiwa kanku adalci mana, yanzu idan y ar wajenka ce za ka bayarda shawarar a d auketa a bawa Ma aruf ne?? Cikin d an b acin rai mutumin ya ce ba na son sakarci! Mu zauna a yi ta kashe mu kenan kake so ko yaya? Duk wannan abun da muke yi kusan fa ku matasan layin za a ce ana karewa.. Tabbas tsoro da gudun zubar da jini suna daga cikin dalilan da yake so Mallan da iyalinsa su bar Unguwar amma kuma still yana son muk amin Mallan d in ne shiyasa yake dad a zak alewa. Kamar had in Baki a take ragowar mutane biyun suma suka hayayyak o har da cewa ko dai Mallan ya bar Unguwar ko kuma su koresa k arfi da yaji tunda sun lura son kan nasa ya yi yawa kuma idan ba a yi masa da gaske ba haka nan zai zauna daram akan jinin su Yusufa ba a d auki wani mataki ba. Shiruu kawai Mallan ya yi ya k i tanka musu dan a gaskiya idan za a bi ta zab insa a barsa to bai ga dalilin da zai sanya ya bar Unguwar ba sai dai a yi ta kiransa da mai son Kai amma bai damu ba dan ba zai tarwatsa rayuwar Dije da Halima saboda zargin da ba a da shaida ballantana tabbaci a kai ba! Dan shi har ga Allah dukda cewa shima ya yarda d in amma zuciyarsa tana dad a jaddada masa cewa ba Ma ah bane ba A hankali kamar daga sama ya ji Ya Kamal ya ce zan aureta zan d auketa da Iyya mu koma garinmu, Ina fatan hakan zai rufe komai daga gareku? BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 20. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Da sauri Mallan ya hau girgiza masa kai idanunsa jazir ya ce a Kamal ba za a yi haka ba Cikin tarar numfashinsa Ya Kamal ya ce Mallan kar ka ce mini kai ma ka yarda da abunda kowa yake fad Zargi ne suke yi wanda idan aka bari aka tafi a haka shikenan sun tarwatsawa Dije rayuwa kenan har abada! Dan a wajensu ne kad ai barinku Unguwar nan zai zama win! Amma a wajenku kamar kun sake bawa abun mazauni ne, dan haka hakan sam ba ita ce mafita ba, sannan ka yarda da ni idan na ce maka muddin ka bari suka yi nasarar korarka a nan to babu Unguwar da zasu yarda da ku an dinga kwallo da ku kenan dan a kusan kaff garin Kano waye zaka ce bai san labarin Ma ah ba? Ko da ace ma Unguwar da zaku je su d in basu sani ba na tabbata ba zaku yi sati ba labarin komai zai iskesu dan yanzu kiwon mutum ake yi ba na dabba ba. Dan haka ka yi zaman ka a nan inda ka taso har ka yi aure ka tara iyali, ka bani auren Dije ni zan aureta mu bar garin nan da ita in sha Allahu babu abunda zai sameni su kuma bak in fentin da suke shirin goga mata sai dai su shanye abunsu. Ya k arashe maganar yana mai kallon dattawan da suke zaune sunata muzurai. Kafin ya juyo ya kalli Mallan d in ya d aura da cewa Sannan dan Allah kar ka yi min kallon wanda yake son aurenta saboda tausayin halin da take ciki dan ni saboda Allah da son da nake yi mata tuntuni nake so in aureta. A hankali Mallan ya jinjina kai kafin ya ce na gode Kamal, bari za mu gani. Girgiza kai Ya Kamal ya yi sannan ya ce ka daina yi mini godiya Mallan I m not doing you a favour kai ne zaka yi min ta hanyar bani Dije in aura. Sannan Ina so a d aura a yanzu in dai har babu damuwa tun kafin ma mu fita daga nan wani ya b ullo da wata matsalar. e Baki wannan mutumin da ya fi kowa d aukar abin da zafi ya yi kafin ya ce to ai shikenan, tunda burin mutuwa ka ke da shi mu masu yi muku shedu ne! Ya fad i haka yana mai gyara zama An kai ruwa rana dan rabewa biyu mutanen suka yi wasu suka ce a d aura wasu kuma suka ce kar a d aura, dagewar da Ya Kamal ya yi ya sanya ba dan Mallan ya so ba ya amince a lokacin aka d aura auren Kamal Yunusu da amaryarsa Khadija Bashir Isa akan sadaki naira dubu talatin ajalan, dan babu cash a hannunsa dan haka ya ce suna shiga gida zai wuce d akin Iyya yana da ajiya dama ya d auko ya kawo. aurin auren kwata-kwata halartar mutane goma ya samu amma kafin su kai gida da ikon Allah labari har ya iske mutanen gidan. Tun daga bakin k ofa da Umar ya hangosu dama already Yaran sun taru ana rige-rigen waye zai fara ganinsu, ai kuwa yana hangosu ya fella cikin gida da gudu yana ihun ga su nan! Ga su nan!!! A tsaye a tsakar gidan suka tarar da kowa an yi cirko-cirko Babba da Yaro tsoho da matashi ana ta tattauna maganar. Suna shigowa Iyya ta k arasa ta kamo hannun Ya Kamal suka wuce cikin d akinta ta turo k ofa ta rufe ruff. Mallan kuwa d akin Inna ya nufa dan su kad ai ne bai gani a tsakar gidan ba gashi maganarsa da ita emergency ce..yana so ya ji ra ayinta. A zaune ya same su jugumm! Ita da Dije kowa ta yi tagumi tana kallon gefe, Dije ta rame ta fige har wani duhu ta yi a iya kwanakin nan, a take tausayinta ya lullub esa ya ji kamar ya koma don baya jin zai iya jurar ganinta a wannan halin amma kawai sai ya dake ya sake maimaita sallamarsa a karo na biyu tukunna Dijen ta yi firgigit ta juyo tana kallonsa. Wani abu mai masifar tauri da d aci ta had iye tukunna ta ce Ina wuni, sannu da shigowa. Daga haka ta saka hannu ta tab o Inna wadda ta lura sam bata ma san da shigowar Mallan d in ba. Kamar yadda Dijen ta yi itama haka ta yi sai dai ita tana d agowa da suka had a ido da shi tashi d aya fuskarta ta chanja dan haka ta cewa Dije bamu waje ba tare da ta kalleta ba. Simi-simi haka ta mik e ta fice ta wuce kitchen ta je ta nemi waje ta zauna dan bata son had a ido da kowa ji take yi kamar ta binne kanta da kanta. Dije tana fita Inna ta mik e tsaye ta ce ka yi hak uri da abunda zan fad a Mallan amma wannan karon abunda ka aikata ba dai-dai bane ba!. Da muka ga maza har biyu sun rasu duk a ta sanadiyyar Dije ya kamata ace mun dakata ba wai mu sake tafka wani kuskuren ba! Yaron nan ko dan tsohuwar Mahaifiyarsa wadda shi kad ai gareta ya kamata ace ka yi la akari da hakan kafin ka d aura auren! Yanzu idan wani abun ya samesa da wanne ido za mu kalli mutane musamman ma ita Dijen? Ko baka ganin halin da take ciki ne? Yarinyar da a daa wani zubin sai na make mata Baki tukunnna nake samun hutu daga surutu da wak e-wak enta wai yau ita ce sai ta kwana ta wuni bata ce komai ba?! A gaskiya baka yi abunda ya dace ba wannan karon Mallan Cikin katseta ya ce yanzu Halima kema kenan kin yarda da cewa duk wanda ya rab eta kamar ya yanki tikitin mutuwa ne? Ki taimaka Halima dan Allah kar ki bari su buga mata tambarin da suke k arin yi.. Saboda son zuciyarmu da son y armu kuma sai mu bari jini ya yi ta zuba? Inna ta katse shi itama. Runtse idanuwansa ya yi da mugun k arfi sai da ya d an jima a haka kafin ya bud e su ya kalleta ya ce yanzu to ya kike so a yi? Cikin tsananin jin zafin abunda zata ce d in ta d an girgiza kanta sannan ta ce ba zan tab a aurawa Ma ah y ata ba! Ba zan bayarda goyon baya ba ba zan yarda ba! Amma kuma ina mai bayarda shawarar kar ka sake yunk urin aurar da ita a wani idan Kamal ya.. Kasa k arasawa ta yi ta sa hannu ta toshe bakinta hawayen da take ta k arin dannewa suna masu silalo mata. A hankali ya ce idan