← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 59

Sashe 54

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

dad i Ina kuma ga idan shine ya yi? Ko Gimbiya Sakina da aka kashe bayan abun ya lafa sai da ya yi kokawa da guilt da kyar ya yakice abun a kansa A hankali ya ji ta sake rungumosa cikin wani salo da yanayinta na musamman mai tada hankalin duk wani d a Namiji mai cikakkiyar lafiya, abu gud a game da shi shine ko masarsara yake yi wuyarta ya ji hannun mace a jikinsa yanzunnan zai ware! Dan haka ba tare da b ata lokaci ba ya amshe ragamar komai a take suka lalace a wajen. *************** Kamar an fisgi maganar daga bakinta Rakiya ta ji uwartata ta ce Rakiya za ki yarda ki yi aikatau? Tsayawa ta yi chak da cin garin kwakin da take yi kafin ta juyo ta kalleta dan sai ta ji maganar kamar ba daga bakin jajirtacciyar Mahaifiyartata ta fito ba. A take tausayinta ya rufeta lokacin da idanunta suka sauk a a kan karyayyen hannunta sannan yanayin fuskar Mahaifiyar tata ya sanya ta fahimci dole ce ta saka ba a son ranta bane ba. A hankali Yarinyar ta sauk e ajiyar zuciya ta ce A ranta har ga Allah ba ta so dan ta san ba zai wuce ace ta je Gidan Manager ta yi shara da wanke-wanke ba gashi y an mutumin (mata) ba su da mutunci sun iya wulak anci da gori. Tunaninta ne ya katse a take ta d ago ta kalli Mahaifiyar tata da sauri jin tana cewa Wai Ingila ko Saudiyya za a nema muku aikin ku je ku yi a chan. Ba ta san lokacin da wani murmushi ya sub uce mata ba ta ce Ramma da gaske kike dan Allah? Farin cikin da Ramma ta gani kwance a kan fuskar Yarinyar ne ya k ara mata kwarin guiwa, dan haka ta gyara zama ta ce na san ba haka kuke so ba ni kaina ba hakan na tsara muku ba amma k addara ta riga fata. Gara mu tashi mu had arfi da k arfe mu taimaki kanmu rashin gata da rashin galihu bashi da mafita. Amma kinga yanzu idan kika je kika taro kud i kika dawo sarauniya za ki zama a cikin gidan nan. Sai kuma ta matso ta kamo hannunta ta rik e sannan ta ce amma ki yi min alk awarin fad amin gaskiya a game da komai sannan ko da wasa idan wani ya zo miki da tallar lalata kar ki amince ki kama mutuncin kanki dan Allah Rakiya sannan ki sanar mini zan san yadda za a yi ki dawo ko a chanja miki wani wajen. Cikin katseta cike da zumud i Rakiya ta ce karki damu, za mu je na yarda ma ni kam d ari bisa d ari. Sannan zan kare mutuncin kaina a duk inda nake, in sha Allahu sai na kaiki Macca. Cikin tsananin farin ciki Ramma ta ce Ameen Ya Hayyu Ya Qayyom d iyar albarka Dan sosai ta ji dad in amincewartata lokaci guda saboda a tunaninta za a kai ruwa rana kafin Yarinyar ta yarda sai gashi kamar ma ta fita zumud Da gasken kuwa Rakiya ta fita zumud in dan a asalin gaskiya Rakiya irin Yaran nan ne masu high taste sannan tana da masifar girman kai gata ba ta son wahala da talauci, kawai so take yi ta kud ance ta ji dad i ba tare da ta sha wahala ba. Shiyasa wannan tayin ta ji sa kamar busharar shiga gidan aljannah, ta san ko Abuja aka kai mutum aiki dad i yake sha ballanta kuma uwa uba k asar waje inda zata je ta yi rayuwa irin ta turawa sannan babu k anzo babu mai da yaji babu miyar kuka!!! Tana wannan lissafin har ba ta san lokacin da murmushi ya sub uce mata ba. Sallama Maman Mariya (Gwaggwo) ta yi ta shigo wanda hakan ya sanya Ramma ta yi saurin gimtse maganar da ta shirya yi. Sai dai kuma ta makaro dan Maman Mariya d in ta riga ta jiyo su jiya ma kuma dama ta ji suna maganar ita da Mama a d akin Iyya. Waje ta nema ta zauna, kai kana ganin yadda take rarraba idanuwa za ka san maganar sirri ce take so a yi, sai da ta yi k asa-k asa da murya tukunna ta ce tun jiya nake ta so mu yi magana Allah bai nufa ba Allah sarki kawai Ramma ta ce tana mai d auke kai dan ma kar ta samu fuskar yi mata zancen da ta san ta ji. Sam Gwaggo ba ta damu da yadda Ramma take ta cika tana batsewa ba ta sake matsowa kamar za ta shige cikin jikinta ta ce jiya na ji kuna wata magana ta abun alkahairi ke da Mama, da farko na d auka kunnuwana ne ba su jiye mini dai-dai ba! To yanzu kuma Ina cikin jan ruwa a rijiya na jiyoki kina maganar ke da Rakiya, ya abun yake ne? In da Hali a had a da Mariya itama. Da sauri Ramma ta ce Aikuwa ba na jin Mariya za ta samu dan ba wai waje ne wanda ake kai kowa da kowa ba, nima ita ta ga Rakiya da Fiddausi ta ce za ta kaisu, kuma aikin ma na iyaka mutum biyu ne ta ce, gashi ta riga ta ce Rakiya da Fiddausi kawai. Sai a lokacin Rakiya wadda ta yunk uro itama zata yi magana ta ji hankalinta ya d an kwanta. Yo idan aka had a ita da su Mariyan aka kai wa kenan za ta yiwa yanga idan ta dawo? Dukda kasancewar su Mariya sun girme mata sosai dan Kubra ta kai 18 ma Mariya sha bakwai Fati kuma sa ar Dije ce amma iyayi da shegen wayo da manyance irin na Rakiyar ya sanya ta shiga cikinsu ta yi kane-kane, kasancewar ita ta yi karatu tun daga nursery ya sanya ajinsu ya zamana d aya gabad ayansu dan su duk basu shiga da wuri ba Dije kuma daga primary ta fara Mariya kuwa sai a ss2 ta shiga yanzu haka ko sunanta ba ta gama iya rubutawa ba wannan ma ya taimaka wajen kasancewarta a cikinsu, sai dai kuma sun fita samari da y an matanci dan duk d insu suna da wayoyi da kayan gayu dai-dai gwargwadon k arfin iyayensu musamman ma Fati, hakan ya sanya wasu lokutan idan kishin ya murd a take kishi da su, yanzu kuwa ga dama ta samu damar da ta san idan ta je ta dawo duk sai ta fi su dan haka ba zata bari su yi gogayya da kowa ba Shiruuu, Gwaggo ta yi kafin chaan ta ce to shikenan, ba komai. Daga haka ta mik e ta fita a ranta ta gama aiyyanawa za ta samu Mama da maganar dan tabbas ta jiyo kyashi a cikin zancen Ramma. Ita kanta Ramma sai da ta fita tukunna ta ji kamar ta bita ta ce mata kar fa ta samu Mama da maganar dan ta san halin Gwaggo da shegen nacii in dai ta sakawa ranta abu to ba ta da zuciya ita kuma Ramma tsoro take yi kar aje idan Mama ta ga Mariya ta d auketa ta ce Fiddausi ta hak ura sai ta k ara wayo, dan a asalin gaskiya Ramma k arawa Fiddausin shekaru ma take yi saboda Yarinyar tana da garin jiki, amma asalin shekarunta goma ne. Kafin dare ya yi Rakiya duk ta susuce sai da ta tisa Ramma a gaba suka tafi d akin Mama ta kira waya a gabansu aka tattauna aka tsayar da Magana akan Saudiyya za a kaita ita da k anwarta, ita za ta yi reno da girki, k anwarta kuma shara da wanke-wanke. Tukunna hankalinta ya kwanta. Murna a wajen Rakiya ba a cewa komai kamar ta zuba ruwa a k asa ta sha. Ita kanta Ramma murnar take yi dan albashin Rakiya ya fi dubu d ari biyu na Fiddausi kuma dubu d ari da hamsin. Inna ta na zaune ta na karatun Al qurani Ramma ta sake lek osu, Dije da Ya Muhammad har yanzun suna nan jiya i yau salla ce kawai take tayar da su Shi ya yi a zaune ita kuma tana iya yi a tsaye (Sallar da sai daga baya da ta tuna tukunna ta je ta yo wanka ta zo ta shiga jerosu tun daga ta azahar d in ranar da Ya Kamal ya rasu) amma ko abinci sun k i ci, Inna kuma ta koma gefe ta zauna tana ta karatu, dan gaba d aya ta ma rasa ta Ina zata fara. Haka nan ta shiga ta nemi guri ta zauna, d akin shiruu kamar na zaman makoki. Ba ta yi minti biyu da zama ba Sumayya ta yi sallama ta shigo. Duk cikinsu babu wanda bai shiga shock na ganinta ba, musamman Dije wadda tun shigowarta ta kafeta da idanuwa. Inda take ta nufa tana zuwa kawai ta fad a kanta ta fashe da kuka. Ajiyar zuciya Ramma da Inna suka sauk e a tare yayinda Dije ta tsaya kawai kamar wata mutum mutumi. Sosai Sumayya take kuka sai da ta yi mai Isarta tukunna ta d ago ta kalli Dije wadda zuwa yanzu take kallon k asa ta ce ki yi hak uri Dije ki yafe min abunda na yi miki, alhini da bak in ciki suka sanya idanuwana suka rufe na gagara yi miki hukunci mai kyau, na manta cewa ba ke kika rubutawa kanki k addararki ba kuma Allah ya riga ya gama tsarawa Mahaifina ajalinsa da yadda zai rasu tun kafin ya zo duniya, ki yi hak uri ki yafewa k awar da ta guje miki a lokacin da kika fi buk atarta. Ta fad i hakan tana mai sake rungumeta. Ta yi kusan minti uku a jikinta tana hawaye kafin ta d ago ta kalleta ta ce Dije ko dai baki yafe min bane ba? Sai kuma ta sake rushewa da kuka, dan sosai tausayin Dije ya rufeta a lokacin da labarin rasuwar Ya Kamal ya iske ta yanzu kuma da ta ji labarin yadda aka tsinto ta a kan gadon Ma a duk sai ta ji kamar ta kurma ihu, Mahaifiyarta
Chapter 54 · 0% Book details