Sashe 21
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
hud u, sai Ya Muhammad talatin, Dije tana ss3 yanzu haka Ya Aminu ya gama University amma shi Ya Muhammad da kyar aka samu ya kammala diploma daga nan shi da kansa ya ce ya hak dan karatun duk a daddafe ya yi gashi sai yayi ta zubewa ana kwaso shi. Aure kuwa sau biyu ya yi sa shima daga nan ya ce ya hak Dan bayan wadda aka sani ya aura a nan unguwa uku, Mallan ya nema masa auren wata a Garko aka d aura ya tare sai dai ko kwana ita kam bata yi ba ma aka fitar da ita a sume! Dan dama a tsorace yake tun da yaga an d aura auren yake gudun abunda zai je ya dawo, kuma tsoro wahala da b acin rai su suke triggering ciwon nasa. Sai Maman Kubra, ita kuma tana da y a da yawa amma rasuwar Mijinta ya sanya aka karb e su aka barta da k ananun kawai y an biyu Kubra da Usman (Usso), unfortunately Usman yana shaye-shaye sosai an kasa rabasa da shi haka nan ake ta fama, Kubra a k alla yanzu shekarunta sha takwas amma rashin dai dai ita a cikin gidan ya sanya ta shiga group d in su Rakiya. Doguwa ce sosai fara sol da ita dan asalin Mahaifinsu Igbo ne, yanzu haka duk y an uwanta suna hannun Kakarsu wadda itama ta tsani uwarsu kamar mutuwarta saboda kasancewarta Bahaushiya ita kuma ta fi so a auri ta su. Wannan rashin jituwar da ke tsakanin Kakarsu da Uwarsu shi ya yi sanadiyyar yanke hatta zumuncin da ke tsanin su Kubra da y an uwansu. akunan da suke kallon k ofar shigowa tsakar gidan kuma (guda hud u) D aya na Asabe ne, d aya Empty ba kowa a ciki, sai na kusa da shi kuma d akin wata copper ne (Grace) ita kam ba ma ta zama sosai Kullum sai dare take dawowa ta kwana da safe k arfe tara take fita. Copper nan tana ganin ikon Allah a cikin gidan dan hatta band aki idan ta shiga ta fito sai an yi masa wankan tsarki, gashi su yi ta munafurcinta da Hausa dan ita bata ji ammafa tana fahimta, dan suna farawa ta san me suke yi, gata shiru-shiru da ita babu ruwanta amma hakan bai hanasu nuna mata wariyar launin fata ba. Bayaga aikin da ya yi mata yawa da d an chilling d inta har da halin y an gidansu Dije ya sanya ba ta yarda ta dawo gidan sai duk sun yi bacci. Sai d akin Ramma wanda yake a k arshen wajen kusa da rijiya. akuna uku da suke a jere da kitchen kuma na kusa da d akin Ramma d akin wata tshohuwa ne Iyya. Iyya wata tshohuwa ce dan duk gidan babu mai shekarunta. D anta d aya kwal a duniya Ya Kamal. Business da ciku-ciku ne suka kawo sa garin Kano ganin yana shirin dad ewa a garin ya sanya ya je ya d auko Mahaifiyarsa suka zo nan. Maganar Allah idan ka d auke Mallan to kaff gidan babu mai hankalin Ya Kamal a maza a mata kuma Iyya. Wasu irin mutane ne masu kamala da d attako. Ya kamal a maza duk ya girmesu dan hatta Ya Muhammad ya bashi watanni biyu, yadda yake tsaye a kan duk wani al amari na gidan da y an gidan za ka d auka uwa d aya uba d aya suke, har kwana ya tab a yi a police station saboda Usso, sannan al amari indai ya shafi Dije da y an d akinsu to ya kan tsaya tsayin daka har sai ya ga komai ya dedeta, wannan dalili ya sanya Dije take matuk ar ganin girmansa, gashi kuma Aboki ga favorite d inta Ya Muhammad. Sai d akin Gwaggo, Gwaggo itace mahaifiyar Mariya da Musa, a gidan daga Ya Kamal sai Ya Muhammad sai Musa a shekaru, shi kam Musa da aurensa ma matarsa tana da tsohon ciki dan ba a dad e da yin aure ba, amma kasancewar duk a layi d aya ne suma suke haya ya sanya kusan kullum yana gida. Sana arsa keke Napep ce da shi (d an sahu ne) Sai Mariya ita kuma shekarunta sha bakwai ita ma tana ss3 ajinsu d aya da Dije. Sai d akin kusa dashi..d akin Maman Sagir, Sagir d in sa an Minu ne sai dai shi yana aiki a company na shinkafa so yana samu ba laifi dan haka uwar Kubra da uwarsa suke son aura masa Kubra wadda tun zuwansa gidan ta mato a kansa, shi baya wani sonta amma su kam sun nace haka nan yayi ta wulak antata yana yi mata rashin mutunci amma ita ko a jikinta dan Yarinyar ba dai sauk in kai ba, in dai ka ji ana case da ita tana hauka to akan Sagir ne. Dan kwarkwar ta ke komawa when it comes to him, ta kan je ta samu mutum har gida a yi ta rigima saboda Sagir, shiyasa su Mariya suke cewa ta haukace a kansa, duk yadda aka yi asiri ya yi mata. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 09. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Mallan bai samu ya dawo daga asibiti ba har dare sakamokon yanayin jikin na Ya Muhammad sam babu sauk .Inna ta je ita kad ai babu yadda Dije bata yi ba akan a barta ta je ta gansa amma ko kallonta Inna bata yi ba haka nan aka tafi aka barta kuma da ta dawo ta tambayeta ya jikin nasa nan ma ba ta ko kalleta ba. Inna ta so ta zauna amma sam ba zata iya jinyar tasa ba dan doke-doke yake yi sosai dole maza ne za su iya kuma asibitin basa yarda da masu jinya sama da mutum biyu. Tun lokacin da Inna ta fita Kubra da Rakiya suka dasa kujera a tsakar gida suke ta yadawa Dije magana, da yake Kubran fianc in Sagir ce ita zai aura shiyasa tunda ta ji ance yana kallon Dije wani malolon bak in ciki da kishi suka taru suka yi mata k abe-k abe ta rasa inda zata saka ranta. Rashin wayo ya sanya ta kasa danne kishinta, gashi Dijen kwata-kwata ta k i kulasu hakan ya sanya take ga kamar ko tsoronta ta fara ji yanzun tunda dama ita duk ta girme musu, ko kuma dai ko meye za su yi mata ta san ba lalle ta kula su ba tunda ga abunbuwan da suke ta faruwa kuma duk itace sila..sun san ko dan halin da Ya Muhammad yake a ciki ba lalle ta kula su ba. Tun safe suke abud aya ba ta kulasu ba, da yamma bayan Inna ta dawo Dijen ta fita siyo kukar miya Kubra ta bita a baya ta lab e ta nemo Yara wajen su biyar ta raba musu naira ashirin ashirin ta ce idan Dije ta fito su yi mata ihu su ce mata y ar Iska. Dukda Yaran suna d an shakkar Dije amma hakanan suka amshe kud in tana fitowa suka hau ihu suna kiranta da y ar iska kafin su kwasa a guje su bar wajen gudun kar ta damk e su. Wani Yaro ta kama a cikin yaran d an k arami wanda Allah bai bawa ikon fecewa ba har ta kai ga damk ar sa. Sai da ta sauk e masa maruka hud u kyawawa tukunna ta tambayesa wa ya saka su dan daga ganin abun ta san sakasu aka yi. Tiryan-tiryan Yaron ya gaya mata, tsabar mamaki bata ma san lokacin da ta cikashi ya gudu ba. Aikuwa ta na shan kwana ta ci karo da Kubra a tsaye, wadda tana ganinta sai ta d an diririce sai kuma ta nutsu ta kama kanta. Kallonta Dije ta tsaya tana yi kamar kuma wadda aka bawa izini tashi d aya ta cikumo hijabinta ta nad e mata fuska da shi ta shiga kimarta kamar an aikota, ganin Kubran tana shirin kwacewa gata Babba ya sanya Dije ta rarumi dutse ta buga mata a ka. Ta dai ga ta tsugunna daga nan bata san ya ta kaya ba ta yi gaba abunta ta barta da fuska a rufe. Sosai su Kubra suke bata mamaki su da iyayensu idan suna wani abun ko da yake ba laifinsu bane ba duk laifin Kaka ne. Ta ji daga bakin Inna Farko-farkon fara zuwan y an haya gidan sosai suke yiwa Kaka da Inna fadanci har da su Ya Muhammad, a lokacin d aki aka ware Inna take amfani da shi a matsayin nata kitchen d in su kuma suke amfani da kitchen d in gidan. Bak in cikin fadanci da girman da ake bawa Inna ya sanya Kaka ta tashi kitchen d inta ta saka ta ta koma cikin y an haya sannan ta ce musu duk d aya ake ko laifi su Ya Aminu suka yi musu suna da ikon kimarsu! Da Mallan ya yi magana ta hau shi da fad a wai zai koyowa iyalinsa girman Kai. Dukda haka hankalin Kaka bai kwanta ba sai da ta dinga tsinka Inna a gaban jama ar gidan ta tabbata sun rainata har ta kai sun fara fad a da ita tukunna hankalinta ya d an kwanta, kuma duk f iri-k iri za ta bawa Inna rashin gaskiya ta zazzageta a gaban kowa. Zuwan Asabe gidan shi ya taimaka aka sake rainasu, dan yanzu haka mutum ba su fi biyu ne a cikin gidan ba da za a ce ba sa bin Asabe bashi kuma ta k i biya. Sannan rashi da babu ma ya taimaka sosai wajen janyo musu raini dan kusan y an hayan gidan nasu ma sun fi su rufin asiri wasu lokutan. Suna girmama Kaka da Mallan amma Asabe kam da y an Mallan an rainasu, Inna kuma munafukai masu wayo da fuska biyu sune kawai suke bata girma (su Maman Fati) Tana wannan tunanin zuciyarta fal bak in ciki ta k arasa gida. Tunda yamma ta yi Asabe ta ga Mallan bai dawo ba ta san cewa watak il fa sai ya iya cewa a chan zai kwana bayan ya san yau d in kwananta ne!