Sashe 7
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
sannan zaninta har ya kama wuta nan ma Allah ya taimaka ruwan da ya zube ya jik oina ya kashe wutar jikin zanin nata wanda ta d aura akan rigar baccin jikinta da ta murhun duk ya kashe. A zuciye ta yi kan Ramma za ta rufe ta da duka Iyya ta shiga tsakaninsu, tsabar bak in b acin rai Asabe bata san lokacin da ta ingije Iyya tana zage zage ta yi kan Ramma ba! Dai dai nan Ya Muhammad wanda tun d azu yake ta jin hayaniya ya shigo cikin kitchen d in wanda shigowar tasa ce ta sanya aka samu rangwamin bala in da yake shirin faruwa dan a yadda Asabe take a zuciye haka itama Ramma shiyasa ta ja ta tsaya jira kawai take yi ta k arasa inda ta ke ita kuma ta yi mata illa. Ba yadda ya iya ba dan ya so ba haka nan ya ruk o hannun Asabe da kyar kuwa ya iya rik e ta dan sai fisge fisge take yi tana zage zage kamar tab iya, sannan ya shiga tsakaninta da Ramma da suke ta jerawa junansu ashar ta uwa ta uba. Salati Kaka ta yi daga shigowarta kafin ta ce ka cika mata hannu ko sai na ci ubanka? Kwartancin naka kuma yau ta nan ya biyo? Da sauri Ya Muhammad wanda shi ya ma manta ya kamawa Asabe hannu ya cika ta sai kuma ya yi sauri ya fita ransa na gama b aci dan ya san yanzu zata fara Inna kuma ba barinta za ta yi ba. Yana fita Asabe ta ce Kaka wa adin zaman matar nan a cikin gidan nan ya cika yau wallahi sai ta tafi, na gama yi mata kara. Wata uwar gud a Ramma ta rangad a wadda ta tashi kusan kowa a cikin gidan, kafin ta ce sai ki bari idan kin Isa da gidan da mai gidan tukunna ki yi magana! Banza wadda bata da k ima a idon miji kawai! Allah na tuba kina borar ki da ke ke har kin Isa ki ce za ki sa a tashe ni a cikin gidan nan? azu fa Ina jinku ke da shi da kyar ya barki kika shigar masa d aki alhalin duk ranar kwanan Halima tun bayan sallar isha take tafiya idan ba ta je ba kuwa nan zai fara jera mata d an kira! Ai Wallahi kin yi asara, kamar yadda uwarki ta rako mata duniya kema haka nan kika rako mata duniya, borori kawai!. Jikin Asabe ne ya fara rawa idanunta suka cicciko .ganin haka ya sanya Kaka ta yi saurin cewa kar ki kulata, wuce ki tafi, bar ni da ita. Dan ta fahimci yadda maganar ta daki Asabe tsaff tana iya zubar da hawaye a gaban Ramma da mutanen gidan da duk aka firfito suka yi cirko cirko, aje a sake rainata. Da sauri kuwa ta juya ta fita dan itama ta san ba zata iya rik e kukanta ba. Tana shiga d akinta kuwa ta sake shi marar sauti. Asabe tana fita Kaka ta cewa Ramma ta tattara kayanta ita da y anta su bar gidan tun da ba ta san mutunci ba. Ramma kuma ta yi tsalle ta dire ta ce Wallahi ko kud in hayan da ta biya na shekara ya cika babu inda za ta je, sai ta samu wani gidan tukunna, ai ba haka ake yi ba . Nan da nan fad a sai ya koma kan Kaka da Ramma..dama Kaka haushin Ramma ta ke ji saboda yadda take yawan zagi da gorantawa Asaben kamar ba a gidan Mijinta take haya ba. arshe dai Mallan ne ya zo ya raba fad an dan tabbas Ramma ta fi Kaka gaskiya tunda ta bayar da kud in haya kuma sun amshe sannan ya san yanzu haka idan Ramma ta tayar da balli ta ce a bata kud inta ta tafi tabbas basu da kud in da za su bata, kuma da ikon Allah Kaka ta san da hakan amma ta zage tana balli, kamar idan aka ce ta kawo zata kawo d Bayan an lallab a Kaka ta koma d aki Ramma da Maman Kubra suka ce basu yarda da jik a musu icce da Asabe ta yi ba dan kusan rabin iccen dake a kitchen d in idan aka d aga su tsiyayar ruwa ma suke yi, gashi gari babu rana alamun ma ruwa za a zuga yau d in, ragowar kuma suka ce ba komai ai tsautsayi ne kuma za su ma iya yin amfani da waensu a hakan, Maman Kubra da Ramma kuwa sai da suka karb ari biyar biyar a hannun Baba kud in icce tukunna hankalin su ya kwanta a cewarsu ba za su sha wahalar sha ani da jik en icce saboda Asabe ba. Sai da k ura ta lafa tukunna aka fara watsewa ana kafa layin band aki domin kama ruwa da yin alwalla. Gidan su Suwaiba Ramma ta je ta samu ta d aura ruwan da zata saka fanken nata a ciki, kafin ruwan zafin ya yi kuwa suka kafa dandalin munafurci kamar ba asubar fari ba. Allah ya taimaka allurar jijiya tana aiki a jikin Inna dan har aka gama budirin nan ba ta sani ba, da kyar Dije bayan ta dawo daga band aki ta iya tashinta, ta tashi ta yi sallar asuba Cikin wani d an madaidaicin masallacin da ba zai d auke sama da mutane hamsin ba! A tsare yake ga hasken lantarki dan solar ce da su Babba ba laifi. Layi uku ne a cikin masallacin inda na chan k arshe yake cike da mutane na biyun ma haka yayinda ba farkon kuma (kusa da liman) ya kasance babu kowa a wajen tun daga farkonsa har k arshensa Layin k arshe shima ya cika dan haka wani magidanci wanda ya tare jiya a unguwar har ya zo zai shige aka ce masa ai babu guri a cikin masallacin dan haka sai dai ya tada wani jam in a kan simintin barandar masallacin. Da mamaki ya ke kallon saurayin da ya gama yi masa bayani kafin ya ce Chan gaba ba sahu bane ba?? Dariya saurayin ya yi kafin ya ce Eh akwai mai wajen ne Daga haka ya juya dan har an tada ik ama. Wani d an gajeran tsaki magidanci ya ja kafin ya ce mai waje kuma a masallaci? Wanne irin shirme ne wannan daga haka ya wuce ciki chan sahun gaba ya tsaya shi kwalli d aya kwal ya tayar da ik Ba a kai ga kaiwa ruku u ba Ma a ya shigo shi da Yaransa guda bakwai ta k ofar da ya saka a ka bud a masa dai dai saitin sahun farkon. Da mamaki yake kallon mutumin kafin kawai ya d auke kanshi ya wuce bayan ya yiwa Yaran nasa alamar su kyalesa da yatsunsa uku. Ana idarwa aka fara watsewa..Mallan (Wanda ya kasance limami a masallacin) shima tunda ya waigo ya ga wani a sahun su Ma a hankalinsa ya tashi dama chan a tashen yake. Kaff cikin masallacin mutun uku ne (Mallan sai wani tsoho da wannan mutumi na sahun su Ma a) kawai suka tsaya yin addu a amma ragowar duk guduwa suka yi. Wannan tsohon yana fita Ma a ya kalli wani a cikin Yaransa ya ce je ka siyo min kayan b alli b alli, kai kuma ka rufe min shi Daga haka ya mik e ya fita waje. Da sauri Mallan ya runtse idanuwansa da mugun k arfi sai kuma ya juya gaba d ayansa ya ci gaba da karatun Azkar d in da yake yi, yana gamawa ya d auki Al qurani ya shiga karantowa Dai dai nan wannan mutumin ya mik e ya nufi k ofa dan gaba d aya hankalinsa yana a kan wayarsa ne shiyasa bai ga lokacin da aka rurrufe k ofofi uku na cikin masallacin ba. Kallon k ofofin ya yi yana mamakin ya aka yi suka rufu kafin ya k arasa jikin wadda take kallonsa ya gwada bud ewa ai kuwa ilai ya tarar a gark ame kamar yadda yake zato, gashi k ofofin wasu irin k ofofi ne kamar na tsoron prison dan sam ya kasa ganin ta Ina zai bud e ta ciki. Da mamaki mutumin ya juyo ya kalli Mallan wanda ya kasa d agowa sai kuma ya k arasa inda yake ya ce akaramakallahu Barkanmu da asuba A hankali Mallan ya ce Barka ka dai Cikin nutsuwa mutumin ya ce masa inaga Yara sun rufe mu fa ta baya, ko akwai yadda za a yi a bud e ta ciki? Mallan yana shirin yin magana Oscar wanda ya shigo yanzun ya k araso wajen ya ce mu ne muka rufeka saboda Oga yana da ganawa da kai ne a waje idan ka gama addu ar, wuce mu je in kai ka wajensa. Kallonsa mutumin ya yi wanda sai da gabansa ya d an yanke ya fad i dan ba Ma a kad ai ba hatta Yaran nasa abun tsoro ne, shiyasa mutane da yawa suke mamakin yadda sam Dije bata jin shakkarsa. Gyaran murya mutumin ya yi kafin ya ce ana ka cewa Ogan naka za mu gana da shi anjima dan yanzu haka ko gida ba zan koma ba direct daga masallancin nan akwai in da zan je Cikin katseshi Oscar ya ce Oga ba ya jira! Idan Oga ya bada umarni dole a yi a lokacin!! Sannan Ma a ba Oga na bane ba ni kad ai, Ogan kowa ne har da kai da uwarka da ubanka dan uban babanka! Cike da b acin rai wanda tsoro ya hana shi yin tasiri har ya kai ga baiyyana kansa mutumin yake kallon d an tsakurkurin d an daban da yake tsaye a gabansa yana masa magana kamar wani ubansa! A yadda ya gansu gaba d ayansu ya san ba hankali ne da su ba tsaff za su yi masa illa gashi sun tsattsare k oina har da wani rufesa a ciki dan kar ya gudu, dan haka ya zab i kawar da duk wani b acin rai ya bi bayansa suka fita tare domin zuwa inda Ma in yake duk dan a zauna lafiya