← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 59

Sashe 55

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

kanta sai da tausayin Dijen ya baiyyana a kan fuskarta lokacin da ake labarta labarin, amma da yake idanuwanta sun rufe da jin haushi da bak in ciki da tsana sam sai ta gagara fahimtar tausayin nata take ji k arshe ta b ige da yi musu Allah shi k ara, yanzu haka ma ba ta san nan Sumayyan ta yo Sumayya na shirin sake jijjiga Dije Ramma ta k araso wajen ta rik e mata hannu ta ce haka nan take tun safe, ki d aga mata k afa ki barta yanzun ta d an nutsu tukunna. Tsananin tausayi ne ya sanya ta sake rushewa da wani kukan kawai ta kifa fuskarta akan cinyar Dije ta ci gaba da rera shi kamar an aikota. A wannan gab ar kam sai da suka saka Ramma kuka dan Inna ma hawaye ta fara haka shima Ya Muhammad wanda basu gama fahimtar mai ya saka shi kukan ba tunda shi dai ba magana yake yi ba. Sosai d akin ya komo kamar na zaman makoki dan in banda sheshshek a da sautin kukan Sumayya babu abunda yake tashi a cikinsa. Innalillahi wa Innailaihirrajiun Sautin muryar Kaka ta karad e ko ina sai kuma kukanta ya cika kunnuwansu mai matuk ar sauti da firgitarwa. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 28. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Dije ce ta fara mik ewa tsaye zumbir! Amma hatta makwafta sai da suka rigata isa tsakar gidan ita da Sumayya wadda ta rik e mata hannu tana janta da k arin ganin sun k arasa fita tare. Suna Isa bakin k ofa Dije ta fara jiyo sautin kukan Inna itama ya fara tashi, ga na Asabe ga na Yaran gidan har da su Kubra dan haka ta jaa ta tsaya ta rik e hannun Sumayya g am! Kamar wata zararriya sai kuma ta fara magana a gigice bari in gaya miki abinda ya faru, dama d azu na ji Mallan ya ce hanya babu lafiya to yanzun na san accident ya yi ko kuma Ma a ne ya kashe sa, idan muka fita kika ga ba haka bane ba Sumayya ki wanka min mari! Saboda ba ni da tantama hakan ne, gawa zan gani! Sumayya wata gawar makusancin nawa zan sake gani a yau shikenan Da sauri Sumayya ta rungume ta ta saka hannu ta toshe mata Baki ta saki wani irin kuka mai cin rai. Yadda aka d aga labulen d akin aka finciko Dije zuwa waje sai da ya yi matuk ar tsorata Sumayya. Da kyar ta iya rik e kanta bata zube a wajen ba, tana d agowa aka d auketa da wani irin mari sannan aka shak eta. Sam Dije ba ta yi kokawar kwatar kanta daga hannun Asabe ba dan tabbas ko da ace Asabe ba ta kashe ta ba to ita zata kashe kanta, ta gama tsara hakan tun lokacin da aka fincikota idanuwanta suka sauk a akan wani k onannen mutumi bak irin (hatta kamanninsa sun b ace) kwance a kan taburma yana janyo numfashi da kyar. Wanda take da tabbacin shine dan ga rawaninsa nan yashe a gefe wanda ta sanshi da shi duk ya k one da kyar ma ake iya ganesa. Lumshe idanuwanta ta yi kawai ta saki jikinta Asabe rik e da wuyanta tana wujijjigata tana gwara kanta da bango tana tsine mata. Da kyar Ramma da Mama suka fincike Dije daga hannun Asabe, rashin kuzari a tattare da ita ya sanya ta tafi Yaraff!! Ta zube a wajen. Cikin mad aukakin b acin rai Ramma ta ce iyar Ina ce ke? Ce miki aka yi kin fita jin zafin abinda ya samu Mahaifin nata ne ko yaya? Za fa ki iya chanja shi ita kuwa ba za ta tab a samun kamar sa ba. Haba mana dan Allah ku dinga yiwa kanku adalci mana! Daga abu d aya ya faru kuma shikenan ko wanne bala i idan ya kunno kai sai a ce ita ce saboda tsabar dabbbanci irin naku! Ina ce d azun nan na ji ana cewa Kaka hanya babu lafiya amma ta ce ya taho a haka kuma shine saboda tsabar rashin adalci sai ku ce Dije ce sanadi, ki gaya min had in Dije da wannan al amarin ai idan akwai wadda za ki tuhuma to Kaka ce tunda ita ta ce duk tsiya duk bala i ya taho a yau ba sai gobe ba. Ta yi maganar ta na mai kallon Kaka fuskarta na baiyyana tsantsar b acin ran da take a ciki. Saboda haukar ta su ta fara isarta. Kawu Isa wanda duk ba su ma lura da shi bane ya yi gyaran murya sannan ya ce ki bari ki ji kan labari kafin ki yanke hukunci Ramma Duk waigowa aka yi aka zuba masa ido fuskarsa shima ka na gani ka san ya ci kuka. Kamar ya in ji Ramma ta yunk uro masa rai a b ace amma sai wayar da ya kunna recording ta yi saurin katseta jin muryar Mallan tarr suna waya da Kawu Isa Ka taho ne? Kana Ina? Tun d azu wayarka ba ta shiga asa-k asa murya na rawa cike da tsoro Mallan yake magana ta inda yake cewa da na taho matsalar network ne, a tasha kuma bayan na sauk a har na fito bakin titi zan tari abun hawa ya kawoni gida sai na ga Ma a shi da waensu irinsa a tsaye sun fi su biyar. Ya ce min ni yake ta jira tun safe akwai muhimmiyar maganar da yake so mu yi ni da shi . Ban so na bishi ba amma sai na ga kamar Yaran nasa suna shirin yi mini illa shiyasa na yanke shawarar binsa. Wani gida suka kaina, to kuma har ya zauna zamu yi maganar sai aka shigo aka gaya masa wata magana a take ya mik e suka fita a gigice. Dawowarsa ke da wuya kawai sai ya dawo min a buge kuma shi kad ai, har yana ik irarin sai ya kasheni! Daga haka ya fad i a wajen. Allah ya so daga ni sai shi ne a d akin ragowar suna harabar gidan, dan haka na yi saurin guduwa ta wata k ofa a bayan gidan. Yanzu haka gani nan a chan gaba da kwankwasiyya estate ka yi sauri ku zo ku taimakeni dan Allah dan na ji kamar sun farga sun biyoni. Dai-dai nan ya katse kiran da sauri, recording d in ya k are. Cikin kuka sosai Kawu Isa ya ce ko da muka je bamu tarar da komai a wajen ba sai k onannen Mallan. Su Ma in sun gudu. Ban kaishi asibiti ba dan na yi tunanin ya cika, sai yanzunnan kuma na ga ya fara numfashi da ikon Allah. In banda sheshshek ar kuka da salati babu abunda yake tashi a cikin gidan. Sai da aka d an d auki lokaci tukunna Kawu Isa ya d aura da cewa tunda na ji shiru dama na san da walakin shiyasa yana kirana na yi saurin saka recording, saboda an had ani da waensu y an sandan dama masu aiki gaskiya da gaskiya an ce Wuyarta in kai sheda garesu in sha Allah idan suka gark ame Ma aruf to babu wanda ya Isa ya fito da shi. Tun ranar da Yusufa ya bar duniya ban zauna ba, da Mallan ya bani labarin yadda Ma in yake ta bibiyarsa sai na sakawa abun ido, to d azun ma da ya kirani na d auka ko biyosa ya yi ko kiransa ya sake yi duba da yadda ni da kaka muka yi ta nemansa baya amsa waya, ashe ransa yake nema. Ya k arashe maganar yana mai fashewa da kuka. Gaba d aya wani sabon kukan aka sake a tare banda Dije wadda kukan nata ya jaa ya tsaya chak. Inna ce ta mik e da kyar jiri yana d ibarta tana ganin dishi-dishi ta shiga ta d auko purse d inta da take da y an kud e a ciki ta ce mu kaisa asibiti, zama a nan ba zai yiu ba. **************** Wari! Hamami! K arni had e da wani irin azababben d oyi ne yake tashi a cikin d akin. Durk ushe take a bakin gadon ta kama hannunsa tana wani irin kuka mai tsananin cin rai. Yayinda ita kuma gawar tasa take nan kwance a kan gado har yanzu sanye da fara k al d in alkyabba mai tsananin kyau da tsada. Kasancewar sa fari tas ya sanya ake iya ganin yadda ya fara komawa kore-kore gashi ya kumbura sumtum! Gaba d aya halittarsa ta sauya. A hankali cannular da aka saka masa a jijiyar hannun nasa ta zilmiyo ta zamo ta fad i a kan gadon. Da sauri Likitocin da suke a tsatstsaye a bakin gadon suka sunkuyar da kawunansu kowa ransa babu dad Da sauri Gimbiya Zakiyya ta tashi daga kan sofar da take a kai ta fice da ga cikin d akin gaba d aya tana hawaye, bakinta toshe da hannunta. A karo na babu adadi Nuraddeen wanda shima ya ga fad owar cannular daga hannun gawar ya sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya matso ya sake tsayawa a dai-dai kanta ya ce ranki ya dad e, abubuwa sun fara fita daga jikinsa alamun ya fara sacewa, ki bari a yi masa wanka a kaisa makwancinsa kar ki wulak anta gawar mutum mai martaba kamarsa. agowa ta yi ta mik e tsaye a fusace ta ce Nura na ce kar ka sake ce mini ya rasu ko??? Sai kuma ta yi gaba alkyabbarta tana jan k asa tana hard eta cikin sassarfa mai kama da gudu-gudu ta k arasa wajen babban Likitan tana zuwa ta damk i kwalar rigarsa gefe da gefe da hannayenta duk biyun ta ce why are you just standing here? Tell them he s still alive!! Tell them that my son is not dead!! They are going to bury him alive, don t let them do that. You promised to save him, tell them he ll soon open his eyes and see the lights again. Ganin ba shi da niyyar kula ta ya sanya ta koma kan d ayan ta ce
Chapter 55 · 0% Book details