Sashe 42
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamal ya rasu? Haba Halima kar ki yi tunani irin haka mana! Sannan kina tunanin idan Dije bata a gidan wani Ma ah zai barmu mu sha ruwa ba tare da mun aura masa ita ba? Idan ma ya bari so kike ta k arashe rayuwarta babu aure kenan ko yaya!? Saboda ba ka so y arka ta k arashe rayuwarta babu aure sai ka yi ta yin silar rasa rayukan wasu? Ta yi masa tambayar a d an zafafe. A hankali ya matso ya kamo hannayenta biyu ya ce Halima duk abunda kika ga Ina yi shine dai-dai, a da nima na so in sare amma kamar yadda Kamal ya fad a hakan ba ita ce mafita ba, sannan idan fa bamu yiwa tufkar nan hanci ba to tabbas akwai babbar matsalar data fi wannan da muke ciki yanzu a gaba, abunda nake so da ke shine ki yarda da ni, in sha Allahu babu abinda zai sami Kamal, za su wuce garinsu Minna shi da ita a yau ko gobe dan haka kawai ki bisu da addu Daga haka ya juya ya fita kansa yana wani irin sarawa jiri yana d ibar sa ai kuwa yana shiga d akinsa ya zube. ****************** Kamar kullum yau ma da safe fada ta cika mak il an zo kwasar gaisuwa, kowa ya sha ado na gani na fad i, gold a jikin matan nan kuwa kamar ruwa ko ina hannu k afa yatsu wasu har da goshi da gefen hanci. Sosai abunda Gimbiya Mariya ta yi yauma ya sake fusata wasu dan tabbas abun nata dole ya tab a kowa tunda ya shafi Giwar Mata, wai dan an turo ta a wheelchair shine ta ce sai dai a koma da ita duk lokacin da ta warke sai ta tako ta zo da k afarta. Matar ba ta wani kula ta ba dan ita zuwa yanzu takanta take yi rashin lafiyar yau daban ta gobe daban jikin tsufa, Hakanan aka juya da ita ai kuwa ta k arawa kanta ba in jini a wajen dayawa yayinda wasu kuma mugun k ullin su a kanta ita da d anta ya nunku. Sarki yana shigowa kowa ya shiga bashi girma kamar yadda aka saba, sai da ya k arasa wajen zamansa tukunna aka d an nutsu da kirari dai-dai lokacin da wannan farin kyallen yake sauk owa, ya rufe sa ruff shi da kujerar tasa ta yadda duk kwakwar mutum bai Isa ya ga komai ba. ida yana zama idan ya gama kimtsawa to shine da kansa zai danna wani abu a jikin kujerar tasa kyallen ya yaye wanda a kullum da sauk owar kyallen da zamansa da yayewar kyallen baya kai mintuna biyu cikakku amma gashi yau har an haura mintuna goma shiruu A hankali k us-k us d in mutane ya fara tashi a cikin fadar yayinda hankulan wasu ya yi chaaa! Wasu kuwa kamar su kurma ihun murna dan suna da tabbacin hak arsu ce ta cimma ruwa. Wasa-wasa sai gashi har ana shirin shiga mintuna talatin dan haka Gimbiya Mariya ta mik irjinta yana dukan uku-uku ta k arasa wajen. A hankali ta sa hannu ta tura labulen ta shiga wajen wanda shigarta ya yi dai-dai ta kifewarta a wajen, sumammiya. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 21. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. A take Fadar ta hautsine yayinda Wambai Waziri da Galadima suka mik e daga wajajen zamansu suka k arasa suka shiga wajen a gigice. Shi kansa Wambai sai da Galadima ya ruk osa tukunna da kyar aka samu ya dedeta bai sume musu ba. Amintattun Hadimanta aka kirawo suka zo su biyar suka sauk o da ita yayinda kan kowa a wajen yake a k asa masu kuka suna yi. Sai da suka zo tsakiyar Fadar da ita tukunna Likitocin dake a cikin Fadar waenda aka yiwa kiran gaggawa suka matso aka d aurata a gado suka wuce babban asibitin masu mulki da ke a cikin masarautar da ita. Hatta bayin da ke a zazzaune cikin Fadar 24/7 sai da aka sallamesu aka tabbatar da kowa ya watse tukunna aka kawo wani gado mai rumfa tsakiyar Fadar su Wambai da Gimbiya Zakiyya suka d auko Sarkin wanda ya wani lankwashe ya yamushe tashi d aya k afafuwa da hannayensa suka shanye ya koma d an mitsitsi sannan a sume, suka d aurasa a kan gadon aka wuce Gidansa direct da shi dan a chan za a jona komai a kula da shi secretly har Allah ya bashi lafiya saboda gudun fitar zance Tafe take cikin shigar b adda kama tana ta sauri kamar zata kifa. Daga ita sai amintacciyar hadimarta ne suka yi wannan fitar dan ko a cikin amintattun Hadiman nata waenda ta yarda da su su uku da wannan guda d ayar tak wadda suke tafe tare yanzun ta yarjewa tasan akwai alak a tsakaninta da Nuraddeen. Kusan da Daji za a kira wajen dukda kuwa a tsakiyar gine-ginen main cikin masarautar yake amma wani irin fili ne mai d auke da wasu irin shekararrun bishiyu manya-manya waenda a k alla sun kai guda d ari!. Kutsawa take yi ta cikin bishiyun nan kamar zata kifa, da k arfi ta ji an finciko hannunta bayan wata makekiyar bishiya, da farko Hadimartata bata gane shi d in bane ba sai da ta lek a tukunna ta fahimci shi d in ne dan haka ta jaa baya ta koma ta tsaya. Bai jira ko gaisawa sun yi ba ya ce amma ba ki kyauta mini ba this time around gaskiya! Tun da har kika ji na ce miki ki jira ai kinga kenan akwai dalili..akwai abunda nake so in samu kafin a k arasa shi ko? Ko kin fi ni son ganin ya kauce ne? Ya k arashe maganar tashi a d an tsawace alamun ranshi ya kai k ololuwa wajen b aci dan da gaske a fusacen yake saboda Allah kad ai ya san kalar matsala da delay d in da kwanciyar Sarkin nan ta yanzu zata janyo masa, gashi ga dukkan alamu ba lalle ma ya tashi ba. Sai da ta sauk e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta fincike hannunta wanda ya ruk o ta ce da fari dai ka san tsawa daga gareka a gare ni bata da mazauni ko? Shiruuu ya yi yana kallonta itanma shi ta tsare da dara-daran idanuwanta tana jiran apology Da gaske yake yana sonta kuma kamar yadda yake son abu mai matuk ar mahimmanci daga wajen Gimbiya Mariya to haka itama wannan, besides she s not completely useless, dan haka ba dan yana so ba ya ce mata sorry Yana mai kawar da kansa gefe dan sosai ta kafesa da ido kamar mai shirin rufesa da duka. Numfashi ta fesar kafin ta ce ban yi komai ba! Saboda ka sanni ba na magana biyu dan haka ka yarda ko kar ka yarda tun daga lokacin da ka yi mini bayani na dakatar da komai yanzu ma haka zuwa na yi in yi maka maganar cewa akwai matsala amma tunda ba kai bane ba shikenan. Tabbas ko ma waye ya jik a mana aiki. Saboda hawanka kan karagar mulkin nan ba tare da taimakon abun hannun Mariya ba it s impossible.. Shiruu duk suka yi kafin chaan ta ce bari in je, za a zo nema na zuwa anjima Ina da bak Da sauri ya ruk o hannunta ya ce ban gaji da gan.. Dan ya lura har yanzu a fusace take, kuma da gaske bai gaji da ganin nata ba. Cikin katseshi ta ce Plss Nuraddeen, mu ji da abunda ya ke a gabanmu yanzu dan akwai matsala tafe kuma muddin ka bari Sarki ya mutu ba tare da Mariya ta baka abunda ta yi alk awari ba to ka san cewa da kai da babu duk d aya. A wajena da wajen kowa ma dan haka ka yi lissafi mai kyau ka nemawa kanka mafita. Tana gama fad in haka ta juya ta wuce fuuu kamar zata tashi sama bayaga Nuraddeen mutane hud u ne manya a masarautar ta san sunada k udiri irin nata kuma duk ta bincike su ta k ashin k asa ta gano ba su bane ba, to wai waye haka wanda ya aikata musu wannan d anyen aiki haka cikin bazata! Tabbas an had a mata jagwal Tana wannan lissafin ta wuce ta barsa a wajen.. Ya dad e a wajen kafin chaan ya furzar da iska a fili ya ce za ki shigo hannu ne! Duk wannan izza da rashin kunyar taki za ta kau ne za ki yi bayani Sai kuma ya shiga tunani tare da lissafin waye ne mai wannan d anyen aikin haka? Tsaki ya yi ganin yana shirin bawa kansa headache ya ce ko ma waye za a nemo sa ne Dan ya san dole da had in bakin Baiwa/Bawa ko Bafade ko Dogari aka yi aikin nan, kuma yin aiki da su ka barsu a doron k asa hatsari ne babba! Kai ko da ace ma ka kashesu dole a gano gaskiya ta hanyar wani ko wata d an uwa ko Abokinsu dan basu iya rik e sirri ba gasu da shegen munafurci! Gashi idan aka fara bincike a cikin masarautar har hanji ko Ina sai an dubo an gano gaskiya. Idan kuma aka gagara aka mak ale a taso mai gaiyya mai aiki ya bincika wanda in dai a k asar KHAK IL aka haifi mutun aka binne cibiyarsa kuma ya aikata laifin to fa dole sai an gano a cikin kwarya. Shiyasa su suka tura tsohuwar Jakadiya ta nemo musu waenda bama y an k asar ba ta yadda suna gama yi musu aiki za su aika su lahira kuma duk kwakwar mai gaiyya bai Isa ya iya gano su ba tunba ba a k asar aka binne cibiyarsu ba, sannan za su tsoratar da su ta yadda ba su Isa su yi sirri da kowa ba idan ba su d in ba *************** Sai da Minu ya dawo da daddare tukunna aka san halin da Malllan ya ke ciki. Sosai hankalin kowa ya tashi dan sam ko motsi ba ya yi dan haka aka wuce da shi emergency direct