Sashe 38
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
nan tun kafin fita ta gagareta, mutane sun yiwa abun hukunci da wuri wanda ba su da tabbacin Ma ah d in ne ya yi tunda ai bai ma san adreshin Yusufan ba ka ga kuma ba zai yiu ace ya nemo ya yi shiri ya je ya kashesa a cikin kwana d aya tak! Da ya ji labarin auren nata ba. Jinjina kai Mallan Manniru ya yi, duk da cewa Dije ta kasance k awa, babbar k awa ma kuwa ga y ar sa har ga Allah dama ya dad e yana harin Yarinyar. Yanzu kuwa ga dama ta samu, dukda kuwa wanchan al amari da ya faru da Yusufa yana d an firgita shi amma sai ya tuna ai basu da tabbacin hakan ne, dan haka ya d ago ya kallesa ya ce Na amince Jinjina kai Mallan ya yi cikin jin wani relief yana sauk ar masa ya bashi hannu suka sake gaisawa ya ce na baka Khadijah, kar ka damu da duk wata bidi a sadakinta kawai za ka mik o a d aura muku aure yanzu. Bari in nemo shaidu sai a k arasa masallacin Murmushi Mallan Manniru ya yi irin ta jin kunyar surukantakar nan, sannan ya d an sosa bayan kansa ya ce da wuri haka Mallan A hankali gaban Mallan yana fad uwa dan so yake yi kawai ya ga ya d aurawa Dije aure ya ce In sha Allah Jinjina kai ya yi ya ce to shikenan babu damuwa amma bari in je in sanarwa Mahaifiyata da iyalina in ya so daga nan ko bayan la asar ne sai a d aura Daga haka suka yi musabaha ya juya ya wuce zuciyarsa fes, tabbas ya san ya tsinci dami a kala! Mutane suna ta tunanin wani abu daban gashi shi zai Angonce kuma ya san in sha Allahu babu abunda zai same shi, shi fa dama tun lokacin da ya ji batun rasuwar Yusufa da aka ce Ma ah ne sam abun bai kwanta mas a ba, dan ya yi kamar tatsuniya ko wasan Yara Yana wannan tunanin ya k arasa gidansa, mai d auke da d akuna bakwai inda yake da Mata uku Y a ashirin da bakwai da Mahaifiyarsa duk a cikin gidan kuma da ikon Allah sana arsa an kantin ne ta inda yake sayar da kayan kanti, da shi yake ciyar da iyalinsa da taimakon mata da y ansa waenda suka kama sana a ba da wasa ba dan kaff cikin su babu mai zaman banza, hatta d an k aramin Yaronsa mai shekaru biyar yanzu haka yayunsa maza da suke d aki d aya sun fara tafiya wajen da suke fenti da shi yana kallo dan a samu ya koya da wuri. Mallan ya so ya b oyewa Inna dan yana jin tsoro kar ta hana, shi kuma har ga Allah shi kad ai ya san me yake hangowa a future d in Dije muddin ba su yiwa tufkar hanci da wuri ba, amma kawai sai ya zab i ya gaya mata. Dan haka ya koma gefe bai bari ma ya shiga gidan ba ya kirata a waya ya shaida mata batun auren Dije da Mallan Manniru wanda za aura a yau in sha Allah , daga nan ya d an bata haske akan dalilinsa na yin hakan. Tabbas bata so had in ba dan ko babu komai Mallan Manniru Mahaifi ne ga k awarta kuma matayensa duk mutanen kirki ne ana shiri da su matuk Amma fa Hausawa sun ce so so ne amma son kai ya fi! Shiyasa Mallan d in yana gaya mata abunda yake hange da yadda ya rasa samawa Dijen Miji a Getso ma duk sai jikinta ya yi sanyi ta yi shiruuu kawai kafin ta ce Allah ya zab a duk abunda ya ke alkhairi Tana baro kitchen inda ta gama wayar ta nufi d aki. Tana shiga d akin ta tarar da Dije da Sumayya baiwar Allah tana ta rarrashinta yayinda ita kuma ta kafe k unshin hannunta da kallo tana ta zubar da hawaye. Tausayin su ne ya rufe Inna duk su biyun dan haka kawai sai ta juya ta bar musu d akin ta fito tsakar gida ta nemi waje ta zauna ta rafka uban tagumi.. Ba ta dad e da zama ba Iyya ta fito ta dinga rarrashinta tana bata baki .da kyar Inna ta ke iya danne zuciyarta ta hana kanta yin kuka, abubuwan sun yi mata yawa ne Astaghfirullah ga Ya Muhammad chan a kwance bai ma san Ina kansa yake ba, Likitoci sun ce a yi addu a kawai, ga kyarar da Kaka take yi mata dan Wallahi kawai pretending take yi amma abun yana masifar damunta, sannan ga Mallan wanda kwana biyun nan daga ya yi wannan idan ta kawar ta share sai ya sake yin wani, gaba d aya zaman nasu ya k i yin dad i ko wannensu a gigice, yanzu haka ma da ya kirata highlight kawai ya yi mata kuma da ta tambayesa ya dawo ne? Ko yanzu ya taho? Nan ma bai gaya mata ba, Mallan d in da a da ko kaya in zai saka to tare suke zab a amma yanzu ta lura kamar har da b oye-b oye ma ya fara shiga cikin lamarin nasu, ta yi masa uzuri tabbas saboda halin da yake ciki amma kuma abubuwan sun kasa fita daga kanta. Tana cikin wannan tunanin ta ga an fito da Ramma tsakar gidan an shimfid a mata tabarma an kwantar da ita, hannun nan ya yi suntum! Ita kanta ta kumbura dan jiki take ji ba kad an ba! Asabe itama hannun ya yi muni amma ba wani sosai ba dan tana ma iya yin komai dukda anata hanata saboda gaba amma ta k i ji idan ka ganta ras kamar ba mai jinya ba komai yi take yi dan bayan hannun ne ba ciki ba yayinda na Ramma ya munana sosai..D an koyo ne ya d aurata a gida ashe ba dai-dai ya d aura ta ba, dama tun a ranar Iyya take ta ce musu su kaita asibiti d aurin bai yi ba amma aka k i ko da yake saboda rashi ne da babu dan in aka je asibiti kud in kati ma ba lalle su iya biya ba. Sai d azu ne tukunna aka gane ashe d aurin bai yi ba to yanzu dai an kira wani kwararre zai zo ya gyara. A gefenta y an suka zauna, sun saka ta a gaba wanda su kad ai suka san halinda suke ciki dan ba iyaka tashin hankali ba ko da yunwar cikinsu aka barsu ta ishe su, rabonsu da abinci tun jiya da safe wanda Iyya ta zuba musu. Ita Inna bata san basu da kayan abinci ba da zata basu ko da iyakacinsa kenan gareta dan kaff gidan ita da Iyya ne kawai basu da rowa. Gashi su matan basu iya sana ar komai ba uwar kuma da take komai gata a kwance. Usama ne ya kwanta a wajen yana ta faman murk ususu dan shi kam hak urinsa ya k are zuwa yanzu, Inna tana shirin yin magana Hajiya Uwani ta shigo cikin gidan a fusace Suwaiba a bayanta tana ruk ota tana cewa ki tsaya mana. Kar ki yi haka dan Allah, tsaya ki ji Ita kuma tana cewa ki rabu da ni fa! Ki bar ni in jaa musu kunne ramin kura daga ita sai y anta wallahi bakin rijiya ba wajen wasan Makaho bane ba, ba zan zauna in nad e hannu a cuce ni ba! Firfitowa na cikin d akin suka fara yi, kafin ka ce kwabo tsakar gidan ya cika tap! Hatta su Sumayya wadda suke d aki tare da Dije. Tunda Uwani ta shigo dama Inna ta sunkuyar da kanta k asa dan ta san labari ya iske mata kenan. Idanun matar yana sauk a a kan Inna ta ce muguwa azzaluma!! Butulu! Makira Da kika san duk wanda ya ko kalli y arki kamar ya yanki tikitin mutuwa ne ai sai ku hak ura da aurar da ita ko kuma ku bashi shi d in ya aura kawai, amma shine tsabar muguwar zuciya irin taku za ku mak alawa Mijinmu? Mai ya sa ba kwa jin tsoron Allah ne?? Rass!! Gaban Sumayya ya yanke ya fad irjinta ya fara bugawa, a hankali ta zamiye hannunta daga cikin na Dije ta k arasa inda Mahaifiyar tata take tsaye ta ce me ya faru? Wanne Baban ne zai auri Dije? Cikin b acin rai wanda yake had e da firgici da tsoro ta ce Baba ubanki mana! Ina da wani Mijin sama da shi ne? Shi ne dan tsabar nemawa Kai aka bashi wannan masifar ta yi maganar tana nuna Dije, sannan ta d aura da cewa shi kuma ya amsa, wai anjima bayan sallar la asar za a aura masa ita. Da k arfi Inna ta runtse idanuwanta tana dad a danne zuciyar da take tasowa take yunk uro mata, dan sosai ta kawo iya wuya (mai hali a duk halin da yake ciki halinsa halinsa ne). Juyawa Sumayya ta yi suka had a idanu da Dije, a hankali Dijen tana hawaye ta shiga girgiza mata kai alamun ita babu ruwanta, kafin da kyar ta matsa kusa da ita ta samu ta iya furta Wallahi ban san ma me yake faruwa ba, muna d akin nan tare da ke mun fi kwana uku kina tare da ni. Kuma Ina so ki saka a ranki maganar nan ba tabbatacciya bace ba dan ba zan tab a yarda in auri Baba ba. Zancen banza ma kenan!! Abunda an riga an bashi ya karb a kuma me ya rage? Sunanki da nashi ya riga ya had u dan haka kin gama gamawa da mu! Allah ya Isa tsakani na da ke in har wani abun ya samu Mijina wallahi Allah sai na baku mamaki da ke da mugayen iyayenki Ta fad i hakan tana mai rushewa da kuka. uri jama ar gidan suka lullub eta suna bata yayinda idanun Dije suke cikin na Sumayya tana hango b acin rai yana maye gurbin tausayinta d in da take gani a cikin idanun nata, hannunta