Sashe 23
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
dama a k idarsu breakfast ma a k ofar gidan suke yi! Kuma ko Ma a zai kai k arfe d aya na rana bai fito ba to suna nan ba zasu je koina ba ruwa! Iska! Rana ba su isa su tashe su a wajen nan ba har sai sun ga fitowar Ogansu. Yana fitowa suka mik e suka hau ife-ife suna sara masa, tapping shoulders d insu ya yi suka gaggaisa idanuwanshi a kan y ar k urar da aka kawo masa rake a cikinta himini guda! In sha Allahu zai tsaya ya yi sana ar nan tsakaninsa da Allah Ya aiyyana hakan a cikin ransa dan da farko su Oscar sun shirya ne akan Ana kawo raken za su dinga rabawa gida-gida dole kowa ya karb a ya bayarda kud i ko kana sha ko baka sha shi Ma in ne ya hanasu ya ce a kafa trader duk mai son siya ya zo ya siya. Kamar daga sama suka ji jiniyar y an sanda, kafin ka ce kwabo layin ya d inke mak il da motocin y an sanda har da wasu masu kayan sojoji a tare da su. Suna zuwa ba su yi wata-wata ba masu kayan sojojin nan su biyu suka yi kanshi suka datsa masa ankwa aka tafi da shi. Sai da suka tafi da shi tukunna aka gane ashe wannan sabon magidancin da yayiwa b alli b alli kwanaki ne y ansa suka kai k ara shine aka zo aka tafi da shi. Tun da y an Unguwar suka ji labari haka nan Mata da samarin layi suka dinga sintiri a gidan suna basu shawarar Wallahi su tashi kafin Ma a ya dawo Unguwar tun wuri su san inda dare ya yi musu Amma ba su ji ba! Babban d an mutumin ma ce musu ya yi su saka a ransu inda ya kai Ma a ba wajen da zai je ya fito ko da nan da shekaru goma bane ba! Ya tafi kenan har abada shi zai kawo k arshensa, su zuba ido su gani! Ganin mutanen masu taurin kai ne ya sanya aka hak ura aka zuba musu ido kowa ya bisu da addu a kawai sannan kowa ya ja y ansa samari Yara da y an mata zuwa gida aka rurrufe koina dan sun san tabbas yau akwai world warr 3 a Unguwa Uku. Dole ce ta fito da Dije daga gida dan har yanzu Baba bai dawo ba Ya Aminu shima kuma shiru gashi basu da ko sisi a gidan dan kud in adashin Inna ma duk an had a jiya ya tafi a asibiti, hakan ya sanya ta cewa Dije ta je gidan wata k awarta a bayan layinsu ta karb o mata ranchen dubu biyu ta kawo mata ta je asibitin kawai da kanta ta ga me yake faruwa. Sun dai ji anata hayaniya k asa-k asa d azu a gidan amma ba su san me yake faruwa ba da yake throughout yau d in suna d aki shiyasa ma Inna ta barta ta fita. Ta karyo kwana kenan da yake gidan k awar Inna a layin gidan mutumin yake ta hango Babban d ansa ya tara samari yana ta cika baki da zage-zage! Har da cewa Baya gari lokacin da abun ya faru ne shiyasa Ma a ya samu har ya yiwa Mahaifinsa hakan sannan bayan ya dawo rashin lafiyar ubansa ce dama ta sa bai kula Ma a tun a ranar ba amma yanzu kuwa tunda ya waiwayeshi Wallahi kashinsa ya bushe su saka a ransu ya tafi kenan har abada. A ranta ta ce Allah ya sa! Ma a ko masifa. Da gudu ta ga wata mota ta shigo cikin layin wanda hakan ya karkato da hankalin gaba d aya jama ar wajen ..da ikon Allah personal motar dpo d in police station d in da aka kaisu suka tuk o, Oscar shi ke driving sai Scorpion da wani daban a gaban, yayinda shi kuma Ma a yake a baya ya hakimce ya saka wani bak in glass. Waenda Allah ya bawa ikon ganesu kafin su k araso ne suka kwasa a guje, wasu kuma basu ma san mai ya faru ba suna gani ana gudu suma suka hau gudun, ragowar samarin kuwa masu son ganin kwakwaf tsayawa suka yi har sai da Oscar ya k araso da motar wajen ba tare da ya jira ya yi parking ko ya kasheta ba ya diro daga cikin motar k ofar ma a wangale ya barta ya zaro wata zabgegiyar Adda ya shiga sauk eta a kan duk wanda ya samu. A take wajen ya hargitse in banda ife-ife babu abunda kake ji. Fitowar su Scorpion ce ta sake hautsina wajen dan suma suna fitowa suka shiga sare-sare. Tunda Dije take Allah bai sa ta tab a ganin irin fad an na su Ma a ba sai yau, ta dai san d an daba ne ya addabesu wani zubin har curfew suke saka musu a unguwa kuma babu wanda ya Isa ya fita har sai sun janye curfew d in sannan har hayar sa ake yi su je su yi kashe-kashe kuma a nan Unguwar tasu ma yana yi amma bata tab a ganin su in action suna chachchakawa mutane wuk a ba sai yau, shock da matsanancin tsoro da suka shige ta a lokaci guda na ganin yadda akeyiwa mutane kamar wasu kajin sallah ya sanya ta k ame k am a wajen ta gagara motsi, dama chan ita tana da tausayi shiyasa tun tana Yarinya take cewa ba zata iya yin Likita ba dan ba zata iya yanka jikin mutum ba .tun tana Yarinya lokacin ko layya ce ta zo duk tsagarancin Dije bazaka tab a ganinta a wajen da ake yanka raguna ta je kallo ba. Scorpion d in ne ya dawo ya zo ya bud ewa Ma a mota tukunna ya zuro afarsa ya fito daga cikin motar! Wanda fitowar tasa ta sake ruruta guje-guje da ife-ifen jama Direct wajen d an mutumin ya nufa wanda har yanzu yake a tsaye a cikin riller gidansu ya saka sakata ta ciki yana waya da alama y an sandan yake sake kira. arasawarsa wajen ta yi dai-dai da k arasowar Mahaifiyar saurayin, tana zuwa ta tsinka masa Mari ta ce inace daga wajensu ya tsinko ya taho amma shine ka tsaya a waje kake sake kiransu? Wuce ka shiga cikin gidan kafin su yi maka illah! Ita ba ta ma lura da Ma a ba dan duk ta rikice sai da ta ji ya saka k afarsa ya daki riller dai-dai wajen sakatar da wani irin mahaukacin k arfi a take k ofar mai raga-raga ta dare biyu. Ihu ta saka ta fara rok onsa amma ko kallonta bai yi ba ya sa hannu ya shak o wuyan saurayin nan ya d ago shi kamar wani kayan wanki ya fito da shi ya dire sa a gabansa. Wani irin wutar bala i da tsananin fushi da b acin rai Saurayin ya gani a cikin kwayar idanun Ma a ga wata masifar shak a da aka yi masa da ta sanya yake ji kamar yanzu-yanzu zai bar duniya dan haka gaba d aya sai ya fita a haiyyacinsa idanuwansa suka fara k afewa. Kuka sosai matar take yi, cikin mad aukakin tashin hankali ta fito daga cikin barandar gidan nasu ta zo ta fara k arin kwatar d anta amma cilli d aya Oscar ya yi da ita tunda ta tafi ta kifa ta kasa tashi sai wani irin kuka da ta dinga yi. Wata zabgegiyar wuk a Ma a ya sa hannu ya zaro daga k ugunsa tana wani irin kyalli ya d aga sama ya kalleta! A take uwar saurayin ta sake gigicewa fad i take a, A a! A tana mai k arin tashi amma ta kasa dan a kan k afarta ta fad Cikin saurayin Ma a ya kalla kafin ya saita wuk ar ya soka masa ita! Sai da ta lume ciki gaba d ayanta. Tashi d aya matarnan ta shak i numfashin tashin hankali ta sume a wajen. Ido cikin ido suke kallon juna shi da Saurayin nan wanda har yanzu bai cikawa wuya ba ga kuma wuk a ya chaka masa a ciki yana k akarin mutuwa yana kallonsa. Cikin wani irin zafin kai ya fara juyi da wuk ar nan tana a cikin cikin saurayin a haka sai da ya yi juyin 360 da ita a cikin cikinnasa tukunna cikin wani irin zafi yana kallonsa ido cikin ido ya ce Ka yi kuskure! A kaff fad in Unguwar nan Ana Malik! Kai a kaff garin nan ma Ana Malik!!Infact a Nigerian ma gaba d ayanta i m untouchable!!! Ina so ka saka hakan a ranka ka dinga amfani da shi har zuwa k arshen rayuwarka idan kuma Allah ya sa k arshenka kenan Allah ya ji k an ka. Yana gama fad in haka ya sakeshi ya zare wuk ar at the same time ai kuwa jini ya hau ambaliya fiye da farko yayinda saurayin ya tafi luuu ya fad i kansa ya bugu a jikin dakalin barandar tasu. uwar tasa ta yi dede da fad uwar Dije wadda sai da ta gama juye fitsarin mararta a wajen tsabar tsoro tukunna ta tafi ta fad i sumammiya a wajen. Yana juyowa idanuwansa a kanta suka fara sauk a ga fuskarta nan zagaye fayau cikin brown d in hijabinta har k asa. A hargitse ya juya ya kalli Oscar cike da tashin hankali ya ce me kuka yi mata? Ya yi masa tambayar yana mai nufarta. Rufa masa baya ya yi yana yi masa bayani a kan tun d azu take tsaye yanzu kuma kawai ya ga ta fad i, ai sun san ya yi musu iyaka da ita da y an gidansu wallahi basu tab ata ba! Sam Ma a ba jinsa yake yi ba dan hankalinsa ya kai k ololuwar tashi saboda yadda ya ganta a yashe a k asa kamar marar rai! Yana zuwa ya shiga duddubata sai da ya tabbatar babu wani rauni a tattare da ita tukunna ya kinkimeta ya nufi motar da suka zo da ita gaba d aya ya rikice