Sashe 13
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dije duk shakkarta da suke yi sai da suka ajjiye tsoro a gefe suka gwabza da ita. Ko breakfast ba ta tsaya yi ba ta shirya tsaf ta fito tana ta sauri dan suna da punishment d in da aka basu za su k arasa yau ita da Sumayya, wanda laifinta ne ita kad ai amma aka had a da Sumayyar ta shigar mata suke yi tare. Gashi ta san sai ta biya mata, Sumayya kuwa da nawa watak il zuwa yanzu ko wanka ba ta yi ba dole ta je ta azalzaleta su je su gama da wuri, dan ta na son samun lesson d in Literature d in da za a yi musu yau da safe, da ita za su fara waec gashi ba ta san uwar komai a ciki ba. Allah kuwa ya taimaketa dan tana fita ta hangota itama ta tunkaro gidan nasu Duk da an shiga an fita sai da y an ajin suka sanya aka raba mata aji da Sumayya tun suna aji hud u amma har yau k awancen su yana nan kullum kuma tare suke zuwa makaranta su dawo tare boko da islamiyya. Sannan kusan ko da yaushe ma ne suna tare d in dan tunda suka shiga ss3 yawancin periods d in nasu had e su ake yi a yi musu lessons d in tare dan haka kusan duk periods d in suna tare. Kowa yana mamakin wannan k awancen nasu dan sam halinsu bai zo d aya ba. Ita Sumayya sanyi ne da ita sosai sab anin Dije da ba a isa a saka mata hannu a yatsa ba ta ciza ba. angaren Dije kuwa amana da gaskiya da rashin munafurcin Sumayyar ne ya sanya ta rik eta k awance dan sam Dije ba ta k aunar munafurci gashi ba ta iya ba shiyasa kwata kwata ba ta shiri da su Rakiya dan Rakiya Fati Kubra da Mariya gaba d ayansu munafukai ne na bugawa a jarida. A hakan wai k awaye ne duk su hud un amma kowa munafurcin kowa take yi a tsakanin su, wani zubin idan fad a ya had osu aka fara bankad e bankad e sai ka ji halin nasu kamar na y an shed Suna shiga cikin makarantar suka wuce band akin direct suka fara aikinsu Dije tana aiyyana yadda za ta ci uwar Zainab dan itace musabbabin wannan aikin k azantar da take yi, fad a ne aka yi da ita ta yi mata shegen duka shine aka ce har da Sumayya aka had a aka basu punishment dan malaman cewa suka yi dukan da aka yiwa Zainab d in ya fi k arfin ace mutum d aya Yarinya budurwa ce ta aikata shi .ita Zainab tunda ita aka daka sai aka bata na kwana hud u su kuwa na sati d aya aka basu yau za su gama. an ya rage ba a basu suspension ba ma dan irin haka mostly a ajin Yara a ka fi samu ba wai su god ai god da su ba. A gajiye suka koma ajin, kasancewar sun san lesson d in malamin Hausa mai himmar zuwa ya wuce Sumayya dan da sassafe yake yiwa y an A (ajin su Sumayya) B kuma (ajin su Dije) sai an kusan tashi, shiyasa kawai suka wuce ajinsu Dije inda ake musu lesson d in literature a daidai wannan awar . har sun danno kai Dije ta jaa hannun Sumayya suka tsaya ba su shiga ba sakamokon jiyo muryar Rakiya da ta yi kamar tana munafurcin y an gidansu, ai kuwa tsayuwarsu ke da wuya ta ji Mariya ta ce yo ai ke kike wannan maganar ita ma Ina ga idan aka bibiya fa mahaukaciyar ce irin d an uwan nata. Zigidir fa ta janyota ta fito da ita daga band aki ai wallahi yau ba dan an rabamu ba da sai na nuna mata nima ban girma ba na iya haukar Yarintar har yanzu tana kaina ba ta barni ba. Dariya y an matan kusan su goma suka saka ..da yake Malamin literature d in bai zo ba shiyasa suka had a daba a nan cikin ajin suka hau sana ar ta su ta munafurci. Cike da dariyar mugunta wata a cikin y an matan ta ce Ai na ci dariya da aka ce ya biyo matarsa har waje da wuk a Astaghfirullah, shegiyar Yarinya babu yadda ba a yi da ita ba akan kar ta auresa mahaukaci ne amma ta k i, sai da ta fara jiyo k amshin lahira tukunna ta farga. Ta shafawa kanta lafiya, gashi yanzu, ran Asabar d innan za a d aura mata aure da mai hankali abinta. A hankali wata a cikinsu ta ce ni wallahi tausayi yake bani Cikin katseta Rakiya ta ce kee!!! Waennan ba abun tausayi bane ba! Ba su san Annabi ya faku ba duk cikinsu Malan ne kawai na kwarai amma tun daga kan Innar tasu har zuwa kan Dijen ba na Allah bane ba, shi kansa mahaukacin ba na Allah bane ba. Na ubanki ne??? Muryarta tsaye a kansu ta sauk a garesu. A take wasu a cikinsu suka rud e yayinda su Rakiya suka yi tsaki, suka ci gaba da hirarsu Ajijn nasu seat guda hud u ne amma mai cin mutane da yawa dan dogaye ne sosai, kuma biyu sun karye (d ayan babu k afafuwa biyu d ayan shima haka) d ayan kuma nata ne ita da Sumayya da wasu a cikin y an ajin dan haka ba a zama a kai, sai d ayan mai lafiyar shima na wata Yarinya ne maggi irin k edaran nan k atuwa masu shegen k arfi da masifa, daga Dije sai ita a masifa a kaff ajin nasu. Cikin ikon Allah su Rakiya gaba d ayansu a kan karyayyen seat marar k afa biyu guda d aya dogo suka had a wannan dabar ta su, katako kawai suka nemo suka saka a chan k arshe da kuma tsakiya inda babu k afafun. Ta riga ta san kan seat d in shiyasa tashi d aya ta saka k afa ta ingije malejin nasu ai kuwa suka taho luuuuu kamar irin sun hau super d innan suka zube a simintin k asan ajin. A zuciye suka taso Allah ya taimaka wani malaminsu wanda ya ji hayaniya ya zo wucewa ya shigo cikin ajin, shi ya raba damben da ya ke shirin kunnuwa dan duk yawansu d innan ko d arr Dije ba ta ji ba haka ta ke shirin shiga a dambatu Sumayya na rik eta ta na fisgewa. A duniya Dije tana son d an uwanta Ya Muhammad kuma tana tsananin jin tausayinsa gashi kusan kullum idan ciwonsa ya tashi to ko ita ko Inna ne sila, shiyasa take dad a jin ciwo idan jahilai suka goranta masa, sannan shiyasa take bin maganarsa take kuma kare duk wani abun da zai b ata masa rai. Wani punishment d in aka fitar da su aka sake basu, tare da bulala ashirin ashirin a dukka su goma sha hud un har da Sumayya sannan aka saka su kneel down a rana har aka tashi. A tunanin Dije idan aka tashi za su tunkareta ko su tare mata hanya dan haka ta shirya musu tsaff, sai dai su y an matan ko kallonta ba su yi ba kowa ya kama gabansa saboda sun san dambe a hanya ba nasu bane ba dad in dad awa kuma duk akwai samarinsu a Unguwar dan haka sun san sun girma sab anin ita da kwata kwata kamar ma ba ta san me ake nufi da girma da y an matancin ba tsabar yadda ta saka fad ace fad ace da dambe a gabanta. Sosai ta had iye takaici kuwa dan ta shirya yadda zata d ebo k asa ta tada k ura ta ci ubansu tunda ta san sun fi ta yawa. Da kyar Sumayya ta d an shawo kanta ta saki jiki takaicin su Rakiya ya fita daga kanta da kyar, a haka ta share lamarinsu suka d an tab a hira kafin su k araso k ofar gidan su Sumayya Dijen tana ta nanata mata sak onta da take so ta taho mata da shi daga k auyensu d in da za su je gobe gaisuwa ba za kuma su dawo ba sai sun yi kwanaki hud Ita dai Sumayya a tsorace ta ke da wannan sak o na Dije amma sanin da ta yi cewa idan ba ta kawo ba tsaf za su iya samun matsala ya sanya ta amsa mata da suka yi sallama suka rabu bayan ta yi mata Allah ya kiyaye hanya, dan ba lalle su sake had uwa ba Sumayyan ta ce kasuwa za su je yau ba za ta je islamiyya ba dama tun jiya ta d auki excuse na tsawon kwanakin da za su yi, gobe kuma fitar asuba za su yi. BAYAN KWANAKI HUD Asabar. Sai da Kaka ta yi kwana biyar a asibiti tukunna aka sallameta. Ba dan Likitocin sun so ko dan ta warke ba sai dan shegiyar tsirfa da iyayin da take yi musu kamar wata consultant, gashi ta kawo wani daga Getso shi ya gyara mata ma hannun har da cewa wai su zo su koya daga wajensa shi d in tshohon hannu ne, idan aka bata magani bata sha sai tsumin wannan mutumin kawai take sha sannan ba ta yarda da drip ba! Ganin ta cike musu waje ya sanya kawai suka sallameta suka ce ta je gida ta k arasa jinyar a chan, ba damuwa. Minu kusan shi ne ya yi jinyarta shi da Asabe dan shi yake d aukarta ya kaita bayi idan za ta yi uzuri a cewarta wai bata iya tashi ba zata iya yin tafiya ba sai ka ce a k afa ne ta samu gocewar k ashin. Sannan duk wani aike shi ne kuma da kud in sa yake yin na motaa amma hakan bai hana Kaka aibanta Inna da Dije tare da zaginsu su a gaban kowa ba. Tun yana jin haushi yana ji kamar ya mayar mata har ya zo ya rabu da ita dan tabbas zuwa yanzu ya fara yiwa Kaka kallon kwarkwar. Inna ta je sau d