Sashe 35
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
**************** A rikice sannan hankali a masifar tashe Gimbiya Sumayya ta shiga sashen Mahaifiyarta gudu-gudu sauri-sauri. A babban parlournta inda ta saba zama ta amshi gaisuwar kowa ta tadda ita Yadda take tafiya kamar zata kifa jikinta yana wani irin masifar karkarwa ne ya sanya Mahaifiyar tata ta mik e tsaye tun kafin ta k araso ta ce Gimbiya Sumayya kanki akwai motsi ne??? Kalli yadda kike tafiya kamar baki san matsayinki ba? A take duk bayin da suka rakota waenda suka sha gudu garin binta suka zube k asa suka sunkuyar da kawunansu k as, haka suma ragowar bayin da suka tadda a wajen (duk suka sussunkuyar da kawunansu k asa) Karkarwa take yi jikinta yana kyarma har yanzu ta gagara furta komai. Da kyar ta iya cewa Gimbiya Mariya.. Tana magana tana nuna waje da hannunta ba tare da ta kalli wajen ba, ta d aura da cewa ta tara mutane a babban filin rabo wai za a jefe Gimbiya Sakina! Wani irin mahaukacin bugawa k irjin Gimbiya Mai Babban d aki ya yi wanda hakan har sai da ya sanya ta durk usa ta kai k asa tsabar yadda abun ya daketa. A take duk bayin suka sake yin k asa da kawunansu yayinda hadimanta guda biyu makusantanta suka k arasa da sauri suka d agota. ayar ta fara k arin zaunar da ita yayinda d ayar ta shiga yi mata fifita tare da fad in maganganu masu sanyaya ruhi. ewa ta yi kawai ta wucesu ta zo ta wuce Sumayyar hankalinta a masifar tashe Tabbas yau kam sai dai a tsireta amma sai ta nunawa Mariya matsayinta! Yo hauka ake yi? Sakina fa y ar Sarki ce jikar Sarki gaba da baya da zata ce zata jefeta tana shaye-shaye ne? Ta yaya ma zata zuba ido ta bari a jefe mata y arta kamar wata baiwa? Wanne irin sharri ne haka aka yi mata da har zai sanya wachchar mahaukaciyar ta yi yunk urin jefeta? ..Tana waennan lissafe-lissafen ta zo ta wuce Sumayya fuuu kamar zata tashi sama. A take bayinta suka mara mata baya ita kuma Sumayya wadda ta sulale a wajen nata suka durk usa suna kururuwa gashi basu da ikon tab ata. A chaan babban filin rabo Tun kafin ta k arasa ta hango Gimbiya Sakina d aure jikin wata k atuwar bishiya jikinta babu komai sai doguwar shimi har k asa fara tas dan hatta d ankwali babu a kanta sannan duk wani abun ado kama daga y an kunne zobuna suma duk babu gasunan ajjiye gefe guda tare da kayanta yashe a gefe alamun yanzun ne aka cire mata. Dishi-dishi Gimbiya Mai Babban d aki ta fara gani tsabar mad aukakin tashin hankali da b acin ran da ya sake rufe ta! Wai yanzu y arta ce d aure jikin wannan k antacciyyar bishiyar a gaban bayi haka tsaye chak a kan k afafuwansu? Sannan on top of everything wai shirin jefeta ma ake yi!? Tana cikin wannan tunanin ta k arasa inda Gimbiya Mariya take tsaye tana zuwa bata yi wata-wata ba ta sa hannu ta juyo da ita ta d auketa da wani irin mahaukacin Marin da ya sanya kowa durk usawa a wajen kawunansu a k asa suka shiga cewa tuba take yi! Uwar sarki matar sarki a yi mata aikin gafara hannunta ne ya sub uce! A tsawace ta juyo ta ce ku rufewa mutane Baki! Sai kuma ta juya ta kalleta ta ce Garr nake ganinta kuma ban tuba ba dan ubanki! Rikicewa wajen ya yi yayinda wasu a cikin mutanen wajen suka fashe da kukan an zagi uwar sarki. Cikin b acin rai ta ce wasa ya wuce wasa amma ban da tsole idon uwar Miji da tab arya! Dan ni duk haukan nan da kike yi tun daga ranar da aka nad a Yareema a matsayin Yareema har ya kawo Sarki wallahi a matsayin wasan Yara na d aukesa, dak iya wadda bata san inda yake yi mata ciwo ba! A hankali wani Bafade ya k araso wajen shi da waensu sojoji guda biyu ya ce Gimbiya Mai Babban d aki ki gafarceni, amma maganganunki sun yi tsauri ga Gimbiya Uw Tass!! Ta d aukesa da Mari ta ce ku kuke ganinta a matsayin Gimbiya Uwar Sarki ni har gobe a matsayin k antacciya y ar talakawa nake kallonta! iff! Haka wajen ya yi ba ka jin komai sai sheshshek ar kuka, sai kuma suka ci gaba da cewa Allah ya huci zuciyar Gimbiya Uwar kowa Wata nannuyar ajiyar zuciya Gimbiya Mariya ta sauk e, tabbas sai ta gasa mata aya a tafin hannun da ya mareta, amma ba yanzu ba zata samu lokacin ta ne. Dan haka kawai sai ta juya ta kalli jama ar da ta tara a wajen ta ce Bismillah, za ku iya fara aikin lada Ta yi maganar ko kallon gimbiya Mai Babban d aki bata yi ba. Dai-dai nan Nuraddeen ya k araso wajen yana wani bubbud Nufar bishiyar Gimbiya Uwar Marayu ta yi yunk urin yi amma Sojojin nan suka hanata shallake jan layin dake zagaye da bishiyar ballanta ta k arasa ga Sakina wadda duk dauriyarta zuwa yanzu ta fara kuka. Cike da Isa da izza Nuradden ya k arasa inda take ya ce kin kuwa san me ta yi? Ko dai bakinku d aya? Ki rufawa kan ki asiri ki bar nan tun kafin a had a da ke! Cikin fushi ta juyo za ta d aukesa da Mari shima amma sai ya yi saurin rik e hannuwan nata cikin b acin rai ya ce kar ki kuskura tukunna ya yarfe hannun nata da k arfi dan har sai da ta tafi ta yi tangal-tangal kamar za ta fad i kafin ta d ago ta kafesa da idanu cike da tsananin mamaki da b acin rai tana masa kallon irin kana hauka ne? innan. Shima d in ita ya tsare da dogayen idanuwansa cike da kwarin guiwa ba tare da wani d ar-d ar ba. Ba ta shi take yi ba yanzun dan haka kawai sai ta zagayesa ta sake nufar wajen y artata, amma sai ya kalli tulin Sojoji da Dogaran da suke tsaye a wajen ya ce musu ku d auketaa a nan! Ba su yi yadda ya ce ba sai da Gimbiya Mariya ta ce musu ku d auketa aka ce!!! Tukunna wasu Sojoji guda biyu mata na masarautar suka nufeta suna zuwa d ayar ta d urkusa ta shiga k arin d aukarta dan irin jibga-jibgan matan nan ne sojojin. Hattara daiiii Muryar wani Dogari wanda suka taho tare da Wambai da Waziri ta karad e wajen Tsayawa kowa ya yi yana kallonsu, hankali ya koma kansu Suna k arasowa wajen Wambai ya ce kunce ta! Jiki na rawa Dogarin nan ya nufi wajen amma sai matar (Gimbiya Mariya) ta daka masa tsawa idan ka tsallake jan layin nan to ba zaka fito ba sai dai a fitar da gawarka dan tare za a jefe ku! Sam Dogarin nan bai damu ba haka ya fara k arin shiga wajen dan ko a mutu ko a yi rai farin cikin ubangidan nasa shine a gabansa, dukda kuwa ya san wacece Gimbiya Mariya kuma ya san me shallake umarninta ka iya janyowa. Wambai d in ne ya dakatar da shi sannan cikin b acin rai ya kalleta ya ce Saboda ba ki d auki rai a bakin komai ba? Hala kin manta wacece wannan d in ko kuwa dai kan ki ne ya juye. Takowa ta yi ta zo gabansa ta tsaya ta ce hattara dai Wambai! Ba kowacce magana ce idan ta taho maka za ka Furtata ga Gimbiya Mariya ba! Zan yi maka uzuri a matsayin mistake amma idan ka kuskura ka maimaita hakan a karo na biyu to zan hukunta ka hukunci mai tsanani dan ya zama ganganci, kuma Gimbiya Mariya ba ta d aukar wargi. A fusace Waziri ya yunk uro zai yi magana Wambai d in ya rik e masa hannu da sauri. Sai da ya d an daidaita fushinsa kafin ya ce Mai ya faru? Ba ni da lokacin da zan tsaya yi muku bayani! Sakina ta yi Laifi kuma zan hukuntata, that s final! Da kyar ya iya janyo numfashi ya fesar da bakinsa ya sake controlling kansa tukunna ya kalli Nuradden ya ce mai ya faru? A hankali ya jinjina masa kai sannan ya matso ya ce bayan dogon bincike da nazari mun gano ita ce ta saka kayan tsafi a k ashin gadon mai martaba shekaru biyu da suka wuce, ga videon ta nan lokacin da take bawa Hadiminsa wanda aka kama da laifin dumu-dumu A take ya kunna ya mik a musu wayar. Karb a suka yi jikinsu har wani b ari yake yi tsabar tashin hankali, gata nan tarr da murya da komai, dukda kuwa video d in a karkace yake kuma dishi-dishi alamun an sha wahala wajen d auka da nemosa amma kowa yana gani ya san Gimbiya Sakina ce. Turk ashi!! Tabbas ko a cikin rami idan ka yi abu a cikin masarautar nan to sai ya fito! Duk wani abu na Makirci da zaka yi in dai ka barr wanda kuka yi tare da shi to sai ya fito, kai ko ka kashe ma tabbas sai an samu leakage daga wani d an uwan wanda ya yi abun ko wani wanda ya sanshi! Dan da taimakon Oga kwata-kwata, k ungiyar masu bincike ta masarautar take amfani shiyasa duk k antar evidence sai sun ganota sun yi amfani da ita ko da kuwa bata kai girman kwayar shinkafa ba. Tabbas shima yanzu ya sake tabbatar da Oga kwata-kwata ba gaibu bane ba! Kamar yadda ake cewa (Astaghfirullah!!!) Wambai ya aiyyana hakan a cikin zuciyarsa hannuwansa suna karkawa! Ba su da ikon kub utar da ita dama chan to yanzu kuma ga evidence! He really can t believe wai yau shine zai nad e hannu ya zauna a gaban idanunsa a jefe Gimbiya y ar d an uwansa! Dan ya san ko da ace Gimbiya Mariya bata da evidence to ba su Isa su hana ba ballantana kuma ga evidence. A hankali ya mik awa Mai Babban D aki videon d