← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 59

Sashe 17

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fita Mama ta mayar da kallonta ga Ma a wanda yake nan kwance a kan tabarma har yanzun idanuwansa a lumshe. Fuskar tasa ta k urawa ido a take ta ji duk ta muzanta! Babu wanda zai kallesa sau d aya ba tare da ya fahimci wayene shi d in ba. Allah ya d aura mata matsanancin son d anta Ma aruf dan zata iya cewa babu wata uwa da take son d anta sama da ita a kaff fad in duniyar nan, shiyasa take jin tsoro a duk lokacin da irin wannan ciwon nasa ya tashi, kuma take gujewa duk wani abunda zai tada masa ciwon nasa, dan tana matuk ar jin tsoron abunda zai rabata da shi dan haka take kare duk wani abun da zai janyo b acin ransa, wanda hakan ya sanya take ganin kanta as selfish take kuma jin tsoron ranar da zata tsaya a gaban Ubangiji ta yi masa bayanin amanar da ya bata, ta san tana iyaka bakin k arinta kuma tana addu a ba dare ba rana amma tabbas wani abun har da kasawarta Addu a ta shiga yi masa sosai tana zaune a hakan .ta jima tana addu a tana mai neman taimakon Ubangiji kafin chaan ta sauk e wata nannuyar ajiyar zuciya Babu aure babu sana a babu girma, ko yaushe Allah zai shirya min Ma aruf d ina?? Ta yi maganar da ita a tunaninta a zuciyarta ta yi ba ta san a fili ta yita ba. A hankali ta ga ya bud e idanuwansa ya zuba mata su, wanda sai a lokacin ne ta fahimci ashe maganar tata ta fito fili. A hankali ya gyara ya mik e ya zauna kafin ya d an k uraa mata ido sai kuma kawai ya mik e ya ce Bara in je in yi sallolina Daga haka ya mik e da kyar dan har yanzu k irjinsa bai dawo dai-dai ba. Ya wuce zuwa d akinsa. Ta d an jima a zaune a wajen kafin chaan kuma ta mik e itama ta wuce bayi dan har an fara kiran sallar isha. Cikin tsananin tashin hankali Inna ta nufi k arshen tsakar gidan inda mutanen da suka kinkimo Ya Muhammad suka nufa da shi. Jikinta har karkarwa yake yi tana isa ta durk usa a gabansa ta shiga duddubashi a lokaci guda tana tambayar mai ya same shi? Wani Yaro ne ya ce tare suke shi da Dije yana tambayarta mai ya sa ta je wajen Ma a ta bari ya rik e mata hannu , sai kuma kawai ya yanke jiki ya fad Difff!! Haka kowa ya d auke wuta hatta Kaka wadda take ta sababin kar a wani d aga hankali ai hakan ba komai bane tunda dama an riga an san da zaman ciwon nasa na hauka Sheshshek ar kukan Dije ne ya ci gaba da tashi a tsakar gidan, cikin raunin da ba d arta ba ta matso tana zuwa ta durk usa a kusa da Inna tana cewa Inna mu kaishi asibiti, kar yau ma ya s Wani irin gigitaccen mari Inna ta sauk e mata wanda ya sanya ta yin shiru a lokaci guda kuma ta shiga shock! Ita da gaba d aya al ummar gidan na tsakar gidan da masu lab e dan waenda za su ce sun tab a ganin Inna ta sakawa Dije hannu k alilan ne a cikinsu, yawanci in zata hukuntata sai su kad ai da daddare take yi. Cike da tsana Kaka ta ce ai ba ki ga komai ba! Wallahi ba ki ji komai ba Halima wannan y ar taki sai ta saka ki kuka da ciwon zuciya, kuma yanzu ai kin makaro dan lokacin hukuntata ya riga ya wuce ko kin yi a banza dan shi reshe tun yana d anye ake tankwara shi idan ya riga ya bushe aka ce za a tankwara sa to karyewa zai yi. Tsakanin Dije da wannan Yaro kuwa za ki ce na gaya miki wallahi komai ya riga ya gama wakana sai dai kuma kar a kuma! Tana gama fad in haka ta juya ta shige d akinta zuciyarta fesss!! Idan akwai abunda take so a duniya to bai wuce ta ga Halima da y anta sun wulak anta sun tozarta ba. Magana Dije ta yunk ura za ta yiwa Inna Minu ya daka mata wata razananniyar tsawa wuce ki shige ciki!!! Da sauri ta mik e tana kuka sosai ta shige ciki Hankalinta a masifar tashe ranta a b ace. Tana wucewa Mallan ya ce a kai masa shi d Tun daga nan Mallan ya rufu a kan Ya Muhammad shi da wani Yaron sa aka kira Likitan bayan layinsu shima ya zo amma ba a samu Ya Muhammad ya farfad o ba sai k arfe sha biyu na dare shima kuma da ihu ya tashi abunda aka fi gudu kenan dan duk lokacin da ya suma ya farka da ihu to sai an yi sama da wata d aya ana abu d aya. Har wannan lokacin su Dije ba su rintsa ba haka wasu jama ar ma a cikin gidan dan d aya bayan d aya suka dinga shiga d akin Inna suna yi mata jaje tun suna d ari-d ari har suka ware suka shiga dannarta. Kaka ita ma ba ta rintsa ba dan jira take ya farfad o a gama da shi Dije ta zo ta bar mata gidan d anta dan ta ce wallahi tunda ta illatata to ta gama zama k ashin inuwa d aya da ita. Dalilin ma da ya sanya ta d an d aga k afa shine kukan da Mallan ya saka mata..dan suna tsaka da yiwa ya Muhammad add ua bayan Maghrib sai gata ta zo, ta tsaya ta ce ko Dije ta fita daga gidan ko ita ta tafi, shi kuma Mallan dama already hankalinsa a tashe yake ga shi shirun da ya ga Inna ta yiwa Kakar yau ya san definitely akwai matsala a gaba ga Ya Muhammad ya k i ko da motsi ne shiyasa kawai ya saka mata kuka wanda kukan da taga yana yi ne ya sa ta d an d aga masa k afa ta na jira ya gama ya zo ya same ta a yi ta ta k are. Asabe kuwa ta na gefenta in banda famfo ba abunda take yi mata ita kuma tana sake hawa zuciyarta na d a yin zafi tana ji idan ba ta kori Dije daga gidan ba to ba ta haifu ba kuma ba ta haifa ba Musamman ma da ta lissafa ta ga wannan d in dama ce ta same ta a b agas da zata yi amfani da ita ta zartar da k udirinta na shekara da shekaru, shiyasa ta zage dantse ta kuma saka a ranta tabbas ba zata yi sanya ba. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 08. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Ciki-ciki ya yi sallama ya d aga labulen d akin ya shiga. A zaune ya sameta ita kad ai kamar kullum tana karatun Alk urani. Bata kulashi ba shima bai katseta ba bayan ya nemi waje ya zauna kawai sai ya yi shiruuu alamun ya yi zurfi a tunani. Sai da ta kai aya tukunna ta yi doguwar addu a sannan ta juyo ta kama kanshi ta shiga yi masa addu Sai da ta ida tukunna suka shafa a tare, daga nan d akin ya yi shiruuu .bayaga d azu da suka gama shan azabar karara ta tayasu da addu a..tun ranar da ya shak e Mallan idi ta yi masa fad a bai sake zuwa ya zauna da ita haka ba, sai dai da safe ya shigo ya gaisheta da daddare ya lek o ya ajjiye mata abunda ya kawo ya yi mata sai da safe ya fita, shiyasa gaba d aya take a tsorace tana ta addu ar Allah ya sa bai saka abun a ranshi sosai ba gudun motsawar ciwonsa, shiyasa d azun da aka kawo mata shi zuciyarta ta kusan bugawa a tunaninta b acin ranne ya tado masa da ciwon sai daga baya tukunna ta gane ashe azaba ce, sannan sai da ta fahimci abun bai yi k arfi da tsanani sosai ba kamar last time tukunna hankalinta ya d an kwanta ..ta san cewa she is selfish tabbas! Amma Ma aruf shi kad ai take da shi a duk fad in duniyar nan shiyasa take tsoron duk wani abinda zai janyo abinda zai rabata da shi idan akwai abinda take tsananin tsoro shine ta ga ciwonsa ya motsa dan a yadda ya sha da kyar the last time ita kanta ba wai likitoci da suka bada tabbaci ba ta san any mistake to game over ne Barka da dare Maama Muryarsa ta katse mata tunaninta. Ajiyar zuciya ta sauk e a hankali ta ce barka, ya jikin naka? A hankali ya ce na warware Garin yaya karara ya shafeka ne wai? Ta yi masa tambayar tana kallonsa, d an k uraa mata idanu ya yi kafin chan ya sunkuyar da kansa kawai. Shiru ta yi ba ta sake yi masa maganar ba suka dasa zaman shiru a cikin d akin. Kafin chaan ta mik e ta je ta d auko wani ruwa a cikin gora ta k araso inda yake ta zauna ta bud e tukunna ta mik a masa ta ce gashi, d azu na lek a zan ba ka na tarar ka samu barci. Ungo karb i ka sha da bismillah. A hankali ya saka hannu ya karb a, ya yi bismillah ya shiga sha. Sai da ya shanye tukunna ya ce na gode Maama. Shafa kansa ta yi tana murmushi sannan a hankali ta ce Allah ya k ara maka lafiya da nutsuwa agowa ya yi ya kalleta yanzun ma cikin muryarsa mai cike da dakiya da izza ya ce Ameen Tukunna a hankali ya d an matso ya mik a hannunsa da yake a ta b angarenta ya rungumota ya ce fushin ne har yanzu? Dan ya lura da yanayinta. Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce tunani kawai nake yi ko sai yaushe Allah zai shirya mini kai! Ina yin addu a Ina sadaka amma
Chapter 17 · 0% Book details