← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 59

Sashe 20

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidan su mai yasa basu kalleta ba? Ko mata maza ne su? Sai shi k aramin d an iska ko? Kinsan a tafin hannuna kike dan haka wallahi ku kiyaye ni in ba haka ba zan yi muku abunda hankali bai zata ba muddin kuka sake shiga sabgarmu. Tana gama fad in haka ta wuce ciki ta je ta janyo hannun Dije wadda tun d azu ta k ame a kitchen d in take kuka. Suka fito suka wuce d aki aka bar ragowar mutanen gidan da k us-k us, wanda da yawa a kan maganar gidansu Asabe da Inna ta sakar musu latest suke yi. Mahaifin Asabe irin babban mutum ne a unguwar kowa ya sanshi sai dai mai kud in bahaushe ne dan shi kansa idan kika ganshi ba za ki ce ya tara ba ballantana y a da matansa, kusan kaso goma a cikin d ari na gidajen Unguwar duk nasa ne amma ko atamfar anko idan ta fito ba iya siyawa mata da y ansa yake yi ba dan abun nasa ya had e masa da matsananciyar rowa da mammak o da son tara kud i (ko wa yake taramawa? Oho masa!) Kusan kowa ya san gidansu wannan dalili ya sa idan aka ji b im! Na gidan ake d abbaka abun a zuzuta shi! Suna wucewa Minu ya shiga ya d auki flask d in abinci ya fice dan sai a lokacin hankalinsa ya samu damar jiyo masa vibration d in wayarsa da take cikin aljihun jean d in jikinsa wanda yake da tabbacin Mallan ne. Su Dije suna shiga d aki ta zube a k asa ta shiga bawa Inna hak uri, ko kallonta Innar ba ta yi ba ta wuce ta je kan gadonta ta zauna tana huci tana jijjjiga k afa dan bata gama hucewa ba. Sun jima a haka kafin Dije ta zame ta kwanta a wajen tana sauk e ajiyar zuciya ajejjere, ba ta dad e ba bacci ya yi awon gaba da ita. GIDAN SU DIJE. Asalin Mallan cikakken Bahaushen garin Kano ne, k auyen Getso. Kaka su biyu kacal Allah ya bata Mallan (Bashir) da d an uwansa Kawu Isa wanda shi har yanzu yake zaune a k auyen Getso yayinda Mallan dama shi tun lokacin da ya baro garin ya taho neman ilimi yake zaune a gidan Malaminsu, wanda zuwa yanzu Allah ya yi masa rasuwa. A nan ya had u da Inna (Halima) wadda babu kalar abunda Kaka bata yi ba dan kar a yi auren amma da yake rabo ya rantse sai da aka yi..Da taimakon Mahaifin Mallan wanda yake tsananin son had in ba dan komai ba sai dan fahimtar da ya yi Halima ita ce sanyin idaniyar d an nasa ita ce farincikinsa, dan haka ya tsaya tsayin daka har sai da ya ga auren tukunna hankalinsa ya kwanta, wanda ana yin auren da wata d aya ciff Allah ya karb i ransa, (shekaru talatin da d aya kenan yanzu). Anan Mallan ya sayi gida bayan an raba musu gado, wanda nan ma iko da kud irar Allah kad ai ta sanya aka sayi gidan nan dan babu yadda Inna ba ta yi ba amma ya sayar da gonar sa ya zo ya sayi gida babba mai d akuna da yawa a unguwa uku, dan Mallan ya so tara y a barkatai hakan shine burinsa, dukda kuwa ya saka a ransa in sha Allah Halima ita kad ai ce matar aurensa amma ya tsara zata haifa masa akai-akai in sha Allahu har sai haihuwar ta tsaya dan kanta. Bayan rasuwar Mahaifinsa Kaka k in ci gaba da zama a Getso ta yi ta tarkato ta dawo gidan Mallan da d amarar korar Inna daga gidan ta ko wacce hanya. Kwata-kwata Mallan bai san cewa Kaka ba ta son Halima ba dan ta k ashin k asa take yin komai. Sai da Inna ta samu cikin Ya Muhammad tukunna true colour d in Kaka ya fito fili ras! Dan kasa ci gaba da danne tsanar Halima ta yi, hankalinsa ya tashi kam a wannan lokacin dan k iri-k iri Kaka ta nuna ba ta son cikin k arshe ma ta ce ba na Mallan d in bane ba, sai da ta saka Inna ta rantse a gaban mai unguwa tukunna aka samu ta sarara mata. Tun daga nan kuwa hankalin Mallan bai kwanta ba, dan tunda Inna ta fahimci Kaka bata k aunarta itama ta botsare dama itama fitinanniyar ce ta bugawa a jarida shiyasa kwata-kwata sai aka gagara samun sauk i ta ko wanne b angare, kullum cikin rigima suke babu mai d agawa wani k afa. Sai da Kaka ta kwanta jinya a lokacin da aka ce mata Inna ta haifi d anta Namiji fari sol da shi kamarsu d aya sak! Kamar ta yi kaki ta tofar( lokacin shekara d aya da auran Inna da Mallan). Bayan ta warke ta je Getso ta dawo, ita dai Inna har gobe Kaka take zargi akan rashin lafiyar Ya Muhammad dan tunda ta dawo ta d aukesa ta shige d akinta da shi daga baya ta dawo mata da shi shikenan Yaron ya fara shisshhid ewa a take idanunsa suka k .sai da aka kai ruwa rana tukunna da kyar aka samu kansa a asibiti, ai kuwa tun daga nan ko kuka ya yi mai tsaho sai sun yi sama da sati a asibiti, sai da ya yi wayo tukunna aka fahimci ashe abun hauka ne, dan Idan ya motsa har duka yake yi kuma burinsa kawai ya kawar da duk wani da ke a kusa da shi, to idan ya lafa kuma sai ya zama kamar wani zombie kafin a hankali a hankali kuma ya warware. Da aka haifi Ya Aminu nan ma sai da Kaka ta kusan zaucewa wanda hakan ya yi matuk ar bawa Mallan mamaki da tsoro kuma ya sake tabbatarwa tabbas ba ta son Inna. Tun daga nan ta tayar da ballin sai Mallan ya k ara aure A ganinta tunda ta kasa ita kad ai idan aka yowa Innar kishiya kishiyar zata tayata su fitar da ita cikin sauk Asabe y ar k awar Kaka ce dan tunda Kaka ta dawo layin suke shiri a lokacin sune manyan layi, ita Kaka d anta yana da gida mai d akuna dayawa ita kuma mahaifiyar Asabe Mijinta yana da kud Daga baya baya dai Ita mahaifiyar Asabe ta d an ja jiki lokacin da duniya ta fara yiwa Mallan zafi, dan shi bai yi karatun boko ba, kuma tunda Malaminsa (uban gidan sa) ya rasu komai sai ya jaa baya. Sai dai kuma Kaka tana zuwa da zancen aure ta yi karaf ta amince dan a lokacin Asaben ta yi laifi Mahaifinta yana shirin aurawa wani Yaronsa ita kuma Yaron nasa a Sumaila yake matansa uku ita ce ta hud u, gashi dama ta san Asaben tana son Mallan, fad a ne kawai ba su yi ba a ganin uwar hakan zubar da girma ne. Sai da Inna ta yi da gaske tukunna ta iya rik e kanta da auren ya taho gadan-gadan. Shi Kansa Mallan d in ba so yake yi ba babu yadda ya iya ne, haka nan Kaka ta yi ruwa ta yi tsaki sai da ta ga Asabe a d akin Mallan tukunna hankalinta ya kwanta. Lokacin auren Mallan da Inna shekaru 15 kenan. Babu kalar gorin da Inna ba ta ji ba, har da cewa A bawa Asabe d akuna hud u dan ita d in tana da dangi da nasaba an san za a yi mata kayan d aki Sai gashi Asabe ta zo daga ita sai wani gado low class a lokacin, da wata yololuwar katifa, ai kuwa nan itama Inna ta samu na yi ta tisa su gaba da nata gorin dan ko ita da take ba uwa ba uba ba dangi kayan da ta siyawa kanta a lokacin aurenta ya fi na Asabe. Ganin wannan gorin bai ci ba sai Kaka ta fara maganar haihuwa dan a lokacin shekarar Inna goma sha biyar da auren Mallan amma y ayanta biyu tana da cikin Dije. Kullum Kaka bata da abin fad e sai a matsa ga mai cika gidan nan ta zo Sai gashi sai da aka yi shekaru hud u lokacin har Dije an Haifa ta yi wayo sosai tukunna Asabe ta samu cikin Zainab da kyar kuma tun daga kan Zainab haihuwar ta tsaya mata ita ma Inna haka wanda zuwa wannan lokacin duk sun fahimci Mallan d in ne bashi da rabon haihuwar da yawa. Duniya ta yi zafi, babu tayi yawa, wannan dalilin ya sanya Mallan ya fara raba d akunan gidansa a haya saboda su samu abin rik e kansu, su dinga rufawa kansu asiri, dan shi Mallan bai iya sana a ba sam bata karb esa ba, Ya Muhammad kuma bashi da Isashshiyar lafiya, Minu ne kawai da ya taso yake sana ar carpinter, sai ko kiwon kajin da ya fara, wanda kud in duk a registration da handouts ya yi ta tafiya, dan yanzu haka ya kammala buk inda ya karanci geography service yake shirin farawa. akuna goma sha uku ne a gidan, biyun farkon na Mallan ne da Kaka, sai na farko da yake cikin d akunan hannun dama kuma na mazan gidan ne, duk wani Namiji tun daga kan Ya Kamal har zuwa kan Umar duk a d akin suke. Na kusa da shi kuma d akin Maman Fati ne, Maman Fati tana da Miji Yunusa cirani yake zuwa Lagos yana da wata a chan, ya kan yi wata bakwai bai zo ba, kuma idan ya zo bai fi ya yi kwana biyu ba ya koma. Baban Fati irin masifaffun mazan nan ne shiyasa wani lokacin ita kanta Kaka take shakkarsa. Ita kuma Maman Fati munafurci da fuska biyun da ta kware a kai ne ya sanya take iya zama da shi, dan hatta matarsa ta chan chanjawa yake yi baya tab a iya yin shekara d aya da mace saboda halinsa na zuciya da saurin fushi da fad ansu biyu, Fatima (sa ar Dije da Umar sa an Zainab). Sai d akin su Dije, Dije shekarunta sha shidda, Ya Aminu ashirin da
Chapter 20 · 0% Book details