← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 59

Sashe 27

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

da ta zabura ta mik e a razane ba, jikinta yana wani irin karkarwa. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 12. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Yama gama fad in haka ya kashe wayar ya juyo yana huci zuciyarsa tana tafarfasa. A kan hannunta idanunsa suka sauk ta damk e zanin gadon da take kai da dukkan hannuwanta biyu kamar zata fasa shi ne. A hankali ya k arasa inda take ya tsaya a kanta ya k uraa mata ido, motsi ya ga idanun nata sunayi suna karkarwa da gaba d aya ilahirin jikin nata ma. Damn it!! Ya furta a hankali wanda hakan ya sanya ta fahimci yana tsaye a kanta ne kusa da ita! Ba ta san lokacin da ta zabura ta mik e a razane ba, jikinta yana wani irin karkarwa. Sai da ta mik e ta bud e idanuwanta tukunna ta fahimci ashe a asibiti ta ke, wawwaigawa ta yi ta ga d akin daga ita sai shi sannan kamar ma dare ne dan haka ta matsa sosai jikin bango wani mad aukakin tsoro mai tafe da takaici yana lullub uraa mata ido ya yi yana kallon yadda ta ke kuka yana jin sauk ar hawayen nata kamar zubar ruwan zafi a kan k irjinsa, a hankali ya matsa kusa da ita ya zauna a bakin gadon wanda hakan ya sanya ta sake mak alewa sosai a jikin bangon ta kawar da kanta gefe ta k ame sosai dan hatta sautin kukan nata ma ya tsaya dan sosai ta gimtse bakinta, sai uban hawaye da suke ambaliya wani na korar wani. A hankali ya ke kallonta cikin wani irin yanayi, sai da ya gama nazartarta ya gama hango tsorone tsantsa a tattare da ita, bayan ya tuna yadda Likitan ya ce masa shock ne ya sanyata ta suma , tukunna a hankali ya fesar da wani irin huci wanda ya sanyata ta sake k ame jikinta ta manne da jikin bangon kamar zata tsaga shi ta shige ciki sakamokon wani irin wari da numfashinsa ya feso mata da shi! Ba wai wari na k azanta ko warin baki ba! Wani irin wari ne wanda ba ta tab a jin kwatankwacin irinsa ba amma dai ta fahimci warin kayan shaye-shaye ne sakamokon yadda ta ji kanta ya yi wani irin mahaukacin sarawa a lokacin da ya fesa mata hucin numfashinnasa ita kuma ta shak A hankali cikin wata iriyar calm murya sannan a slow sosai ta ji ya ce Ba zan tab a cutar da ke ba Khadijah. Da sauri ta juyo ta ware kyawawan idanuwanta da suka rine ta zuba masa su wanda hakan da ta yi ya sake assasa mata tsana da matsanancin tsoronsa kallo d aya za ka yi masa ka fahimci shi d in rik en d an daba ne sannan yanzu da ta had a idanu ta shi ta sake fahimtar a buge yake mak ill!! Sai dai kuma wani ikon Allah a lokaci guda maganar ta sa ta soma yunk urin yin tasiri a kanta saboda yadda take hango zallar gaskiyar abinda ya fad in a cikin kwayar idanunsa wanda hakan ya bada gudummawa wajen sanyaya mata ilahirin jikinta Kamar kuma wadda aka mintsina a take ta yi firgigit! Ta d auke kanta lokaci guda ta dawo cikin haiyyacinta. Cikin takaici da tsoro ta fara k arin sauk a daga kan gadon gaba d aya, da sauri ya rik e mata hannu ya ce relax, ba ki da lafiya fa Ya yi maganar a dake. Wani irin kallo ta yiwa hannun nasa sannan ta d ago ta kallesa, wanda hakan ya sanya kawai ya d auke hannun nasa. Ina y an uwa na? Mai yasa na kasance a nan tare da kai? Ta yi masa cikin takaici tsoro da damuwa. A hankali ya runtse idanuwansa kafin ya bud esu, sai kuma ya mik e a hankali ya juya ya fita bayan ya sake ce mata ki nutsu ba ki da lafiya Bai dad e da fita ba lokacin Dije har ta gama shirin fecewa wata nurse ta shigo, juyin duniya amma Dije ta k i zama a asibitin nan ta ce ita Gida zata tafi. Dai-dai ta fito su Oscar suka taso dan su ya barwa jiranta amma kallon da ta yi musu ta k ara sauri ya sanya suka gagara tsaida ita dan sun san basu Isa tsawatar mata ko su rik eta ba .a baya dai Scorpion ya bita ya ga ta tsayar da abun hawa ta fad a masa inda zata je ta shiga, tukunna ya koma ciki ya na mai gwada layin Ma a wanda tunda ta fito ya fara k arin kiransa amma tun lokacin layinsa engaged. Da niyyar zuwa gidansu ya fita domin ya taho mata da ko da Minu ne dan ya lura a mugun tsorace take da shi wanda hakan ya sanyashi dana sanin abubuwa da yawa a karon farko na rayuwarsa. Yana fita kiran Maama ya shigo cikin wayarsa, dan haka ya amsa Ka zo yanzunnan ta ce da shi cikin sheshshek ar kuka! Sai da gabansa ya yanke ya fad i kafin ya ce wani abun ta kashe wayar. Gudu-gudu sauri-sauri ya k arasa bakin titi, dan already ya aiki Grenade da motar da suka taho da ita ta dpo. Napep d in da ya tarar akwai mutane a cikinta amma haka ya fincikosu ya watsar ya shige suma kuma basu yi yunk urin yin komai ba saboda yanayinsa da suka gani. Shi kansa mai Napep d in a tsorace yake da shi dan haka ya dage ya dinga tsula uban gudu kamar yadda Ma in ya umarcesa. Yana shiga cikin gidansu tun daga soro wajen d akinsa ya fara jiyo muryar wata mata tana cewa to ni dai bari in yi sauri in tafi kafin ya zo, dan ya saka mana dokar zuwa cikin gidannan kamar yadda na gaya miki yanzun. Kuma wallahi ya kula da kanshi dan wannan karon kam ba zamu yarda ba Kuka sosai Mama take yi yayinda matar take k arin saka slippers d inta dan haka duk basu lura da Ma a wanda ya shigo a zuciye zuciyarsa tana wani irin tafarfasa ba. Sai da matar ta gama saka slippers d inta ta d an yo gaba kawai ta ji ta k ume da k irjinsa gab! Kamar wani dutse ko motsi bai yi ba amma idanuwansa kad ai idan ka kalla sun isa su gigita ka. Inda-inda ta farayi ganin yadda ya kafeta da idanuwa sai kuma ta fashe da kuka kawai tsabar tsoro..ta durk usa a gabansa tana kuka wiwi tana cewa ka rufa min asiri inada jikata guda d aya ni kad ai gareta bamu da kowa idan ka kasheni za ta tagaiyyara Wata mahaukaciyar shak a ya yi mata ta mik e tsaye ganin yadda take sake ruru wutar tsanarsa a idanun Maama, yana d agota bai yi wata-wata ba ya d auke ta da wani Irin mahaukacin gigitaccen Mari dama tun d azu a k ule yake ga kuma Dije da ya fahimci ita tsoronsa ma take ji yanzu kuma ga Maama. Matar tana zubewa a wajen dai-dai Maama itama ta durk ushe ta fashe da wani irin gigitaccen kuka! Jikinsa ne ya hau karkarwa ya yi kan Maama zai rik eta ta mik e ta fara jaa da baya tana cewa Ashe har yanzu zalincin naka yana nan Ma aruf? Ashe har yanzu baka daina kashe mutane ba? Ashe har yanzu zuciyarka babu Allah? To wallahi tallahi bari ka ji in gaya maka da kaina nan zan mik a ka ga hukuma in yaso sai in ga uban da zai kwatoka! Ma aruf a gaban uwa ka kashe mata d anta! Ya kake tunanin zata ji? Ya kake tunanin zan ji idan wani ya kashe mini kai a gaban idanuna???? A hankali ya sake tunkararta hankalinsa a masifar tashe ta ce kar ka matso kusa da ni!! Cikin tsawa sannan ta ce babu ni babu kai daga yau! Ka ji abunda na fad a maka ko baka ji ba??? A da Ina tunanin har da sharrrin K uruciya da zafin abunda ya faru da kai ne sanadi hakan ya sanya na nad e hannu na yafe maka b arnar da ka yi a baya nake nema maka sassaucin azabar girman zunubinka a wajen Ubangiji amma yanzu kam baka da wani excuse Ma aruf!! Kuma bari ka ji in gaya maka ya zama dole ka amsa laifukanka kuma a hukunta ka ko da kuwa hakan yana nufin zan rasa ka ne! Idan ka kasance d an daba wannan zan iya yi maka addu a idan ka yi kisan kai a lokacin k uruciya wannan shima zan iya d aga maka k afa amma bazan zama selfish in nad e hannu in zauna Ina gani kana kashe rai da hannayenka ba! An yi an gama ta faru ta k are!!! Wani irin mahaukacin karkarwa jikinsa ya shiga yi yana jin wani kalar birkitaccen tashin hankali yana dad a bijiro masa. A hankali ya matso kusa da ita wannan karon kam ihu ta yi jikinta ya na karkarwa idanunta jazir! Ta ce na ce maka bana so ka tab a ni ko? Ba na son ganinka!!! A hankali ya runtse idanunsa ya d auke numfashinsa na wasu y an sakanni sannan ya saki yana jin tashin hankalin da bai tab a jin kwatankwacinsa ba. Juyawa ya yi da niyyar cin uwar matar nan ko ya samu ya huce ya hangota dai-dai tana fita daga gidan Sannan na baka mintuna ashirin ka dawo da Yarinyar da ka yi Garkuwa da ita gidan iyayenta Cike da rashin fahimta ya juyo yana kallonta dai-dai nan kiran Scorpion wanda yake ta yi masa babu k autawa ya sake shigowa cikin wayarsa dan haka ya amsa yana shirin yin magana a fusace ya ji Scorpion d in ya ce masa suna waje, yana son ganinsa. A k ule ya ce ka tabbata ka tare min matar da ta fito daga cikin gidanmu yanzunnan. Yana gama fad in haka ya kashe wayar ya d ago zai yiwa Maama magana ya ji ta d aukesa da wani irin gigitaccen Mari. Cikin mad aukakin b acin rai
Chapter 27 · 0% Book details