← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 59

Sashe 32

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka yi ya tafi a banza, wai ai shima an k ona masa gida kuma an kashe masa Aboki sannan yanzu haka Mahaifiyarsa tana kwance. Kamar ma laifin akan samarin layin ake so a d aura wai ai sune suka fara tayar da husuma Sannan aka ce wai su Ma ah ba su kashe kowa ba wasu y an daba ne da ba a san daga ina suka zo ba (Yaran Scorpion) suka cinnawa gidajen wuta suka yi b arna Daga k arshe dai Mallan ne kawai ya iya tsayawa ya ji k arshen zancen ta inda aka yi musu gargard babu su babu shi kowa ya yi harkar sa dan ragowar mutanen duk fushi suka yi suka fita, saboda a ganinsu hakan straight up rainin wayo ne kawai! Duba da yadda ko d an Yaro mai tafiyar tatata idan ka tambaya a layin ya san waye Ma ah to su kuma y an sanda sun ce su kawo shedar wanda ya tab a kashewa za a d auki mataki sun kasa, dan wannan Yaron ma da ya yiwa juyin 360 da wuk a a ciki an ci sa a da Ikon Allah har yanzu yana icu kuma an ce ba shi bane ba Oscar ne ya yi aikin, wannan dalilin ya sanya kawai mutanen suka yi fushi suka fice daga ofishin y an sandan ransu a masifar b Kamar yadda aka yi musu haka shima Ma ah aka zaunar da shi aka yi masa tsakani da y an layin daga nan magana ta mutu da ikon Allah kamar ba a yi komai ba. Jikin Mama babu kyau sam! Dan ta kwanta mummunar jinya kwarai, yanzu haka shirye-shiryen fitar da ita waje ake yi dan jinyar ba zata yiu a nan ba, wanda iyayen gidan Ma in ne suka d auki nauyi.. He looks calm idan ka kallesa a ido amma fa shi kad ai ya san me yake going through deep down, da mugun kyar yake iya rik e kansa wanda yake jin kamar ba zai iya ci gaba da k arin holding kansa together ba dan tabbas jarumtarsa ta kusa k arewa gashi idan ya tuna shine musabbabin halin da take a ciki yanzun sai ya ji kamar ya binne kansa. Tun ranar da Mallan ya dawo daga asibiti ya fahimci Inna ta d au zafi, dan bai had u da ita ba sai ranar da ya sanar da d aurin auren Dije tun daga nan kuwa bai sake sakata (Inna) a idanunsa ba, dan ko jiya da ya shiga d akinta ma b uya ta yi a cikin bargo gaba d aya ta k i yarda su had u, ya san dai ya ci galaba a kanta tunda ya had ata da mai unguwa ya kirata a waya ya hanata tafiya amma fa fushin da take yi da shi sosai yake tab a shi Dukda cewa y an layin sun san baya nan hakan bai sa kowa ya hau masa sahun sallarsu ba a cikin mutane uku dattawa da suka riga su zuwa masallacin, kamar had in baki. Ana cikin gabatar da sallar Magrib an kusa tafiya ruku un farko kenan kawai suka shigo shi da Scorpion da Oscar da wasu guda biyu daban waenda yanayinsu har ya ci uwar na su Oscarn. Daidaita sahu suka yi suka kabbara sallah cikin nutsuwa kamar ba su ba. Kafin a idar kuwa masallacin ya cika mak il, kowa idan ya shigo ya gansu sai ya shiga shock tukunna kafin ya yi sauri ya tayar da ik ama. Ana idarwa aka fara kallon-kallo, da k us-k .waensu su ce a rufar musu wasu su ce a barsu kawai da Allah dan ko dawowa daga jimamin b arnar da suka yi ba ayi ba gashi y an sanda da kansu sun yi musu tsakani. Farar shadda ce k all a jikinsa yau abunda mutane da yawa za su ce basu tab a ganinsa da shi ba wato manyan kaya, kamar ba shi ba ta baya idan bai juyo ba sai dai yana juyowa zaka fahimci waye shi d in gashi yau idanunsa sun yi wani irin dafewa alamun ransa a b ace yake kuma yana cikin damuwa sannan ya tamke fuska kamar wanda aka aikowa da sak on mutuwa. Har addu a sai da suka yi tukunna ragowar biyun da suka zo da su suka mik e suka fita Ma ah shi kuma shi da Scorpion da Oscar suka k arasa wajen da Mallan yake. Diriricewa Mallan ya yi da farko, yayinda Kawu Isa ya tsaya kallon ikon Allah dan shi mamaki ma suka bashi! Saboda fatar jikinsu kad ai abun kallo da al ajabi ce sakamokon yaddda take kacha-kacha abun kyankyami! Ko ba a fad a masa ba ya san waennnan sune su Ma in da suka tashi kusan rabin Unguwa Uku kwanaki uku da suka wuce. BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 15. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Sai da ya yi iyaka bakin k arinsa ya nutsu sosai tukunna ya ce Barka da dare Baba Wani yawu muk ut!! Mallan ya had iye yana jin fad uwar gaba matuk a dan bai san me ke tafe da su ba. Da kyar ya tattaro kalaman ya samu harshensa ya furta Barkanmu dai Ma aruf, ya jikin Mahaifiyarka? A hankali ya lumshe idanuwansa ya bud e, k irjinsa yana yi masa wani irin zafi, da kyar ya iya cewa Alhamdulillah Shiruu Mallan ya yi yana jira ya ji ko shi za su yi masa gaisuwa amma sai ya ji shiru. Yana cikin wannan tunanin ya ji Ma a ya fara magana cike da kwarin guiwa sannan babu wani kwana-kwana Na san ka riga ka sanni ka san iyayena, na san a musulunce idan mutum ya ga Yarinya yana so to iyayenta ya kamata ya fara zuwa ya nemi izini a wajensu kafin ita, hakan ita ce kamala. To ni ba ma izinin fara zance da ita ko wani abu makamancin hakan na zo nema kad ai ba! Na zo ne in gabatar maka da kaina a matsayin wanda yake neman auren y arka Khadijah kuma Mijinta har a aljannah in sha Allah. Har ga Allah tsabar yadda Mallan ya shiga mad aukakin tashin hankali da rud ani wallahi shi manta ma wacece Khadijar ya yi! Sai da ya dedeta kanshi da taimakon addu i tukunna da mugun kyar ya samu ya iya had a 1+1. Wani Irin gumi ne ya shiga tsattsafo masa ta koina, da ya bud e Baki zai fara magana sai bakin ya hau karkarwa ya ji ya gagara furta komai! agowa ya yi ya d an kallesu ya ga Ma ah ya kafesa da rikitattun rinannun idanunsa babu alamar annuri rahama ko sassauchi a kan fuskarsa. Da sauri ya kawar da kansa gefe yana mai jin yadda zuciyarsa take wani irin hantsilawa kamar za ta fashe ne. Cikin magagin buguwa Oscar wanda suma duk sun zuba masa idanune ya ce Baba ya na ga ka shiga trembling ne? Mu fa nan da ka ganmu ko a yanzu a shirye muke da sadakin mu a hannu, idan kuma kana buk atar preparation to sai a saka sati d aya ko biyu, saboda Mai gida za su tafi k asar turawa ne jinyar Mama kuma da ita yake so ya tafi Cikin bayarda umarni Scorpion ya ce ka yanke komai mu gama magana yanzu, kawai dai ka tabbatar ka yi abunda mukeso, dan ko baka yi ba ranka ne zai b aci amma dole za a d aura da izinin Allah, saboda Oga shine Mijinta har a gidan Aljannah A tare duk suka ce in shaa Allah Ikon Allah, Allah shine mai aljannar amma Astaghfirullah yanzu suma waennan ashe suna saka ran shiga aljannah?? Kawu Isah ya yiwa kansa tambayar a cikin zuciyarsa ba tare da ya san mai bashi amsa ba. Sunkuyar da kai Mallan ya sake yi a karo na babu adadi! Bai riga da ya d aura auren Dije da Ma aruf ba kuma ya san kansa a gabas ba zai tab aurawa ba amma the fact that wai Ma aruf d an daba wanda yake yiwa kallon the most useless human being a duniya a idanunsa! Wai yau shine ya zo yana neman auren y arsa hakan ya sanya wasu hawayen bak in ciki da tashin hankali suka zubo masa shi musulmi ne kuma mutum ne mai addini ya san cewa kyamatar d an uwa musulmi bai dace ba amma tabbas a yadda yake jin kyamar Ma aruf wallah idan aka ce yau ya auri Khadija to sai ya had iyi zuciya ya mutu har lahira!. agowa ya yi suka had a ido da Ma ah wanda har yanzun shi yake kallo ba ya ko k yafta idanu. Ganin yana ta faman dibi-dibi akan abunda ko hauka suke yi ba za su tab ullawa ba ya sanya Kawu Isa ya kalli Ma ah ya ce Mallan Ma aruf ko? Bai jira ya bashi amsa ba ya ce asalin gaskiya shine gobe iwar haka ma Dije tana a matsayin matar wani idan Allah ya yar. To ai da sauk i! Tunda gobe ka ce ba yanzu ko jiya ba, kawai yanzu abunda zai faru shi ne..a d aura musu auren ma yanzu tunda ga abunda na ji kun fara cewa saboda gudun samun matsala, dan a zauna lafiya. Scorpion ya zaiyyane musu hakan cikin katse shi fuskarsa tana mai chanjawa zuwa wani yanayi na daban. Ina ga kamar baka fahimce ni ba .mun riga mun bayar da ita ga d ana d an uwanta, kuma na san ka san cewa neman aure cikin aure haramun ne ko? Cikin tarar numfashinsa Oscar ya ce mun fahimci abunda kake nufi mana kwarai! Abunda muma muke so ku fahimta shine ku chanja tsari a bawa wanchan hak uri a mayar masa da kud insa dan mu bamu san mu ce muna son abu a ce mana A a ba! Kune iyayenta kune magabatanta dan haka chanja hakan a wajenku na tabbata abu ne mai sauk Shi dai Mallan bai ce komai ba Ma ah kawai ya tsurawa ido wanda ya kawar da kansa gefe guda! Ya lura hatta naman kumatunsa wani irin karkarwa yake yi
Chapter 32 · 0% Book details