Sashe 10
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
**************** ..SOMEWHERE IN AFRICA Dukda kasancewar garin a waye yake hakan bai sanya d igon haske ya ratso ta cikin d akin ba! Ga wanda bai san inda kansa yake ba tsaff zai iya cewa duhun daren wata mai kwana d aya ko biyu ne, amma a zahirin gaskiya k arfe goma da rabi ne na safe. Wata dakakkiyar murya aka yi amfani da ita wajen cewa ki tabbata idan aka samu matsala wannan karon ranki ne fansa tare da na y i guda uku! Wani yawu mai tauri d aci da zafi ta had iye sannan ta ce na yi dukkannin abinda ya dace, bani da tantama wannan karon bai isa ya tsallake ba Ki tabbata idan aka samu matsala wannan karon ranki ne fansa tare da na y i guda uku! Aka sake maimaita mata maganar ta farko. Ta san idan ta bari aka maimaita har sau uku hukuncin ta mai tsanani ne dan haka ba dan ranta ya so ba ta ce Na amince! Muryarta na rawa. Marik in k ofar wadda ta kasance ta jar k asa mai shegen nauyi aka kama aka jaaa k ofar ta bud u wanda hakan ya bawa haske damar wanzuwa a cikin d akin tarr! Har sai da ta yi saurin runtse idanuwanta sakamokon sabawar da ta fara yi da duhun d akin. Ficewa aka yi aka barta ita d aya kwal aka mayar da k ofar aka rufe duhun nan ya sake mamaye koina..wani Irin kuka ta fashe da shi jikinta yana karkarwa tashin hankali yana sake lullub e ta, ta san cewa ta yi dukkanin abubuwan da aka sanya ta amma Mai Martaba Sarki ZainulAbidden ba k aramin d an baiwa bane ba shiyasa ta ke cikin matsanancin tashin hankali! Ba zata iya k irga adadin tarkunan da ya shallake ba kama daga haihuwar sa zuwa yanzu ba! Ta yadda aka yi aka haifesa d a Namiji ma kuma ya rayu a cikin masarautar kanshi abin mamaki tsoro da al ajabi ne! Kamar wata zararriya haka ta fara magana tana hawaye ga gumi kamar ana dafata sakamokon rashin b ulin da iska ko d aya zata shigo cikin d akin. Kaicona! Ina zaune a matsayina cikin kwanciyar hankali tare da uwargijiyata gashi kwad ayin k arin matsayi tare da son abun duniya sun janyo min bala Numfashinta ne ta ji ya fara sark ewa sakamokon rashin iska dan ta jima a d akin ta galabaitu, a hankali ta ce Ya Allah ko da ace wa adi na ya zo k arshe ka kub utar min da y Dukda kuwa ta san rayuwarsu a cikin masarautar ba tare da ita ba bala i ne gasu duk k ananu amma gara dai su rayu d in akan su mutu tare da ita A hankali ta fara lullumshe ido daga nan ta silale daga zaunen da take ta sume a wajen Bayan kamar awa d aya, ta ji an shek a mata ruwa! Haske ta gani tarr! An bud ofar Fadawa wajen su biyar suna tsaye a kanta. Kukan babbar y arta ta ji mai kimanin shekaru goma a duniya. Da k arfi kuma da sauri ta runtse idanuwanta bata kai ga bud ewa ba aka ce mata Mai Martaba Sarki ZainulAbidden yana a cikin k oshin lafiya bayan karin kumallo da ya yi da shayi da dambun naman da kika yi masa Bulala arba in ta hau kanki tare da y anki bayan nan kuma Rayukan ku ne fansa!! e Baki ta yi zata fara magiya aka yi saurin toshe mata bakin ta bayanta da wani kyalle haka suma y an nata Ko wannensu sai da Fadawan nan suka yi masa bulala arba in d innan kamar yadda suka furta da wata mahaukaciyar bulala wanda tun a bugu na uku da aka yiwa y ar autarta mai Shekaru hud u da ita Yarinyar ba ta sake shurawa ba! Jina jina haka nan suka yi musu tukunna suka fita suka barsu da Baki a toshe gashi babu ko d igon iska a cikin d akin da ya kasance na jar k asa wanda ta waje aka yi masa kamar plasta da langa langa. Dukda bata gani sosai suna fita ta rarrafa kansu inda take jin nishi sama sama Da kyar hannunta yake iya lalubo mata su, ko da ta duba ta k arshen ta rasu haka shima na biyun babbar y arta ce kawai ta yi saura, dan haka ta jawo ta ta rungume suna wani irin kuka mai cin rai. Bayan kamar awa d aya lokacin da rana ta kwalle numfashi ya yi bankwana da jikin babbbar y ar tata, lokacin itama ba ta cikin haiyyacinta ta yi sumar wucin gadi, sai da ta farfad o sannan ta fahimci rumgume take da gawa Rashin ventilation ga uban warin gawarwakin da wasu suke ta tsutsa da bak in ciki da azabar radad in ciwukan da suka jijji mata yayin dukansu da bulalar doki! Ne suka taru suka sanya itama ta ji zuciyarta ta yi wani irin hantsilawa sai kuma ta bada dummm!!! Daga nan ta ce ga garinku nan. **************** Mallan bai samu ya koma gida ba sai wajajen k arfen goma na safiyar ranar sakamokon suntumewar da k afar wannan bawan Allah wanda Ma a ya yiwa b alli b alli a masallaci ta yi, dan sai da ta kaisu ga danganta shi da asibiti yanzu haka ma yana chan an dai yi dressing an nad afar ana kan bincike. Yana shigowa tsakar gidan ya hango gawar Akuyar Asabe yashe a tsakar gidan baki a nannad Dukda ya san ba lalle Dije ta aikata wannan d anyen aiki ba amma sai ya tsinci kanshi da fara adduar Allah ya sa babu hannunta a ciki, a zuciyarsa. akin Kaka ya nufa da niyyar gaida ita kamar yadda ya saba kullum sai dai kuma ko da ya Isa bakin k ofar ya kwankwasa sai ya ji shiru, bai wani jima a tsaye ba Inna ta fito tana gyara d aurin d ankwalinta, suna had a ido da shi ta d an saki fuska ta ce Ashe kai ne Sai kuma ta d an rissina ta gaida shi dukda wadda suka yi a waya ba da jimawa ba. Cikin kulawa ya amsa mata ta tambayesa mai jiki ya ce mata da sauk daga nan ya fara rarraba ido ya na k arewa tsakar gidan kallo Sai a yanzu ya lura da yadda gidan ya ke shiruu kamar ma babu kowa, dan in banda Umar da ya gani a kan yashi suna wasa da Yara to bai ga kowa ba kuma bai ji motsin kowa ba bayan Halima da suke gaisawa da ita yanzun, sai ko Rakiya da ya hanga a kitchen tana shan ruwa. Gyaran murya ya yi bayan ya gama waennan lissafe lissafen ya ce ina ta kiran wayar Kaka tun d azu bata d auka, tana ciki kuwa? Allah dai ya sa lafiya Ya jero mata tambayoyin idanunsa a cikin nata. Numfashi ta fesar ta sauk e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ta ce Ka yi hak uri Mallan, Kaka Dije ta biyo d azu wai za ta daketa ita kuma ta zille shine ta k ume da bango ta suma, Aminu kuma yanzu ya fita yake ce min har da gocewar k ashi a hannu Lumshe idanuwansa ya yi ya fara k arin controlling temper d insa, sai da ya samu ya d an daidaita kansa da kyar! Tukunna ya ware murya ya shiga kwala kiran Dije! Dije!! Cikin kwantar da murya Inna ta ce tun d azu na aiketa siyo y ar tsala ka ga har yanzu ba ta dawo ba babu ita ba abun karin, sai Aminu na bawa ya je ya siyo mana k osai ga naka a d aki naga Asabe bata nan Shiruu ya d an yi kafin ya juya a fusace da niyyar fita suka yi kicib is da Dije ta kawo kai, bud u da ita kamar wadda ta yi burgima a cikin yashi.. Da mamaki suke kallonta fuskarnan ta yi jaa idanunta sun firfito waje alamun ta ci kuka. Baba ya tab u kwarai da yanayin nata amma hakan bai hanasa d aga hannu ya d auketa da wani irin gigitaccen Mari ba! Cikin karsashi ya ce duk haukarki ta tsaya iya kan mutanen gida amma ko da wasa kar in sake jin fad a tsakaninki da Kaka! Kamar zai wuce ta ya fita sai kuma ya ce mai ya sameki kika yi kacha kacha haka? Ko kema kan yashin kika hau? Sai a lokacin hawayen bak in ciki da takaici suka b alle mata tana yi tana jaan ajiyar zuciya a jejjere Sai da Inna ta daka mata tsawa ba tambayar ki ake yi ba!!! Tukunna ta magantu ta ce a ne ya d aure mini k afafuwa da hannnu a lungun mal.mai kanti wai sai dai in taho gida a haka kamar tsutsar caterpillar, kuma suka dinga yi min dariya Rasss!!! Gaban Inna ya yanke ya fad i, a ranta ta shiga had a kalmomin tana yi musu fashin bak i a cikin kanta a kuma ya d aure ta a lungu!! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ta shiga nanatawa a cikin ranta sai kuma ta jaaa hannunta suka shige d aki ta ma manta da Mallan a wajen wanda shima ya yi mutuwar tsaye daga jin zancen tun kwanakin baya ya cewa Kaka yana so su tashi daga Unguwar amma tunda ta ji saboda Dije ne yake so a tashi d in nan ta yi tsalle ta dire ta ce ba za su tashi ba, ko dai ta kama kanta ko kuma ta zubar ita ta sani amma ba za a wani tashi saboda ita ba kuma in aka sake yi mata maganar sai ta tsinewa mutum. Suna shiga cikin d akin Inna ta hau duddubata sai kuma ta yi cupping fuskarta a cikin tafukan hannayenta ta ce ki gaya min gaskiya mai ya faru?? Cikin sheshshek ar kuka dan sosai abun ya b ata mata rai, wai kamar ita Babba da ita za aure kuma ta gagara guduwa ta ce azu ne da na dawo daga siyian y ar tsala wai dan in yi sauri sai na biyo ta