Sashe 14
Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read
aya washegarin ranar da sassafe ta tafi da abincin kari amma sai da Mallan ya rabata da su da kyar ya maidota gida Kaka har da kukanta wai Halima ta rainata kuma ta mallake mata d Bayan ita ce ta fara zaginta tana shiga ko zama bata bari ta yi ba ta hau zaginta ta uwa ta uba sannan ta dinga yiwa Dije baki da fatan karuwanci, ita kuma Inna ta ce In sha Allah Dije alkhairi kawai za ta gani sannan idan ta sake zaginta wallahi sai ta rama tunda ba ta san ta girma ba ..Asabe ta sa baki Inna ta buge bakin shiyasa da Mallan ya ga dambe yana shirin kwacewa ya yi sauri ya fitar da Haliman ya maidata gida, kuma shima ya yi mata tatas ya ce ko da wasa idan ta sake mayarwa da Kaka magana wallahi sai ranta ya b aci ko me kuwa Kakar ta yi mata. Shiyasa tun daga ranar Inna ba ta sake komawa ba kuma ta d auki fushi da Mallan d in a ganinta ya yi son kai sun had e mata kai. Yau tun safe Dije take cikin farin cikin da Inna ta kasa fahimtar na menene, suna kitchen su biyu suna jefa d anwake tare suna d an tab a hira Sumayya ta yi sallama wanda sai da sallamar tata ta sanya Dije ta kusa kifar da tukunyar d an waken garin mik ewar da ta yi ta a zabure cike da gand oki. Tsayawa kawai Inna ta yi ta zuba mata ido wanda hakan ya sa ta d an sha jinin jikinta. Ta d an jima tana kallonta kafin ta d auke ido kawai ba tare da ta ce mata komai ba. Ta gane me Innar take nufi shiyasa ta gyara jikinta ta sake nutsuwa tukuna ta nufi hanyar fita dan har Sumayyan ta k araso tana k arin sako kai. Gaisawa suka yi da Inna tukunna Dije ta sa hannu ta jata tana mai cewa Inna bara mu je d aki. Jinjina kai kawai Inna ta yi ta ci gaba da jifan d anwaken ta. Sai da ta fito tukunna ta d auki ruwa a buta ta d an wanke hannunta tukunna suka wuce ciki. Suna shiga Dije ta ce Bani da sauri in b oye tukunna sai mu gaisa Ta yi maganar jikinta har wani rawa yake yi. Dariya Sumayya ta yi ta ce ai ban samu ba Bar batun wasa mana. Dije ta ce cikin zak uwa. Dariya Sumayya ta yi ta fito da wani k ulli a hannunta ta ce ungo, ki bi a hankali dai kar k ayi ya koma kan mashek iya, kin dai rik e yadda za ki yi ko? Dije ta ce tana k arin bud ewa. Da sauri Sumayya ta rik e hannunta cikin zaro ido ta ce rufa mana asiri, so kike ki saka mu rawar disko yau kenan, sai fa kin je kusa da shi tukunna, ko har kin manta yadda ake amfani da ita?. Dije ta ce tana mai juyawa ta nemi wajen b oyo ta b oye tukunna ta kalleta ta ce na gode, ya kike ya hanya? Dariya Sumayya ta yi sannan ta ce Sai yanzu kika ganni kenan, lafiya lau nake gida shima lafiya, bari in je in huta, yanzunnan fa muka dawo ko zama ban yi ba na taho kawo miki. Dan Allah Dije kar sunana ya fito. Cike da assurance ta ce mata Baki fa da matsala kar ki damu ai ba zan bari ma ya ganni ba. To Allah ya sa Sumayya ta ce. Sallama ta yi mata daga nan suka fito tare ta yi mata rakiya har bakin soron gidan, Sumayyan tana ta nanata mata cewa dan Allah kar ta bari sunanta ya fito har sai da Dije ta danna mata ashar tukunna ta yi shiru. Juyawa ta yi ta koma cikin gidan nasu ta wuce kitchen a zuciyarta tana ta adduar Allah ya kawo abinda zai sa a aiketa. Aike bai taso ba sai wajajen k arfe hud u na yamma Inna ta aiketa ta je ta karb o mata kud in adashen ta a wajen Rabi dillaliya wadda ta kira wayar Innar ta sanar mata kud i sun had BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 06. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Tun kafin Inna ta dire aya Dije ta mik e zunbur! Tana mai cewa Innar Cikin d an fushi Inna ta ce wai meye ne yake damunki tun safe sai kace mai tsutsu a d uwawu? Sunkuyar da kanta ta yi tana d an sosa k eya tana murmushin yak Inna ta jima tana k are mata kallo kafin chaan ta magantu ta ce Ki wuce ki tafi ki yi sauri sannan kar ki bi ta inda ya ke! Dumm!! Gaban Dije ya yanke ya fad i dan ta fahimci wa Innar ta ke nufi gashi ita kuma shine ma babban dalilin da ya sanya take ta addu ar Allah ya sa a aiketan. Tana shirin nufar wajen kayanta Inna ta ce ta saka uniform d inta kawai ta yi alwalla ta d auki jakarta daga nan kawai ta wuce islamiyya dan ta san idan ta ce sai ta je ta dawo tukunna za ta shirya to za ta makara ne. Jinjina kai ta yi ta ce Daga nan ta hau shiri .Allah ya bata sa a ta faki idon Inna ta d auko k ullin ta jefa a cikin jakar makarantar islamiyyarta ta ajjiye ta je ta yi alwalla ta dawo tukunna ta d auki jakar tana mai cewa Inna na tafi Allah ya kiyaye ki lura sosai saura kuma ki bari a sace min kud i a makarantar Ita dai da kawai take ta bin Innaa har ta fice daga gidan zuciyarta fess. Dayake ta san inda ta nufa ko hanyar gidan su Sumayya ba ta kalla ba ta wuce inda ta saka gaba. Dukda ta kasance mace mai kazar-kazar amma sam idan tana tafiya ba ta iya sauri ba shiyasa ta ji gaba d aya ta k agu ta matsu ta k arasa filin ball d in da ta tasarma. Addu arta d aya Allah dai ya sa suna wajen dan ta san lokuta da dama su kan je wajen tun kafin bayan la asar d Tafiyar kusan mintuna bakwai ce ta kaita tafkeken filin ball d ..tun da ta tunkaro wajen ta hango Oscar shi da Scorpion suna zagaye wajen yayinda Ma a ya ke tsaye ya yi irin tsayuwarsa ta sojoji kamar kullum da whistle a bakinsa yana kallonsu. Sai yanzu da ta iso wajen tukunna lissafinta ya bata ta yaya za ta je ta hura masa kuma har ta juya ta gudu ba tare da an ganta ba? Dan sholl wajen yake babu kowa sai su uku kacal gashi wajen babba. uruciya da k udirin d aukar fansar d aureta da kukan da ya saka ta ne suka tunzurata tare da bata amannar ta tunkare sa kawai komai ta fanjama fanjam! Luckily, su Oscar gaba suke kallo suna ta gudu basu kai ga kaiwa angle d in da za su iya ganinta ba shi kuma dama ya juya baya su yake kallo. Cikin sassarfa at the same time tana mai d auko k ullin dake a cikin jakarta, a haka ta k arasa inda yake dai dai ta gama zarowa ta ware da sauri ta d an durk usa ta hura masa a sangalalin k afafuwansa da yake kayan ball ne a jikinsa sai kuma ta mike ta hura masa a bayansa da wuyansa daga nan ta juya da niyyar d iba da gudu ta bar wajen ta ji gamm!! An ruk o hannunta da mugun k arfi!. Yadda k irjinta ya buga ita kanta ta yi tunanin zuciyarta ta tsage ne. Da mugun sauri ta juyo dan a yadda yake bai ci a ce har ya juyo ya rik eta hakan ba. Da mamaki take kallon sa tana kallon su Oscar waenda sam ba ta ma san lokacin da suka k araso wajen ba. Suma su duka ukun ita suke kallo dan haka aka tsaya ana y ar kallon kallo. Tunda Dije take ba ta tab a jin bakinta ya mutu murus ta rasa abin fad a ba sai yau, wani irin kallo ta ga Ma a yana yi mata wanda yake sanyata jin wani irin matsanancin tsoro dan bai saba yi mata irinsa ba. Yunk urawa Oscar ya yi zai yi magana da sauri ya d aga masa yatsunsa biyu na tsakiya sai kuma ya yi masa alamar su tafi. A take babu musu suka juya suka ci gaba da abinda suka baro ba tare da sun sake ko da kallonsu ne ba. Tsoro da firgici had e da dana sani ne suka lullub e Dije a take ta sake sunkuyar da kanta k asa ta ci gaba da k arin kwace hannunta wanda ita kanta ta san it s impossible dan wani irin rik o ya yi mata kamar zai karyata. Kusan minti d aya tana abu d aya gashi a tsaye kamar wani dutse ko motsi bai fara ba ballantana rawar diskon da take tunanin zai yi, balle har ta samu ta gudu. A hankali cikin raunin da ba d arta ba ta d ago kyawawan fararen idanuwanta da suka d an fara kad awa zuwa jaaa ta zuba masa da kyar ta aro jarumta ta furta mallan ka cika mini hannu Kallonta yake yi bai kuma cikatan ba kamar yadda ta so, a hankali ta ga jajajajaa yana maye gurbin farin cikin idanuwansa, sai kuma gumi ya fara tsattsafo masa a take. Sai da ya lumshe idanuwansa tukunna ya bud e sannan ya juya ya kalli ledar da ta mak ale a k afar bencin da ke a gefensa iska tana kad ata tana shirin barin wajen, d an k urawa ledar ido ya yi wanda hakan ya sanya ita ma Dije ta kalli wajen, a take kuwa gabanta ya yanke ya fad i dan ta yi tunanin da ta gama hura masa ta yar tuntuni iska ta kwasa ta yi gaba da ita. Dakewa ta yi ta sake aro jarumta ta ce masa mallan na ce ka cika