← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 59

Sashe 19

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

zai gano oho!. Ya Aminu ya fito kenan daga d akin Inna zai zubawa kajin sa abinci ya ga mutum yana zillo shi kad ai a kan kujera, da ke Dije tana daga chan ciki shi kuma yana a bakin k ofar shiyasa bai ganta ba ya gansa shi kad Da mamaki ya k arasa bakin kitchen d in idanunsa a kan Sagir wanda bai ma san ya k araso ba. Dai dai Dije ta d an tsugunna a kan k afafuwanta tana k arin rufe flask d in da ya k i rufuwa wanda tsugunnawar da ta yi ya taimaka wajen sake fito da hips d inta ta gefe da gefe. Wani irin murmushin iskanci ya ga Sagir d in ya yi har da wani fito da harshe ya na sid e Baki. Da sauri ya juya ya kalli Dije wadda ita ba ma ta san yana yi ba Allah Allah kawai take ta gama ta fita ta bar amsa kitchen d Wani irin takaici da bak in ciki ne suka lullub e Minu a lokaci guda, bai san lokacin da ya juya ya zaro tsinken tsintsiyar kwakwar da aka jingine a wajen ya tsole masa ido ba! Dai dai Mahaifiyar Sagir d in ta fito .abun ya faru a kan idanunta dan haka ta k arasa cikin sassarfa tana rafka salati da k arfi wanda hakan ya yi sanadiyyar fitowar mutanen gidan daga cikin d akunansu. Tana k arasawa ta rufe Minu da duka Matar ta tsufa sosai ya san ko yunk urin hana ta ya yi tsaff zata kife a wajen shiyasa kawai ya rabu da ita ya saka hannunsa ya kare jikinsa ita kuma tana ta dukansa tana kuka tana cewa Wallahi idan wani abun ya samu idon Sagir sai na yi shari ah da kai. Mugu kawai shegen Yaro Inna ba ta so shiga sabgar kowa ba yau amma duk yadda ta so sai abun ya gagareta, dan haka ta tashi ta fito fuskarnan a had e tamau kamar ba ta tab a dariya ba. Ba su san ta k araso wajen ba sai da ta shiga tsakanin Minu da matar ta rik e mata hannu tukunna. Murya cike da b acin rai ta ce Ana barin halak ko dan kunya, fisabilillahi ko me ya yi miki kuma ko me ya faru ai bai kamata ki dinga d aga murya kina sheganta mini Yaro ba! A gidan ubansa fa kike haya. Yanzu kuma idan na saka baki sai ace na cika fad a a ga laifi na bayan kune kuke shiga sabgata. Har da d an gudu gudu Kaka ta fito ta ce ai tun jiya na gaya miki ki nemo ubansu ba dai d ana ba dan haka ki daina wani hak ilo kina ik irari Cikin katseta sannan a tsawace Inna ta ce Dakata malama ban sako da ke ba! Ko kinga na tanka ki tun jiya? Kina so ki san dalili? Ba ta jira ta bata amsa ba ta ce saboda maganarki ba ta kai in tsaya in sakata a mizanin hankali ba shiyasa, in da ace maganar mutane masu hankali kika yi da sai in saurareki amma ba ni da lokacin shirmenki ne shiyasa ban biye ki ba kuma duk mutum mai hankali ba zai biye miki ba ko kinga shi Mallan d in ya biye ki? Nan ma bata jira me zata ce ba ta ce saboda ya san me yake yi. Jakai, dak ai sannan munafukai sune suke biye ki suke bawa zancenki mahimmanci. Ni nan kin ganni tunda har ba Mallan ne da kansa ya furta wannan zance ba to idan kinga dama Hadiza ki d auki loudspeaker kina bi layi layi kina fad a wallahi ko a jikina. Ta k arshe maganar tana dukan cinya cike da bala Kuka Kaka ta fashe da shi ta juya ta shige cikin d aki tana cewa ko uwar da ta haifeta ba ta kiran sunanta saboda sunan mahaifiyarta ne amma yau ga suruka ta ambaci sunanta bayaga kiranta da mahaukaciya da ta yi, wallahi ba zata zauna ba bar musu gidan za ta yi yau za a yi ta ta k are Mallan sai dai ya zab a dan wallahi ta gama zama gida d aya da su Dije. Asabe da Maman fati ne suka bi bayanta suna rarrashinta yayinda Inna ta doka wani uban tsaki ta juya kan Maman Sagir ta ce ke kuma me Minu ya yi miki? Wadda ba ta san alkhairi ba! Ya kike magana kamar wadda ta ba ni waje na zauna a kyauta? Haya fa nake yi? Cikin katseta Minu ya ce Anty ki yi hak uri a bar maganar nan, Inna dan girman Allah kema ki yi hak uri ki kyaleta ya wuce. Cikin fushi Maman Sagir d in ta ce eh ai dole ka ce a bar magana tunda mu ka cuta, to wallahi ba ka isa ba! Dole a biwa Yaro hakkinsa. Ta fad i haka tana Isa kan Sagir wanda zuwa yanzu ya ware daga mutstsika idon da yake yi amma yana nan zaune a inda yake kawai yana kallon Minu irin a fusace yake da shi d innan. Duddubashi ta yi kamar wani k aramin Yaro tana dubashi tana cewa ya idon naka? Kana gani sosai? Jinjina mata kai kawai ya yi, ba ta d ago ba ta ce Shege mugun Yaro haka nan kawai zai janyo maka, ido ai ba abun wasa bane Wata mahaukaciyar fisga Inna ta yi mata ta juyo da ita sannan ta ce na rantse da mahalliccina ko da wasa idan kika sake shegantamin Yaro da k azamin bakinkin nan sai na tsinka miki mari!!! Da sauri Sagir ya taso ya zo ya tsaya a gaban Inna fuska a had e ya ce cikata!! Sake damk eta Inna ta yi ta kallesa cikin fushi ta ce ba zan cikata ba dan kutumar ubanka!!!! Yunk urawa ya yi zai yi kan Inna Minu ya yi wani irin jifa da shi a fusace ya ce kar ka soma! K aramin mahaukaci Ai kuwa a take gidan ya hargitse dan Sagir sake tasowa ya yi Minu kuwa ya rufesa da duka dama a fusace yake. Da kyar bayan mazan gidan sun shigo suka samu suka kwaci Sagir daga hannun Minu amma fa ya daku dan har ya fasa masa saman ido da hanci da baki. Sai da Iyya ta zo itama da kyar tukunna ta lallab a Inna ta cika uwar Sagir wadda take ta fisge-fisge amma ta gagara kwatar kanta daga hannnun Innar. Ana cikata ta yi kan Sagir tana mai fashewa da kuka kafin ta d ago fuska dagaje dagaje ta fara jero Allah ya Isa Ya Kamal ne ya ce mai ya faru? Ya yi maganar yana kallon Minu. Banza Minu ya yi da shi yana huci sai da ya sake cewa Mai ya faru? Iyya Mahaifiyarsa itama ta cewa Minun mai ya faru tukunna ya ce Kama sa na yi yana k arewa Dije kallo ta juya baya, shine na tsole masa ido Daga nan kawai ya yi shiru. Kwashewa da dariya Ramma ta yi ta ce Allah ya kyauta daga haka ta juya ta wuce ciki. Yayinda Asabe wadda fitowarta kenan daga d akin Kaka ta k araso wajen ta ce amma wallahi ka ji kunya Minu! Saboda an kalli k anwarka? Cikin zafi Maman Sagir ta taso ta ce kuma ina ita k anwar tasa ita ce ta fito babu mayafi? Allah na tuba Yarinya ragowar d an daba ta gama karuwancinta komai ya fito rass ai dole Yaro Namiji mai lafiya ya kalla. Ta fad i maganar idanunta jazur cikin na Inna cike da b acin rai! Dariya Asabe ta yi kafin ta ce maganar ki dutse. Eh ai ba zanga laifinki ba tunda na san Abokin mutuwa kike nema! Gara mu zargi kuke yi ashahadu a wuyanku! Yanzu idan aka ce ku kawo sheda na san wallahi sai dai a kasheku! Saboda na yarda da Dije d ari bisa d ari kuma wallahi abun kunya ba dai a kanta ba ta fi k arfin haka!!!! Ke kuwa a gidanku ni shaida ce y ar uwarki sai da ta haifi shege ga shi chan yana yawo. Da sauri Iyya ta matso ta ce Halima ya isa haka gori babu kyau ko me suka yi miki ki barsu da halinsu. Sannan dan Allah kar in sake ji kince wani ya fi k arfin k addara Dariyar rainin wayo Asabe ta yi sannan ta ce Allah na tuba k addara kuma ta nawa? Jiya ma fa kina ji an ce har filin ball ta bisa dayake abun ya motsa tana so a sosa mata inda yake yi mata k aiyi! Cikin tsananin b acin rai Inna ta ce tsabar ke dak iyaya ce ki rasa a ina zaki yi sharrin naki sai a filin ball tangamemen waje idanun kowa a kansu? Idan kin tashi sharri ki dinga yin wanda hankali zai d auta mana! Ko da yake ba zan ga laifinki ba dan hatta Kattime ashe da cikinta aka yi auren iyayenki sannan yanzu haka babu aure a tsakaninsu suke zaune amma har fad an kwana take yi da kishiyoyi, amaryar gidanku ma da aka saka kwanaki saboda fad an kwana da tayi da uwarki ne aka saketa bayan ita uwartaki a musulunci ma bata da kwanan sai dai zina! ifff haka Asabe ta d auke wuta, tabbas baki ya san abunda zai fad a amma bai san me za a mayar masa ba! Ta rasa ta yaya Halima ta ke samun zafafan surrrukanta da na gidansu, wanda a duk lokacin da suka yi fad a sai an ji new update daga bakinta. Cikin fushi Inna ta ci gaba da cewa dan haka Zina da kike ta ambata a gindinki ta k are ke da y an gidanku da iyayenki ba dai Dije ba wallahi na fad a na k ara fad a Dije ta fi k arfin wannan lalatar dan na yarda da tarbiyyar da na bata. Kuma ba ta gada ba ba ta sha a nono ba kamar yadda yake yawo a jininku. Ke kuma da kike cewa dole Sagir ya kalleta yanzu hakan har abun alfahari ne? Ragowar mazan
Chapter 19 · 0% Book details