← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 59

Sashe 16

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

gadon ba, kamar ba buk atarsa ce ta kawo su d akinba. Ya fi kusan mintuna ashirin Yayinda Hadiman nan mata su uku suke a tsaye kyarr! Ko numfashi da kyar suke jaa kafin da kyar ya magantu ba tare da ya kallesu ba hankalinsa yana a kan wayarsa ya ce undress yourselves A take jikinsu ya d auki karkarwa kamar an jona musu wutar lantarki, dukda mutum d aya ce kawai ta fahimci me yake nufi amma ragowar suma sun d an fahimci yaren nasa Kuka d ayar ta saka ta durk usa tana shirin yin magana ya yi fito, a take sannan da gudu wani hadimi ya shigo ya na zuwa ya durk usa a gabansa kansa a k asa Ka kaita mari Kawai ya ce ba tare da shima ya kallesa ba. Da a kaika mari d in da yake a cikin masarautar gara a kashe ka ta hanyar rataya a cikin kasuwar garin gashi a k aida idan ka shiga Mari sai ka yi shekara uku ma tukunna za a waiwayeka. Kuka sosai ta fashe da shi jikinta yana karkarwa tana rok o tana mai neman yafiya a wajen wanda ita kanta ta san bai ma san mecece kalmar yafiyar ba! A haka aka jaa aka fitar da ita waje babu tausayi babu jin k Yana fita waje ragowar y an matan suka shiga yin abinda suke tunanin yana nufi hankulansu a masifar tashe dan in dai har hakan yake nufi to alk iyamarsu ta tsaya ne saboda sun san me zai biyo baya sannan a al adar masarautar tun daga kan matan sarki har zuwa kan baiwa in dai a cikin masarautar kike aka yi aurenki aka kaiki gidan Mijinki ya tadda hanyarki a bud e to hukuncin kisa ne a kanki! Matan sarki da wasu daga cikin masu asalin mulkin masarautar ne kawai ake yi musu d aurin rai da rai a kurkukun sarakuna ko kuma a yi musu tozarcin da wata sai ta zab i mutuwa ma da shi, amma ragowar kam musamman ma bayi a washegarin ranar ake tsiresu. Tsindir haka suka yi suka tsaya a gabansa jikinsu na karkarwa. Da camerar wayarsa yayi amfani ya gama k are musu kallo ta cikin wayartasa ta hanyar zooming kafin ya ce su juya, nan ma ya gama k are musu kallo Tsaki ya yi cikin d an b acin rai ya ce get out! Da sauri kamar za su zuba ruwa a k asa su sha don murna suka sunkuya suka rarumi kayayyakinsu suka fice a guje tib ir tib ir zannuwansu kawai suka samu damar yafawa suka fice suna masu k arin mayar da ragowar suna masu jero hamdala a zuk atansu. Suna fita ya mik e tsaye cikin d an fushi ya kalli amintaccen hadimin nasa wanda ya yi saurin saukk owa ya sunkuya a gabansa. Cike da izza sannan ka na iya jiyo b acin rai a cikin muryar tasa ya ce is that the best you can find? Jinjina kai Hadimin nasa ya yi ya ce daga cikin dukkannin Hadimai kamar yadda ka buk ata, waennnan sune kawai muka samu masu irin shekarun dai da ka ambata Dalilin kuwa shine ka san batun satar da aka yi a parlourn Gimbiya Zakiyya ya janyo an rasa dayawa. Amma na ga wasu a cikin bayin masu lamba d To hell with them Ya furta hakan cikin zafi, wanda ya sanya Hadimin na sa yin shiru. Fuuuu! Ya juya ya fita ransa a b ace, a take Hadimin ya mik e ya bi bayansa yana fita wasu guda goma a cikin masu tsoron k ofar d akin suma suka take masa baya. **************** BULAMA 0806 402 1951 ANA MALIK!! Book 01. Page 07. Humairah Bulama. Mikiya writers Association. Dije tana barin wajen azabar kararar k auyen su Sumayya ta sake k aimi a jikin Ma a. Duk dauriyarsa bai san lokacin da ya tafi kamar zai kifa ya damk i bencin dake ajjiye a gabansa da sauri ba, a take wani irin zazzafan gumi ya shiga tsattsafo masa fiye da farko ta ko wacce b ular gashi dake a jikinsa kamar wanda ya watsa ruwa. an ya rage bai kurma uban ihu ba, dai dai lokacin da su Oscar suke k arasowa wajen a guje sakamokon ganin halin da yake a ciki shi kuma bugun zuciyarsa ta fara sauyawa ya shiga janyo numfashi da kyar. A machine suka goya shi suka nufi gida da shi wanda kafin su k arasa gidan Oscar shima ya goga, kad an kuwa ya rage bai zubar da su ba, suna isa ko gama cikakken parking bai yi ba ya diro a gigice ya afka d akin Ma a ya shiga toilet ya kunnawa kansa ruwa wanda hakan ya zamo masa kamar mabud in masifar k aiyi. Allah ya so shi bai kwab e kayan jikinsa ba dan a hakan sa ya fito yana zabga ihu kamar ba Oscar ba. Ihun nasa ne ya fargar da Mama ta fito daga kitchen da wuri dai-dai Scorpion ya kamo Ma a yana tafiya da kyar numfashinsa yana fita da kyar sama-sama. Shi kansa Scorpion d in zuwa yanzu ya goga dauriya ce kawai yafi Oscar sannan shi bai zubawa kansa ruwa ba. Mama tana ganinsu a haka ta nufesu hankali a masifar tashe. Da kyar Scorpion ya iya cewa karara ne Mama kar ki matso. Dan haka ta ja ta tsaya sai kuma ta k arasa ta je ta shimfid a musu tabarma Scorpion ya k arasa da shi kai ya samu ya taimaka masa ya kwantar rigingine dan zuwa yanzu shi kam bai ma san a wacce duniyar yake ba ga numfashi yana ta d aukewa kamar mai shirin barin duniyar. Kuka Mama ta saki har ta mik e tana shirin ce musu su tafi asibiti sai kuma ta koma ta zauna dan ta san azaba da bak in ciki ne suke jefa shi a cikin irin wannan halin dan haka ta shiga yi masa tofi. Kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta mike ta ce bara in d auko manja a zuba muku yana rage k ayin. Da sauri Ma a ya ruk o gefen zaninta tana juyowa ya girgiza mata kai kawai. Ta fahimci baya so ta bar wajen ne dan haka ta koma ta zauna ta ci gaba da yi masa tofi yayinda shi kuma ya lumshe idanuwansa kawai ya na mamakin Dije Da mugun gudu Oscar ya afka cikin kitchen d in ya kinkimo galan d in manja ya shiga kwararawa kansa gaba d aya ya gigice, zuwa wannan lokacin shi kansa Scorpion duk dauriyarsa ya fara murk ususu kamar mai shirin fara breakdance, ganin dauriyar fa ba zata kaishi ko Ina ba gashi abin sake k arfi yake yi ya sanya ya mik e ya k arasa ya shiga shafawa jikinsa manja shima, kafin minti d aya sun yi nasha nasha abinsu da manja in ka gansu kamar ma su tallar maita. Kuma har zuwa wannan lokacin a gigice suke dan su dai ba su ji alamun sassauchi ba. Mama ita dai tanata kallonsu duk da halayyarsu amma sai da ta tausaya musu, dan haka kawai take ta binsu da sannu. Shi dai Ma a bai ce komai ba kawai ya lumshe idanuwansa, chaaan! Kamar a mafarki Mama ta ga wani sassanyan murmushi ya sub uce masa. Sai bayan kusan awa hud u tukunna da kyar aka samu k ayin ya d an lafa, ba wai ya d auke gaba d aya bane kawai dai ya d an lafa. Har zuwa wannan lokacin Mama tana tare da su tanata yi masa tofi shima kuma ta bashi add i tace ya yi ta yi, idan ta yi salla ta idar ta yi addu a sosai ta tofa masa, ya d an ji dama-dama haka suma su Oscar da ta basu addu i ta ce su yi ta yi, amma har zuwa wannan lokacin numfashin Ma a bai dawo dai-dai ba kuma idanuwansa a lumshe suke Lissafi kawai yake yi yana mamakin Dije lokaci zuwa lokaci kuma yake sakin wani lallausan murmushin da yake shirin fara firgita Mama.. tabbas yau kam ya had u da wadda ta azabtar da shi cikin sauk i, abunda zaratan maza suka gagara yi yau gashi Yarinya k arama ta yi, dan tabbas shi kansa ba zai iya expressing kalar uwar azabar k ayin da ya kwasa a yau d in ba. Sai da ta ga sun d an fara nutsuwa tukunna ta nemi jin ba asi, har Oscar ya bud e Baki Ma a ya yi saurin juyawa ya zuba masa rinannun idanuwansa da har yanzu basu kai ga fara dawowa dai-dai ba. Shiru ya yi ya had maganarsa, ya sunkuyar da kansa k asa zuciyarsa kamar zata fashe tsabar takaici! Tabbas yau idan Oga ya hanasa halaka Yarinyar nan wallahi watak il sai jininsa ya hau idan bai kamu da ciwon zuciya bama kenan! Ko da ace bai halaka ta ba to Yarinyar ko y ar gwal ce ya kamata a barsu su yi mata tambarin da har tsufanta ba zata tab a mantawa da shi ba. Scorpion kam shi bai yi tunanin yi mata komai ba dama dan ya san Oga ba zai tab a bari ba (kamar kullum), amma fa shima ya shak a dan har yanzun bai gama dawowa dai-dai ba, wai kamar su ace wannan y ar Yarinyar ta haukata ta gigita a cikin k anin lokaci amma gashi da ikon Allah haka nan suna ji suna gani za su bar komai ya wuce saboda ba su isa yin komai a kai ba. Shiyasa ya shiga zaginta da aibantata kawai a iyaka cikin zuciyarsa kamar wani Yaro dan ya san bai isa ya yi a fili ba. Sai da suka sake nutsuwa tukunna Oscar da Scorpion suka ce masa Bara su je su kimtsa Ko da suka fita sai da suka bawa jama a tsoro Allah ma ya so su duhun dare ya iso, yayinda waensu ma da kyar suka iya gane su, haka nan suka wuce zuwa d akunan su da suke haya a wani gida mutane suna ta satar kallonsu dan ba su Isa su yi k iri-k iri ba.
Chapter 16 · 0% Book details