← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 59

Sashe 3

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

hannayenta biyu zata b ulawa Ma a shi da su scorpion sakamokon kunnen uwar shegun da suka yi mata (sun k i tanka mata kuma sun k i su bata hanya ta wuce). Da mugun sauri Minu ya kamo ta ya juyo da ita ya kakkab e hannuwan nata cikin fushi ya ce sai yaushe za ki fara jin magana ne? Eh?? Ya fad in da mugun k arfi kamar mai shirin rufeta da duka! ..Yanzu haka Inna tana chan a kwance jininta ya hau jiya da kyar ya rage ba a basu gado a asibiti ba duk a ta sanadiyyar fad an DIJE da Kaka wanda daga k arshe ya k are a kan Innar dan babu kalar cin mutuncin da Kaka bata yi musu ba a jiyan, amma shine yanzu tsabar Iskanci ta zo zata zubawa Ma a da Yaransa k asa a jiki salon ta janyo musu masifa Da kyar ya iya lallab a zuciyarsa da take ingiza shi akan ya rufe ta da duka, ya juyo a hankali bayan ya sakata a bayansa ya na kallon k asa dan a k ida ba a had a ido da Ma a ya ce ka yi hak uri dan Allah, Yarinya ce za a yi mata fad Irin tsayuwar sojoji ya yi ..ta inda ya saka hannayensa duka biyu a bayansa ya d an raba k afafunsa ba sosai ba ta hanyar bubbud a su kad an! Yayin da ragowar samari biyun suke tsaye a ta gefe da gefensa d an bayansa kad an dan basu jera da shi ba! Dogo ne sosai sannan yana da fad in k ashi amma bai cika k iba ba sam, yanayin surar jikinsa dai a murje take sannan a murmure kuma a murd e wanda hakan ya taimakawa surar jikinsa ta giant sake baiyyana. Ba bak i bane ba kuma ba za a kirashi da fari ba, yanada dogon hanci da madaidaitan idanuwa masu tsayi da asalin kyau, da matsakaicin baki wanda yake nan bak irin wuluk! Kyakkyawa ne idan ka k ura masa ido wanda tsage-tsage da tabubbunan da suke a fuska har ma da ilahirin jikinsa ne suka bada gudunmmawa wajen b oye ainahin kyawun nasa . Daga kan tsakiyar goshinsa wata mahaukaciyar sara ce ta taho a karkace ta bi ta kan idonsa na hannun hagu ta sauk a a dai dai setin k arshen kunnensa, Allah ya taimake sa bata tab a masa idon ba dan tar yake kallonta kuma kana ganin idon ka ga mai lafiya sai dai ta bi har ta kan saman fatar idon nasa ana ganinta tarr! Sai kuma yanke yanke wajen kala biyar a sashe daban daban na fuskar tasa. Kamar yadda fuskarsa take haka nan jikinsa shima yake babu kyan gani, gashi dai shi d in musulmi ne amma jikinsa har da tattoo a wajen damtsen hannunsa na dama an rubuta mamana da wani font mai kyau da heart a gaba y ar k arama. arafuna kuwa su sark i da zobuna da belt da takalmin jikinsa kamar wani kare. Yana sanye da jeans d in khakin sojoji da bak ar vest kanshi babu hula sai wani d an Iskan aski. Yaransa kuma gajerun wanduna ne a jikinsu sai tshirt da p cap a kan d ayan, yadda jikinsa yake haka nan suma nasu ya b aci da tabubbuna d ayan har da k unar wuta a kafatarin ilahirin b arin fuskarsa. Tunda Minu ya fara magana ya kafe shi da idanu ba tare da ya ce komai ba. Sai da ya dire aya tukunna ya sa hannu ya turesa gefe ya gyara tsayuwar sa sannan ya yi taku biyu ya isa gaban Dije yana zuwa ya sa hannu ya finciko hijabinta ta tafi zata afka jikinsa Minu ya yi kalmar shahada ya yi kukan kura ya shiga tsakaninsu ya sake ture Dije daga garesa a karo na biyu. Cika mata hijab d in nata ya yi ta hanyar ware hannuwansa duka biyu da k arfi kuma a lokaci guda kamar wanda aka cewa action! D an taku d aya ya yi ya ja baya dan sosai Minu ya shige cikin jikinsa wajen k arin raba kusancinsa da Dije, sai da ya runtse idanunsa ya yi iyaka bakin k arinsa wajen tausar kansa dan kar ya yiwa Minu illah tukunna ya bud e idanunsa da suka rine da b acin rai ya zubasu a kan Minu wanda ya sha jinin jikinsa ya fara karkarwa, bakinsa na karkarwa yana shirin yin magana d aya daga cikin Yaran Ma Oscar ya d aukesa da wani irin gigitaccen marin da saida ya tafi kamar ana ingizashi ya je ya bugu da wani k aton dutse. Dai dai nan motar y an sanda ta doso wajen wanda hakan ba k aramin mamaki ya bawa mutanen da suke d an lellek owa ba dan basu san amfanin zuwan y an sandan ba. Aikuwa ilai!..Suna hango shi suka ja suka tsaya suka k arasawa wajen, suna mamakin k aryar da samarin suka yi musu suka kwaso su suka kawo su nan wanda sun san tab a shi dai dai yake da rasa aiyyukan su, duk matsayin mutum kuwa. Tunda aka yi wurgi da Ya Aminu ta nufesa ta durk usa a wajen ta fashe da kuka dan sam baya motsi gashi gefen kansa inda ya bugu da dutsen sosai ya fashe. Kukan da take yi sai da ta bawa kowa tausayi a wajen gashi babu mai damar taimakonsu. Tunda ta je ta durk usa a wajen yake kallonta, kafin daga bisani ya juya ya yi wani tsaki ya bar wajen. Sai da ya yi wajen taku biyar tukunna Yaran nasa suka samu damar binsa a baya dan abun ya yi matuk ar basu mamaki! Su da suke shirin fara cin uwar Minu a hakan a yadda yake amma kalli abinda Oga ya yi!? Sosai abun ya d aure musu kai amma sai suka yi tunanin maybe barinsa zai yi ya warke tukunna ya ci ubansa ta yadda zai fi galabaituwa! Amma kuma duba da yadda Yarinyar itama ta dad e tana yi musu hauka amma ya hana ko kallon banza ne a yi mata ya sanya suka saka kokwanto a al amarin A haka dai suka bishi a baya zuciyoyinsu fal tambayoyin da basu isa su yisu ba. Su Ma a suna wucewa kowa ya tuttulo aka yo kan Minu har da y an sandan da aka d auko takanas akan su yiwa tufkar hanci kafin a yi b arna amma suka mak ale. Suna zuwa wajen wata tsohowa ta ce Dalla chan malamai ku matsa daga nan, baku da amfani kwata kwata ga al aumma wallahi, ace Yaro kwalli d aya ya addabemu ya hana mu sukuni amma kun kasa tab uka uwar komai! Tsoronsa kuke ji ne? Ko ya fi k arfin hukuma ne? Ai kuwa kamar jira jama ar wajen suke yi nan suka hau kan y an sandan kamar za su rufe su da duka. Basu kula su ba instead k ari suka yi suka saka Minu a mota a ka wuce da shi asibiti zuciyoyinsu fal alhini! Tabbas abunda mutanen nan suka fad a gaskiya ne amma suma d in komai ya fi k arfin su ne shiyasa. Kusan duk mutanen da suka zo da y an sandan ne suka tafi kai Minu asibiti, d aya daga cikin biyun da suka taho da shi wajen Ma azu Ya Kamal kuma ya tafi kai Dije gida domin su je su sanarwa da su Mallan halin da ake ciki. Babban gida ne gidan haya mai d auke da d akuna a k alla guda goma sha uku ta wani dogon soro suka bi kafin su k arasa cikin gidan wanda tsakar gidan dududu ba zai iya cinye k ananan motoci biyu ba amma sai uban tarkace da igiyoyin shanya ga wata uwar rijiya da aka yiwa d ogwarago kana shiga ita kake fara hange. Band akin maza a farko-farkon dogon soron yake yayinda na mata yake ata gefe jikin k ofar shigowa cikin tsakar gidan sai kitchen a ta chaan lungun bandak in matan fuskarsa tana kallon ka idan ka kalli direction d in da yake. Daga kitchen d in har band akunan gaba d aya babu wanda ya samu arzik in k ofa sai dai in ka zo shiga bayin ka nemi zani ko dai wani kyallen ka yafa ka yi uzurin ka wanda hakan shike nunawa wanda ya tunkaro wajen akwai mutum a ciki. Siminti ne a shimfid e a tsakar gidan wanda bashi da maraba da rairayi sakamokon farfashewar da yayi ta koina. Daga b angaren dama d akuna ne guda hud an fici fici a jere sai guda uku suna kallon su yayinda hud u suke a ta chan k uryar gidan a jere suna kallon k ofa sai guda biyu manya manya sosai d ayan har da band aki a cinkinsa suna kallon ukun k ofofinsu jere da k ofar shigowa amma d ayan d akin an bud e masa wata k ofar ta soro. A tsakar gidan akwai kejin kaji mai hawa biyu da alama kiwo mai shi yake yi sannan alwai rago da akuya sabbin haihuwa ga kuma uban tulin wanki k ulli-k ulli wani a kan wani sun kai guda goma wanda kana gani ka san akwai mai wankau a gidan. A tsaye cirko cirko suka tarar da mutanen gidan Yara da manya da y an mata..tsakar gidan ya cika taff da jama a tubarkallah har da mak wafta. Zainab ta hanga a tsakiyarsu Yarinyar da ba zata haura shekaru sha biyu ba, hankalin kowa a kanta tana ta zuba bayani dalla dalla, duk inda ta kai aya ta dire sai a hau salati da sallallami ana tafa hannu sai kuma a yi shiru ita kuma ta d aura daga inda ta tsaya. Tsabar yadda hankalin ilahirin jama ar yake a kan Zainab babu wanda ya lura da shigowar Dije da Ya Kamal, idanunsu ya rufe daga jin labarin A bu wanda yake kamar busharar shiga gidan aljannah a zuciyoyin wasu. Ganin yadda aka bata muhimmanci aka yi mata k awanya kowa ya bata hankalinsa ya sanya Zainab d in ta fara had awa da k
Chapter 3 · 0% Book details