← Book details Ana Malik Part One Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 59

Sashe 53

Ana Malik Part One Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yara bane ba dan haka suka rabu da ita kawai suka bishi da addu a, suka rik e abun a zuciyoyinsu gashi dama sun ga ma duk a rikice take kwana biyun hakan ya sanya kawai suka rabu da ita suma suka kama sabgogin gabansu. Nuraddeen shine a tsaye a kan komai, shi yake ta nemo mata Likitoci da Malamai duk da kuwa ya san aikin gama ya riga ya gama dan daga gani asirin mai tauri ne ba shi da makari. Gashi hatta Malaman da suke aiki a kansa tuk uru ba su rik e Allah shi kad ai ba ballantana a saka ran dacewa Sarakuna na garuruwan k asar kuwa k iri-k iri ta hanasu duba jikin nasa a ranar da suka yo cincirindon zuwa gaida shi, ta ce musu ya sha magani ya kwanta haka nan suka juya kowa ya kama gabansa shi da tawagarsa, bayan sun yi mata ya mai jikin tare da neman alfarmar ta mik a musu gaisuwa idan ya farka daga barcin Tun jiya da suka zo suka tafi gaba d aya ta gaza zaune ta gaza tsugunne, yau ma da sassafe gari ko gama haskawa bai yi ba ta tafi wajensa, bayan ta je ta ga yanayin jikin nasa sai hankalinta ya sake tashi! Kasa ci gaba da zama ta yi tare da shi dan haka ta fito ta dawo sashenta, ta wuce bedroom d inta. Tunda ta dawo kuwa ba ta ko zauna ba, take ta faman kai kawo dan hankalinta ya kai k ololuwa wajen tashi. Duk dakiyar ta yau kam ta sare dan ba ta san lokacin da ta durk ushe a wajen ta fashe da wani Irin kuka ba.. Babban tashin hankalinta idan Allah rufa asiri wani abun ya sami Sarkin shine wani ya hau karagar mulkin nan Ta san bayin garin sai sun fita freedom muddin aka ce ba d anta ne a kan mulki ba duba da yadda ta dinga treating d in jama Da gudu wata Hadimarta ta shigo ta na cewa ki gafarceni ya uwar gijiyata dole ce ta shigo da ni Maganarta ce ta mak ale da ta hango ta dan haka ta k arasa da gudu sakamokon ganinta a durk ushe ta na kuka. Durk ushewa ta yi itama ta fashe da kuka ta na cewa Allah ya huci zuciyar mai k asar KHAK IL gaba d ayanta! Idan ke kika koka mu kuma sai dai mu binne kawunanmu kenan dan ba za ta yo mana kyau ba! Allah ya tashi kafad un Sarki Allah ya bashi tsawon rai! In sha Allah babu abunda zai same shi Cikin share hawayenta ta kalleta da jajayen idanuwanta ta ce ce miki na yi gurd ewar da ya yi ce ta saka ni kuka? Da sauri ta shanye kukan nata dama na munafurci ne ta durk usar da kanta sosai ta na fad Allah ya huci zuciyarki idan maganata ta b ata miki rai ki gafarceni ya uwargijiyata. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauk e ta mik e tsaya ta kakkab e jikinta sannan ta ce idan kin fitar da halinda kika same ni a ciki yanzu, na san kin san zan sani ko? Za ta yi magana ta katseta ta hanyar cewa me ke tafe da ke! an zabure ta fara magana an samu gawarwakin bayi guda ashirin, sha uku mata bakwai maza. Matan an yanke musu nonuwa tare da horo me tsanani mazan kuma an yanke musu gabansu suma tare da horo mai tsanani kafin a kashe su amma akwai guda d aya yana motsi, Gimbiya Zakiyya tana a chan tare da su tana jera musu tambayoyi, da alama sune bayin da Sai kuma ta yi shiruu ta had iye maganarta da mugun sauri dan Gimbiya Mariyar ba ta san sun san asiri aka yiwa Sarkin ba. arasa maganarki Ta fad i hakan a dake! Diriricewa ta yi da farko chaan kuma ta ce .suka yi sata a bangaren Gimbiya Zakiyya Tsaki ta yi ta juya ta fita fuuuuuu kamar za ta tashi sama kamar ba Gimbiya ba. Unfortunately kafin ta k arasa shima wannan Bawan da ya rage ya cika! Dan haka bak in ciki da tashin hankali suka had e mata goma da ashirin, atleast inda ace za a san mai laifi ta hukunta shi to da zata ji d an sauk i da dama-dama Sallamar kowa suka yi, hatta Dogarai da amintattun Hadimansu a chan nesa da su suka tsatstsaya, kallon bayin suke yi suna sakewa kamar masu son gano asalin gaskiyar wanda ya saka su aika-aikar a kan fuskokinsu Suna nan tsaye kuwa aiken Oga kwatakwata ya iske su! Tabbas guda goma a cikinsu sune bayin da aka haya suka taimakawa d ayansu ya hura iskar asirin da ya nakasta Sarki a k asan dardumar gaban kujerarsa yayin share-share da goge-goge a Fada, guda biyar kuma ganin mai hurawar suka yi by mistake, sai ragowar biyar d in su kuma leakage suka samu. Kuka kawai Gimbiya Mariya ta saka tsabar bak in ciki da tashin hankali a gaban d an aiken. Da sauri Gimbiya Zakiyya ta janyota ta rungume ta shiga bubbuga bayanta, kafin ta sallami d an aiken itama hankalinta chaaaa a tashe. Ita a yadda ta tsara shine idan suka bi diddigi suka gane mai laifin za ta yi zaman sulhu da shi su basu wata babbar Sarauta shi kuma ya karya asirin da ya yi dan tabbas irin wannan asirin tare ake had osa da makarin sa guda d aya tak! Dan haka ta san za a dace, amma yanzu kam tabbas ita kanta ta fara sarewa daga tashin k anin nata sarki Zainul Abiddeen. A hankali ya saki labulen d akin bayan ya gama k are musu kallo ya juya ya kalleta. Zaune take ta d aura k afa d aya kan d aya tana kallonsa, kallon da ya kasa tantance ma anarsa. Yana shirin yin magana ta rigashi ta hanyar cewa Ka je ka rarrasheta mana! Na san kukan nata har cikin ranka kake jinsa. Wani kalar murmushin gefen Baki ya yi wanda ya k ara masa asalin kyau da kwarjini kafin ya dawo ya zo ya tsaya ta bayanta ya kama kafad unta ya ce kishin nawa da ake yi har ya kai haka? Bakinta ta tab e ta mik e ta tsaya sannan ta ce ya batun Jakadiya? Kun yi waya? Dan ni ba zan d auki risk irin wanda waennan suka d auka ba gaskiya, yanzu inda ace wani ya gansu a filin kafin su bar wajen ai da al amari ya b aci. Sannan na tabbata ba duk wanda ya samu leakage suka samu ba, zaka ce na gaya maka dole wani sabo zai fito a gaba. Kamota ya yi ya zagayo da ita ta dawo gabansa ta tsaya, a hankali ya saka hannu ya shafa soft kumatunta da kulawa ya ce wa kuma za ki kashe bayan wanchan ba shi da maraba da gawa Murmushi ta d an yi ta kalli k asa sannan ta d ago kyawawan idanuwanta ta zubasu a kan fuskarsa kafin ta ce na ga kamar ba ka d auki na wajen Mai Babban D aki a matsayin katanga tsakaninka da kujerar nan ba ko? Ajiyar zuciya ya sauk e sannan ya ce Baby, ki rabu da ita wannan, dan ni nata k aramin alhaki ne a wajena, bugu d aya kawai zan yi masa a wuce wajen, kar ki damu Ana Malik!! A k asar Khak il babu na biyuna sai Magajina an mu ni da ke! Ya yi maganar cikin kashe mata ido d aya sai kuma ya saka hannu ya kamo k ugunta ya janyota suka had e waje guda tukunna ya ce Besides Ina da ke ai babu abunda zai zame mini katanga Da sauri ta ture hannunsa cikin d an b acin rai ta ce na ga fa kwata-kwata baka d auki abun nan serious ba, mutum har biyu a gabanka amma ba ka damu ba, gara fa idan ka chanja tsari kawai ka gaya min. Ta yi Maganar tana mai shirin barin wajen. Numfashi ya sauk e kafin ya ce mutum d aya ne yanzu a gabanmu. Chak! Haka ta jaa ta tsaya ba ta juyo ba kuma bata wuce ba. You heard me right Ya fad a cikin tabbatar mata da abunda kunnuwanta suka jiye mata yanzun. Ba ta san lokacin da wani sassanyan murmushi ya sub uce mata ba, a hankali ya tunkarota yana zuwa ya sake rik e mata hannu sannan ya ce a bani goron albishir dai ko? Sai a yanzu ta juyo ta kallesa fuskarta d auke da murmushin da yake baiyyana asalin tsantsar kyawun da Allah ya bata ta ce yaushe hakan ta faru? Ya ta yi da ta gani? Yana Ina yanzu haka? Ta yi masa tambayar cike da zumud Kallonta kawai yake yi cike da so da shauk i kafin ya ce azu Allah ya yi masa rasuwa amma I think ita kanta ba ta sani ba har yanzu. Kallon da ya ga tana yi masa ne ya sanya ya fahimci tana son k arin bayani. Sai da ya jaa numfashi ya fesar sannan ya ce su kansu Likitocin tsoron gaya mata suke yi, d azu ta na barin wajen ya jaa last breath d insa. Gaba d aya hankalinsu ya tashi ni kuma kawai sai na nuna musu ban ma san me ya faru ba nima na bar wajen saboda gudun matsala. Murmushi ta yi ta rungumesa a hankali ta ce Alhamdulillah For the first time a rayuwarsa ya ji wani feeling na rashin jin dad i ya shigesa, sannan alhinin rasuwar Sarkin ZainulAbiddeen ya lullub esa, yana so ya zama Sarki tabbas yana son sarautar Kakan Kakansa ta dawo hannunsa amma tashi d aya duk sai ya ji abun ya sire masa wanda hakan ya yi matuk ar bashi mamaki, saboda in dai lissafinsa ya bashi dai-dai to tabbas abunda yake ji tausayi da jin k an Sarkin ne wanda yake kamar d an uwa a garesa, a take ya ji kokwanto ya bijiro masa akan kud irin su na d an wajen Mai Babban D aki, dan a yanzu haka ma ba shi ya yi ba yana jin babu
Chapter 53 · 0% Book details