← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 176

Sashe 84

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ta daga mata hannu alamar ta dakata. Da wani irin karfi aka murda kofar falon aka turota, daga Ummi har Yesmin da Waira sai da suka mike tsaye suna kallon Ameer da ya shigo falon fuska babu annuri, kai tsaye ya nufo inda Ummi take domin ba kallo kayan alatu suka kawo shi ba balle ya tsaya bata lokaci. Tsaye yayi a gabanta kamar without any rest yana mata wani irin kallo da ya fi kama da tsana. Waira ta saki baki tana kallon Ameer da mugun mamaki shi kam ko ganinta be yi ba domin baya ganin kowa a falon sai Ummi kadai daman zuwan nata ne. Yarfar da hannu ta fara yi tana son ta tuna sunansa ta kasa amman tabbas ta gane shi, abun ka da mai son mutane ta ga wanda ta sani sai jin yayi an shiga tsakanin shi da Ummi an rumgumeshi da karfi. Yana kokarin saka hannu ya ture kowaye ta dago kai shi kuma ya sauke nasa kan kasa dan ganin wanda ya yi masa wannan kasadar. Murmushi take masa mai sauti hakoranta a washe, lokaci daya ya gane wacece ita, ya tuna inda ya fara ganinta, alakarta da gidan ta tuna masa cewar ita ce yarinyar da ya saka a motar Nimra, daman Nimra ta fada masa yarinyar tana gidansu, a yanzu ya gane duk ganin da yake mata a gidan take. Yesmin ta fisgeta ta jefar da karfi kan kujera.

“Baki da hankali daga ganin mutum zaki tashi ki rumgume shi?”

“I know him i know him”

“Idan kika taba shi sai na kusa kasheki. Kai.. Ya zaka shigo cikin falo ka nufi uwar masu gida kai tsaye ko baka da hankali”

Ta fada tana kallonsa kamar yadda yake kallonta cikin bacin rai, shigarsa da yanayinsa be yi mata kama da mahaukaci ba, balle ta ji tsoronsa kama yayi mata da marasa tarbiya yan tijara.

“Yesmin stay out of this please, Ameer me kake so?”

Ummi ta fada sai ya dawo da dubansa gareta.

“Shaida abun da zai saka na yarda da abun da kika fada”

“Ribar nawa zan ci idan na yi maka karya? Na san wannan abun zai iya kai ni gidan yari idan har karya ne, to akan me zan yi haka? Ina da yaya mata kuma Allah ya ba ni mata idan ba ni da hujja ba zan yi haka ba, idan aka auna jinina da naka na tabbatar results daya zai ba da, ba dukiyar Mr Bashir nake kwadayi ba nima Allah ya rufa min asirin da zan iya yin komai... Amman jira ni ina zuwa”

Ta nufi stairs da sauri dakinta ta fara shiga ta bude wardrobe dinta, sai da ta fara kokarin sauke akwatin sannan ta tuna Maleek ya dauki jakar, da sauri ta fito dakinta ta shiga dakin Maleek akan gadonsa ta tararda jakar wasu takardun a watse wasu kuma be taba su ba, wadanda be taba din ba ta dauka tana dubawa har ta kai ga evidence din da take son nunawa Ameer ya sauko da sauri ta iso inda yake ta mika masa. Kallon envelop din yayi ya kasa mika hannu ya karba, kamar wanda aka cewa makomarsa ce a ciki.

“Shaidata tana nan, kuma ka tambaye duk abun da kake so zan amsa maka...”

Cikin nauyin jiki tana zuciya ya karba ya bude, takardar yarjejeniya ya fara cin karo da ita kalar wadda Hajiya Jamila ta bashi, abun da ke rubuce a can shi ne a rubuce a nan babu banbanci har kwanan wata. Daga kasan takardar kuma hoton mahaifinsa ne da ya kara gasgata masa cewar tabbas shi ba ďan Mr Bashir ba ne. Domin kamanin dake jikinsa da fuskarsa su ne a jikin hoton banbancin wannan hoto ne da ya dade shi kuma yana a tsaye ne a zahiri. Zubewa yayi kasa guiyoyinsa ya fashe da kuka ya rumgume hoton a kirjinsa.

“Me yasa zaki yi haka? Me na yi miki?”

Dukawa ta yi tana kuka

“Baka min komai ba Ameer, ban aikata hakan saboda son zuciya ba”

Ta mika hannu zata taba shi sai ya daka mata tsawa da zai da ta zabura.

“Don't touch me”

“I won't i won't”

Ta rike hannayenta da sauri.

“I'm sorry Ameer na san ban kyauta ba, amman ban aikata hakan da nufin bana son ka ba dole ce ta saka”

“Da kina so na, da baki siyar da ni ba tun farko, kuma da baki bari na rayu a gurin wani da yake amsa sunan Ubana ba, da soyayyaa bata barki kin kai wannan lokacin ba tare da ni a kusa da ke ba”

“Wallahi soyayyar ka bata bar ni na samu farinciki da kwanciyar hankali ba, a kullum da kai nake wuni na kwana a zuciya, ina tunani a wane hali dana yake ciki”

“Ni ba ďanki ba ne, you have never been my mother and you will never be, kin san abun dariyar? A kullum sai na yi ma mahaifiyata a addu'a, saboda Daddy ya fada min cewar ta mutu, kuma haka zan cigaba da yin addu'ar har a yanzu, domin har yanzu uwata a mace take, ta tafi kenan ba zata taba dawowa ba, ki bayyana gaskiya a yanzu saboda ki sake ruguza rayuwata, me yasa ba ki bar ni na cigaba da kallon mutumen da ya tsaya min a matsayin Ubana ba?”

“Saboda ina son na farantawa kowa kamin na mutu, na tafi ana yabawa ba a bini da bakar addu'a ba, ina son an roki gafarar kowa Ameer?”

“Har da mahaifina? Ba zaki taba samun wannan damar ba, ba zan taba yafe miki ba, kuma ba zan taba kallonki a matsayin uwata ba..”

“Mahaifinka yana kaunata Ameer, da ace yana raye da baka isa ka fada min wata magana marar dadi ba, ban aikata hakan dan bata ran kowa ba, idona a rufe lokacin bana ganin kowa sai mahaifinka rayuwarsa kawai nake son na ceto”

“Yana kaunarki, amman ke baki kaunar ďansa baki son jininsa, shiyasa kika zabi rabuwa da shi, why me? Miyasa baki siyar da Maleek ba?”

Kamar daga sama suka ji muryar Abiey yana amsa tambayar da Ameer yayi.

“Saboda Maleek ubansa mai arziki ne, Ameer kuma an siyar da cikinsa ne saboda a nemawa Ubansa magani”

Duk kallonsa suka yi, Ameer ya ji ina ma be zo duniya ba, da be ga wannan bakar ranar ba a rayuwarsa. Ya girgiza kai ya kalli Ummi yana murmushi.

“Na gane, tsiya kike gudu, shiyasa da kika samu wani mijin kika watsar da ni, kika tara wasu iyalin? Toh miyasa yanzu kika ruguza tawa rayuwar? Da ace da kika haife ni kashe ni kika yi da na huta ganin wannan ranar, kin cutar da ni ba ki cancanci a kira ki uwa ba, na ga soyayya da kauna daga gurin wadanda ba jinina ba, ya kike son na yi rayuwa a yanzu? Farincikin da nake ne yake kona miki rai?”

Ummi ta kasa cewa komai sai kuka take, ya mike tsaye rike da takardun ya nufi kofa har ta ya kusa fita ya juyo hawaye na masa zuba cikin ihu ya ce.

“Kin san zafin da ďa yake ji idan uwarsa bata sonsa? Da ma gidan marayu suka hai ni, siyarwar ita ta fi min zafi...”

Ya juya ya fice, kai kawai take iya girgiza masa domin kuka ya ci karfinta ta yarda bata ko iya magana. Abiey ya rikota ya nufo inda take ya rikata.

“Ya isa haka, and this is the last zuwan da yaron nan zai yi a gidan nan, domin ba zan dauki ya shigo har cikin gidana ya fadawa matata magana marar dadi ba”

Ummi ta kwanto jikin Abiey tana kuka ta dafe zuciyarta, Yesmin ma kuka take duk da kasancewar a yanzu ne ta fahimci abun da yake faruwa, Waira ma kuka take tana kallon Ummi.

“Me yasa bana da tunani, me yasa ban yi tunanin zuwan irin wannan ranar ba Abiey? Ameer zai iya shiga wani hali, ba zai yafe min ba na shiga uku..”

Shi ne abun da ta iya furta tana kuka sosai kamar zata rusa ďakin.

“Zai yafe miki amman ba a nan kusa ba, dole sai kin jure kin zama jajirtacciya, and i promise you zan yi iya kokarin da zan yi na gyara mun gyara duk wani abu da kika bata”

Ta runtse ido tana girgiza kai, zuciyarta na wani irin zafi kamar an watsa mata tafasasshen talge a ciki.

____________________

Allah sarki Ameer 😭 ni dai duk ya fi ba ni tausayi, taya kana rayuwa da iyayenka rana daya ace ba iyayenka ba ne. Wayyo Allah, ku dauke zancen jindadi ko da wahala ake sha a tare wannan kallon da kake musu a matsayin iyaye canja shi ne abu ne mai wahala, and the most painful part yana zaton uwarsa ta mutu ashe tana raye a kusa da shi........

Ni daman can team DEEN ce yanzu ma ina bangaren ďansa AMEER, gaskiya Zahra baki kyauta mana ba 🥺😏
[6/29, 9:08 PM] My S Line: 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 𝐧𝐚 𝐦𝐮𝐤𝐮 𝐛𝐚𝐫𝐤𝐚 𝐝𝐚 𝐒𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡.
𝐅𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐤𝐮𝐧 𝐲𝐢 𝐒𝐚𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐥𝐚𝐟𝐢𝐲𝐚, 𝐀𝐥𝐥𝐚𝐡 𝐲𝐚 𝐦𝐚𝐢𝐦𝐚𝐢𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐧𝐚 𝐲𝐚 𝐤𝐚𝐫𝐛𝐢 𝐢𝐛𝐚𝐝𝐮.
𝐀𝐦𝐞𝐞𝐧🥰

*Littafin WANI GARI na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*

44
Chapter 84 · 0% Book details