← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 176

Sashe 111

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamin Abiey ya kai aya Maleek yayi karaf ya karbe yana juyawa ya jera tare da Abiey.

“Zuwan Ameer gidan nan ko? Ni ma bana son haka, sai kuma na kyale ne kawai saboda Ummi ta samu natsuwa da kwanciyar hankali, amman ina jin tsoron kar Ameer ya sake sakata cikin tashin hankali wata kila ba saboda kwanciyar hankalinta ya dawo, zai iya amfani da Waira ya cimma wsni burinsa ne sannan ya jefar da ita, na nunawa Ummi haka amman ta kasa fahimta sai kokarin ganin laifina take, alakarsa da Waira tana kokarin wuce gona da iri, ita bata da hankali da wayon da zata gane”

Abiey ya sauke wayar da yake latsa gaba daya yana kallon dansa da mamaki, domin Maleek ya bude cikinsa ne ba tare da ya sani ba, shi dai kawai yana neman abokin tattaunawa ne.

“A cikin zaman Ameer a gidan nan da kuma alakarsa da Waira wanne ya fi kona maka rai?”

Kai tsaye ya amsa.

“Alakarsa da Waira mana Abiey, gida ai yana da hakkin zama saboda ka amince masa kuma mahaifiyarsa tana ciki, amman miya kawo issues din Waira a ciki? Why her? Idan ya lalata mata rayuwa fa? Na nunawa Ummi haka amman ta kasa ganewa, ina tausayin yarinyar nan Abiey tausayi take ba ni, bana son alakar dake shiga tsakaninta da Ameer, kawai dai ina dauke idona ne a yanzu saboda Ummi ta bukaci haka, but still ina jin kamar ba zan iya jurewa ba”

Maleek ya karashe maganar har wani furzar da numfashi yake saboda abun da yake ji a zuciyarsa. Da mugun mamaki da kuma tunani kala kala Abiey ke kallon dansa, this is the first time da ya zama mutum kamar kowa, yake jin kishi akan wani abu da ada can baya damunsa, wani abu da be taba samu muhalli a rayuwarsa ba. Ya dade da ganin canji a rayuwarsa ďansa, sai dai canjin ba irin wannan ba, abun da matarsa Zahra ta dade tana mafarkin faruwarsa da kuma tana jiran zuwansa.

“Kana jin ba dadi idan ka ganshi tare da ita right?”

“Yes kawai ina controlling kaina ne, if not Wallahi ko duka zan iya masa”

Abiey yayi murmushi yana jin dadin a ransa, hannunsa daya ya kai yana bubbuga kafadar Maleek.

“Karka damu, zan daukar masa mataki, ba zamu bari ya lalata rayuwar yarinya karama ba, kuma ya kamata mu maida hankali mu san waye iyayenta ko dan gaba”

Maleek ya sauke numfashi yana kallon wani gurin na dabam.

“Haka ne, amman dai for now kamata yayi mata ace ka yi duk wani abu da zai yanke hulda tsakaninsu, if ba haka ba shakuwa zata shiga kuma zai iya amfani da wannan damar ya cutar da ita”

“Haka ne, karka damu na san abun da zan yi, amman kai ma ya kamata ka rika kyautata mata, ka rika sake mata tana jin sanyinka, ita tunanin yana amfani da weakness dinta ne ya yana janta a jikinsa”

“No ni ba zan iya haka ba, ai sai ta raina ni, kuma na fi damuwa da alakarsu da Ameer ba wai dole sai ta saki jiki da ni ba”

Abiey yayi murmushi

“Ba zaka gane ba Maleek. Apart from wayar da ka tarar ina yi a yanzu ina magana da Doctor Hassan ya fada min abubuwan da ya kamata ace mahaifiyarka tana yi saboda lafiyarta amman taki, ban san yadda zan yi convince dinta ta yarda ba, musamman a yanzuda Ameer ya dawo gidan nan”

Abiey ya tattauna da shi akan abubuwa da yawa suka shafi Ummi, sai kusan ten Abiey ya shiga bangarensa Maleek kuma ya nufo bangaren Ummi. Yana shiga falon Waira ya fara cin karo da ita kwance a kujerar daya barta, sai dai wannan karon tana rumgume da zomonta ne, sai sharbar Bacci take kamar wacce ta yi wani aiki ta gaji. Tsaye yayi a kanta yana kallon fuskarta, bachi ma kyau yake mata kamar yadda idan tana farke take kara kyau da haiba. Wayarsa ya ciro ya shiga instagram for few seconds sannan ya dago kansa ya duba ko'ina na kusuwar falon, ganin shi kadai ne sai Waira ya ba shi kwarin guiwa fitowa daga Insta ya shiga camera ya saita wayar saitin fuskar Waira ya dauke ta hoto har sau biyu sannan ya maida wayar aljihunsa ya kai hannunsa ya buga gefen kujerar sai ta farka a firgice ta kalleshi.

“Tashi ki je daki ki kwanta”

Ta mike tsaye tana wani rangaji kamar zata fadi, hankalinsa sai ya dauku akan karta je hawan stairs ta fadi kasa, dan haka ya bi bayanta be matsake ta daf ba, sai dai damuwa da yayi da karta fadi ta kai kasa ya saka shi tsayawa a space din idan zata fadin ma zai iya tareta, haka ya bita har sai da ta shiga dakinta ya tsaya bakin kofa tana fadawa kan bed ya kashe wutar dakin ya janyo mata kofar a hankali. Dakinsa ya nufa he can't tell why yake damuwa da ita, at first yana tsoron kar Ameer ya bata mata rayuwa ne, yanzu kuma ya gane ba tsoro ba ne kawai har da tausayinta yana yi, na rashin wani gata sai su, bata da family sai su, da ace Ummi zata koreta a yanzu a bata da wani gurin zuwa sai da ta shiga wani hali.
Sai 11pm ya saka tufafin bachinsa sannan ya kashe first switch na dakin, ya kashe bedside lamp yana kokarin kwanta daga zaune da yake sai ya ji kamar akwai mutum a gefensa, ya kai hannunsa ya taba sai ya ji ya taba jikin mutum amman akwai gashi da sanyi sanyi a jiki, da sauri ya kai hannu ya kunna bedside lamp din ya juya be ga kowa ba, ya kai hannu ya taba gurin ya ji babu komai, for the second time ya kashe wutar ya kai hannunsa ya lalaba ko zai sake jin wani abu amman be ji ba. Gaba daya ya kunna wutar dakin ya tashi zaune da kyau yana kallon gadon, be taba jin wani abu makamancin wannan ba gidan gaba daya balle kuma a dakinsa. Ya duba hannunsa ya jimke hannun ya bude yana mamakin me yaji haka? Ya sauko da kafafuwansa kasa ya zauna bakin gadon kamin ya tashi ya nufi bandakinsa alwala yayi ya fito ya sake zama a inda ya zauna dazun ya sake kashe first switch na dakin ya dauki wayarsa dake gefen gadon ya bude qur'ane application dake ciki ya karanta Suratul milk, bayan ya gama yayi addu'ah ya kwanta ba tare da tsoron komai ba. Haka nan kawai bachi yaki daukarsa, jikinsa kuma yaki yi masa dadi daga kwanciyar da yayi, a dole sai da ya tashi ya jigina da kan gadonsa ya dauki wayarsa dan rage dare, sai gashi ya shiga Whatsapp yana duba sakowannin da be shirya amsa sako ko daya ba, ya fito ya leka Instagram ba shi da wani abun yi a gurin dan haka ya fito ya sake komawa Whatsapp, sai dai wannan karon status din mutane yake kallo, kamin ya shiga camera dake status nasa, daman he update a status on whatsapp once in awhile, kara ma Insta ya kan dora hotonsa time to time musamman a lokacin da suke yawan zama tare da abokansa. Yana shiga camera hoton Waira ne first abun da ya fara cin karo da shi domin shi ne last picture da ya sauka a wayar, he can't tell what take him so long zoom the picture yayi ta kallon kamar wani da be taba ganinta ba

*** *** ***

Can cikin bachinta mai nauyi ta ji ana kokarin saka mata hannu a cikin rigar dake jikinta. Yanayin sai yayi mata kamar mafarki take dan haka ta kara gyara kwanciyarta tana sake jiki ba tare da ta sani ba. Hakan be wadatar ba har sai da ta ji ana tashinta daga bachin tare da kiran sunanta da muryar da ta haddace tun farkon zuwanta gidan.

“Waira... Waira... Waira...”

Ta amsa cikin magagin bachi sannan ta bude idon daker, arba da ta yi da fuskar Maleek ya saka ta tashi zaune da sauri tare da buge masa hannunsa dake cikin riga yana kokarin kai wa ga kirjinta.

“Ya Maleek”

Ta fada tana matsawa baya da sauri sai ya haura saman gado da wata kalar fuska shi ba dariya yake ba, kuma ba murmushi ba, ba kuka ba da damuwa ba, haka ma fa far'ar ba ba kuma kishiyarsa bakinciki ba. Still hannunsa yake son kaiwa ya taba kirjinta abun da ba taba mata ba, bata san haramci hakan ko halacci ba, sai dai tana jin abu na wani yanayi na dabam saboda abu ne da bata saba da shi ba, wani be taba kwatanta yi mata haka ba. Sai ta kara matsawa baya taba bata fuska kamar zata yi kuka gashi tsoron take yace ta masa ba daidai ba, if not she will talk ta fada masa bata so. Ganin damuwa a fuskarta har idonta ya fara tara kwalla ya saka ya rika hannunta ya sumbanci hannu ya shafa goshinta zuwa saman kanta sannan ya sauka saman gadon ya fice daga dakin, mamakin abun da yayi mata ya hanata bachi har karfe 4am na asuba, sai 4:30 ta sake komawa bachi, bata farka ba sai da Ummi ta shigo ta tasheta, sannan ta tashi ta yi shirin makaranta ta sauko tana sanye da uniform dinta tana rike da jakarta ta makaranta. Idonta na kan Maleek dake shan ruwan sanyi tun da farar safiya har ta sauko ta isa dinning.

“You didn't greet him”

Waira ta daga kai tana masa wani irin kallo da ita kadai ta san manufarsa ta gaisheshi. Kamar kar ya amsa mata sai kuma zuciyarsa da baki suka ki bashi hadin kai har sai da ya amsa din. Ummi ta aje mata komai na karyawa sannan ta aje mata lunch box dinta a gefen kujerar dake fuskantar wadda Maleek yake zauna.

“Baki gaishe da Namra ba”

Ummi ta fada, sai a lokacin ta lura da wata Namra a gurin, domin tuni tunaninta ya tafi akan abun da ya faru a tsakar daren jiya.

“Ina kwana Yaya Namra”

“Lafiya Kalau”
Chapter 111 · 0% Book details