← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 176

Sashe 67

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nimra ce kwance a cinyar Dr Zainab, kallo daya zaka yi mata ka san damuwa da kuncin zuciya sun saka ta a gaba, domin ta rame sosai kamar ba ita ba, kwana biyu bata iya cin komai sai ruwa su ma kuma idan Ummi ta matsa mata ne, gaba daya ta dauki damuwa ta saka a ranta, bata fita daga dakin kullum tana ciki idan an kawo mata abinci yadda aka aje shi haka za a dauko shi. Duk wani kokari da yar'uwarta Namra ta yi na ganin ta dauke mata hankali daga damuwa abun sai ya ci tura domin ba kadan soyayyar Ameer ya kama ta, tana taba jin som namiji kamar yadda take son Ameer ba, bata san yadda zata cire soyayyarsa a ranta ba ko da kau shekaru dari aka raba mata nan gaba, wani irin sonshi take irin son da take jin zata iya kai karar Abiey da Ummin a gurin wadanda za su barsu su ji maganarsu abarta ta auri Ameer.

“Nimra rayuwa ta yi haka? Dubi yadda kika maida kanki? Ni dai wannan zuwan be min dadi ba sam na ji abubuwa kuma na ga abubuwan da ban jidadinsu ba”

“Mommy yanzu babu yadda zaki yi ki lallaba Abiey ya bar ni na auri Ameer? Wallahi ina son Ameer, daman na san haka zata faru shiyasa na ce zan fada miki wata magana tun a farkon zuwanki na so na fada miki abun a sirrance saboda ki san yadda zaki shawo kan Abiey sai gashi komai ya lalace ya zo ta inda ba mu zato ba”

“Nimra abun da iyeye basa so hakuri ake yi, karka zafafa kace kana so, abubuwa da yawa ba alheri ba ne a garemu, ki yi wannan nazarin kuma ki yarda da hukuncin Allah”

“Mommy ba zaki gane abun da nake nufi ba, Mommy Soyayya akwai ciwo idan kana son mutum zaka ji zaka iya aikata komai saboda ka same shi, idan kuma aka ce mutumen ya barka ko an raba ku sai ka ji kamar ka kashe kanka ka saboda bakinciki”

Dr Zainab ta yi dariya.

“Nimra kenan, ku da kuke yaya kuka san soyayya balle kuma mu da muke iyayenku? Babu alakar soyayyar da ban gani ba tsakanin Mahaifinki da Zahra, idan an bude miki sirrin yadda aka yi sanadin samuwarki zaki sha mamaki, amman da iyayenki suka yi hakuri daga baya sai komai ya zo musu da sauki fiye da yadda suka sha wahala a baya, Mahaifinki ya zo Zahra irin son na tabbatar ace be aureta abu ne mai wahala yayi aure, abu ne mai wahala alaka mai karfi ta sake shiga tsakanina da shi, saboda yana ganin ni na hana shi samun Zahra wacan lokacin, babu kalar haukar da Abiey be yi ba akan Zahra, shiyasa shekaranjiya da na gansu suna sa'insa sai abun ya bani kuma kuma yayi min ciwo, domin tun da ya aureta be taba kirana ko ita ta kawo min kararsa ba, ban ce basa samun sabani ba, amman basa bari a gane balle har ace wani ya shigo yana musu sasanci, Abiey baya son fushin Zahra ko kadan, idan tana son abu yakan fita kaunarsa amman wannan karon abun da na ji kuma na gani ya bani mamaki, sai dai ta wani bangaren yana da gaskiya domin ina hango abun da zai biyo baya, idan na yi tunani ta wani bangare ina ganin cewar gaskiya yake fada, kuma dole a daga masa kafa idan ya nunawa ďan makiyinsa kiyayya, musamman ma ta yadda abun ya bayyana, da ace ba ta wannan hanyar abubuwan suka biyo ba wata kila da an samu sauki, sai dai yadda abubuwan suka zo ne dole su fusata shi”

Nimra ta daga daga jikin Dr Zainab ta kalleta.

“Ban gane abun da kike nufi ba Mommy wani abun nw ya faru?”

Gudun kar aji mutuwar sarki a bakinta ya saka ta kawar da maganar gefe ta hanyar yin murmushi.

“Bari na tashi na duba aikin da ake kar abar Namra ita kadai da aiki, ko zaki zo muje?”

“Aa, Namra ta jidadi zata auri wanda take so an barta zata yi soyayya ta wanda take kauna ba kamar ni ba”

Ta fada tana jin wani sabon kuka na sakata gaba. Dr Zainab ta ce.

“Shi ma sai an bincike halinsa da zuri'arsa idan ya cancanta sai a aura mata idan kuma be cancanta ba sai a bata damar kawo wani kamar yadda aka baki ke ma a yanzu”

“Ni zan kawo ba Mommy, bani da kowa sai Ameer idan ba shi ba sai dai na mutu ban yi aure ba”

“Aa Allah dai ya saukewa”

Shi ne kadai abun da ta fada ta fice daga dakin. Kasa ta sauko tana jin yadda falon ya dauki kamshi ana ga shiryawa bakon Namra abubuwan dadin, ita ma ta zage dantse ana ta aikin da ita saboda bakon nata ne kuma wanda take matukar jin da shi, ko ba komai kokarin zuwan da yake cikin kwana uku abun a yaba ne, kuma hakan ya nuna da gaske sonta yake da aure ba iya chat da waya abun ya tsaya ba, domin tun haduwarsu a Instagram sau biyu kawai suka taba ganin juna a fili, shi ma kuma zuwan gaggawa yake a Abuja sai ta fita su hadu a wani gurin su gaisa, sai da ta sada shi da Ummi sun gaisa sau biyu, ita ma ta gaisa da yan'uwansa sosai har live video yayi ta gaisa da iyayensa, sun santa ta san su. Yanzu kuma ta sanar masa iyayenta suna son ganinsa sai ya zabi ya yanke duk wani abun da yake ya gabatar da kansa a matsayin mai son yarsu. Sati ta bashi shi kuma ya rage ya zabi kwana biyu, saboda damar da yake ta jira kenan na neman aurenta.

  Ummi ta fara sanar ma ranar da zai zo, ita kuma ta sanar da Abiey duk da kasancewar basa cikin yanayi na fahimtar juna a yanzu, sai dai babu wanda ya sani sai Dr Zainab ita ma saboda an yi a gabanta ne. Falon Dr ta zauna tana ta tsokanar Namra kamar ba yarta wai bata shiga kitchen ta taya Ummi aiki amman yau da yake saurayi zai zo har da ita ake komai, Juwairiyyya da Yesmin sai dariyar suke.
Dr Zainab na fita Nimra ta tashi ta nufaci kofa a hankali ta bude ta leka ganin babu kowa saman ya bata damar fitowa tana sanda kamar wacce zata yi sata ta tura dakin Ummi ta shiga ta duba ko'ina bata ga waya ba sai ta fito ta shiga dakin Namra nan ma bata samu abun da take so ba, ta fada dakin Mahmood, shi ma baya nan wayarsa ma bata nan sai Umar dake zaune a kan kujera yana kallon wasi series a laptop.

“Umar dan Allah wayarka zaka ara min”

“Okay”

Ba tare da tunanin komai ba ya cire key ya mika mata wayar sai ta karba ta fita ta koma dakinta da sauri, number Ameer ta saka ta kira wayarsa sai ta ki shiga, saboda ba shi da number ba, ya saka only wadanda yake da number su za su iya kiranshi, ta gwada hakan ya fi a kirga bata shiga ba, daga karshe ta yanke shawarar aika masa da sakon sanar da shi cewar ita ce ya kira ta.
Sakon na shiga kiransa na shigo wayar Umar dake hannunta dariya mai kamar kuka ta amsa kiran ta kara a kunnenta.

“Hello Ameer”

“Nimra how are you?”

Sai ta fashe da kuka.

“Kai ma kansa ba kalau ba, Ameer ina cikin wani hali kamar zan mutu, na rasa ya zan yi na yi missing dinka”

“I miss you too i miss your touch your smell, ina ta tunanin ko a wane hali kike a yanzu, na so na kira Umminki amman ban san me zan ce mata ba, i don't know why ina dai jin kunyarta, wayarki ma tana hannuna i thought zasu kira su karba ba su kira ba”

Ta rike wayar da hannu biyu taba jin kamar ta shige ciki saboda muryar Ameer da take ji.

“Ina kaunar ganinka Ameer, dan Allah ka zo?”

“Ina?”

“Gidanmu, ka zo ka fada musu cewar kana sona kuma zaka aure ni, damar da ka ce min kana jira yanzu ne ya dace ka yi haka, so that mahaifina ya yarda sona kake da gaske, ya yarda aurena zaka yi”

Yayi shiru kamar ruwa ya ci shi.

“Ameer”

“Nimra.. Listen to me let me think about it”

“Ba abu ne da yake bukatar tsayawa tunani ba, a yanzu ya dace ka yi komai Ameer, saboda Abiey yace kasa da wata daya zai mana aure ni da yar'uwarta Namra, ita a yau ma wanda take so zai zo ya gaishe da su Ummi, idan ba ka yi haka a yanzu ba ba za su yarda da gaske aurena zaka yi ba”

“Nimra....”

Sai kuma yayi shiru.

“Nimra.. Ba zan iya yin haka ba, abun kunya ne a gareni ace na zo ina ta hauka akan kanwar abokiya kuma makiyina, bayan iyayenta sun nuna min tsantsar kiyayya, ko baki ji abun da mahaifinki ya fada ba a lokacin da ya zo ya tafi da ke?”

“Ameer karka duba komai, kai da bakinka ka fada min cewar ka shirya fuskantar duk wani kalubale akaina...”

“The things is.... I'm fucking lie, ba gaskiya na fada miki ba, shiyasa na kasa yarda na barki ki sake aikata kuskure, saboda zaki kara jefa kanki da iyayenki a cikin damuwa ne kawai, and maganar Allah na tausaya miki matuka”

“Me kake nufi Ameer?”

“The whole life da muka yi is set up, na shirya haka ne saboda na rama abun da ke da dan'uwanki kuka min, kuma na bakata ran iyayenki kamar yadda nawa ran iyayen ya bace, sai dai yanzu na gane da gaske kin fada so na kuma kin shiryawa komai akaina, sai na ji tausayin amman ni ban taba jin sonki ba even for once, da farkon haduwa dake na dauke ki kamar kawa ne ina jin na sake dake back then na gane komai shiri ne ke da yayanki Maleek sai na shiryawa daukar fansa”
Chapter 67 · 0% Book details