← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 176

Sashe 148

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Yanke hukunci ba a hannunka yake ba Eid karka zafafa, kuma kar bacin rai ko soyayya ta saka ka manta da ka'idodi da dokikin garin nan, idan muka yafe mutum muna nufin cire hannayenmu daga duk wani lamari nasa, ko da kuwa zai mutu ne, kuma ba zamu tarbe shi ba ko da zai bukaci dawowa a garemu, ba kuma zai aura daga garemu ba.
Kaka ya taba fada min cewar kamin a haife ni, wasu mutane biyu sun taba karya mana doka, ya saka aka koresu daga garin nan, har yanzu babu ruwanmu da iyalansu, ta farko daga cikin gari take, lokacin da dadin tsafi yayi mata yawa sai ta zurfafa ta dauki maita, mu kuma ba mu yarda da maita ba, duk wani tsafi bayan wanda muka gada gurin iyayenmu ba mu yarda da shi ba, sanadin hakan muka kora Iya ta bi duniya, har yau babu ruwanmu da zuri'arta, bayan ita kuma Wasim ɗa daga masarautar nan, soyayya ta dibeshi kamar yadda take son dibarka a yanzu, ya karya mana dokoki ya shigo mana da bare, kuma ya fitar da ita ba tare da izinin kakanmu ba, daga karshe ya zabi addininsu da al'adarsa ya watsar da ta mu, hakan ya saka shi ma muka yafe shi, shi ma babu ruwanmu da shi da zuri'arsa, dan haka karka yi kuskure biyewa son zuciya ta kai ka ta baro”

“Duk wata azabtarwa da wahala da na jurewa sha a gurinku, tsawon lokacin da Waira ta dauka bata kusa, na jure ne saboda ina sonta ban taba fadawa kowa wannan maganar ba amman zan fade ta a cikin fadar nan, na san kowa ya lura da hakan, na raine ta tun tana karama har ta fara wayo, rana daya kuma sai wani ya dauke min ita?”

Wani daga cikin manyan masarauta da suke gurin ya mike tsaye ya isa gurin da Eid yake tsaye ya dafa shi.

“Kwantar da hankalinka Jarumi na, akwai mata da yawa a cikin garinmu da suke sonka, akwai matan da suka fi Waira kyau da komai ciki da wajen masarautar nan, ka rufe idonka daga ganin Waira ka bude idonka a garesu cikin kankanen lokaci za a gama da su, karka yarda zuciya ta deba ka gujewa umarnin masarautar nan, domin wannan matashin ba zai yarda ya barka maka Waira ba, ko da kuwa ka yarda ka koma cikin kalar tsafinsa ne, idan kuma muka hana masa ita zai iya gwada jayayya da mu”

“Toh a bar mu mu kara mana, sai a gane waye jarumi”

Ya fada da kakkausar murya yana tabe baki kamar zai yagashi.

“Ba mu taba gwada yaki ba, kuma ba zamu gwada saboda wata korariya a garinmu ba, ban yi tunanin karfin tsafi zai yi tasiri a gareshi ba, ko da ya ce ba zai aureta ba, ba samu yarda ta aura daga garemu ba wannan shine magana ta karshe”

Eid da duk sauran mutanen da suke fadar suka risnar da kai domin nuna biyayya ga Umarnin Sarkin da ba a musawa. Eid ya dago yana kallon Maleek fuska kamar an aiko masa da mutuwa, zuciya kamar bakin maciji dake cike da dafi, ya fice daga fadar yana hararar Maleek yana huci kamar zai fitar da hayaki. Duk wani abun da ake fada Maleek be ji ba, domin da yarensu suke maganar, Waira kuma jinta da ganinta tunaninta mamakinta zuciyarta da ruhinta gaba daya sun tafi gurin mutumen da take kira da yayanta wato Ya Maleek. Furucinsa na cewa yana son aurenta da jarumtar da ya nuna akanta sadaukarwa neman kareta sassauta ra'ayinsa da nema mata farinciki da yanci wani abu da ya kai ta rubuta a dutsen da ba goge zane da alkalamin zinari. Hawaye take irin hawayen da ba zata iya fadar na minene ba a yanzu, na farincikin abun da Maleek yayi mata ne ko kuma na samun yancinta ko kuma na komawa da zata yi gurin matar da ta zame mata uwa? Ko kuma dai na fasa kasheta da aka yi ne? Wata kila kuma na tsafin da suka ce sun yi ta aikawa Maleek ne be same shi ba.

“Nuwaira...”

Kamar wadda aka jefowa numfashi daga sama haka ta zabura ta dawo hayyacinta, sai ta lumshe ido tana jin ba a taba kiran sunanta da dadi kamar yadda Maleek ya kirata a yau ba. Rufe idon da ta yi sai ya saka shi tunanin ko bata ra'ayi ne musamman ma da yayi arba da hawayen dake zuba a idonta gashi tun da ya furta maganar take kallonsa ta kasa cewa komai kuma ta kasa dauke idonta daga gareshi.

“Ko baki so ne? Karki damu, na yi hakan ne saboda na sama miki hanyar fita daga garin nan, idan sun amince sun ba ni aurenki da zarar mun fita ba aurenki zan yi ba, za a miki aure ne best on zabinki”

Rashin Eid a fadar da zai iya fassara musu abun da Maleek yake fada, ya saka Sarkin amfanin da nasa baiwar ta tsafi ya yi communicating da aljannunsa suka fassara masa abun da Maleek ya fada, hakan kuma ba karamin dadi yayi masa, domin ya fahimci Maleek ba gaske yake son Waira ba, hakan na nufin zai fara mata yi mata butulci da zarar sun bar garin kenan, kuma hakan ya nuna Waira bata son shi, a kokarin Sarki na bakanta musu ya kalli na hannun damansa ya ce.

“A fadawa Dardu ya tada busa ya hura wuta, mata su fara nika ganyen za a daura aurensu a yanzu”

Nuwaira ta bude ido da sauri ta kalli Sarki domin daga ita sai jama'ar garin suka iya jin abun da Sarki yake fada ban da Maleek. Sarki ya kalleta yana tana tauna hakora ya ce.

“Zamu aura miki shi, kuma zamu cire duk wani tsafi da kariya ta mu da take jikinki yanzu nan, kuma duk wani abun da zai faru ko ya biyo baya karki neme mu, babu mu babu ke da zuri'arki”

Kasa cewa komai ta yi sai har lokacin hawayen ba su daina sauko mata ba. [8/9, 8:09 PM] 🦋-🦋: 74

“Ki fada masa ya cire kansa daga lamarinki in ba haka ba zai yi nadama”

Maleek yake nunawa amman da Nuwaira yake magana da yaren garinsu.

“Ba zaka cutar da shi ba Eid kai dan'uwa ne a gurina, mai matukar son abun da nake kauna, mai son abun da nake so, mai gudun bacin raina da kukana? Meya same ka ka canja? Kalamanka da kamanin da nake gani a fuskarka ba su ne na Eid da na tafi na bari ba, wannan mutumen shi da iyayensa tarbe ni, sun saka hannu biyu sun rumgume ni, ba dan sun san daga inda na fito ba sai dan karamci da sanin ya kamata irin na su, sun nuna min kauna, a gurinsu na san abun da ake kira da tsabta da kauna da soyayya, a gurinsu na san me iyali yake nufi, a lokacin da zuwa gida ya kama ni, suka sako ni a mota suka rokoni har kofar garinmu akan me kake tunanin idan ka nuna masa tsaya zan ji dadi? A wane hali zan bari ka cutar da shi? Da wace Hujja zaka zabe ni ka bar shi?”

Eid ya dauke hannunsa yana kallon Nuwaira dake magana taba zubar da hawaye. Ta sauke kanta kasa ta kalli hannun Maleek dake rike da nata, sannan ta kalleshi.

“A nan garinmu ne Ya Maleek zan rayu cikin aminci da yardar Ubangijin Kaaba”

“Hakan ba zai gamsar da ni ba Nuwaira, sai na ga halin da zaki kasance kuma sai na yi magana da Sarkinku”

Cikin wata kalar murya mai kamar ta zaki Eid ya zabuwa Maleek har jijiyoyin dake jikinsa suna bayyana.

“Waye kai da zaka ce zaka ga sarki? Mutanen dake cikin fadar sarkin mu ba baka isa ka gani ba balle Sarkin da kansa, duk wani abun da ka yi ma Nuwaira kai da iyalinka mun gode zaka iya tafiya”

Eid ya hade hannun biyu yayi masa godiya har da sirinawa sannan ya nuna masa hanyar da suka fito.

“Ban taba tirjiya ko musayar yawu da kafewa akan abu daya ba sai yau, idan da tsafi kuke taka ni ina takama da wanda yake da ikon akan komai da kowa, and mark my words sai na yi magana da Sarkinku zan tafi sai na tabbatar Nuwaira tana cikin aminci, idan har zan iya barin wani abu ya same ni to zan iya barin Nuwaira ta cutu kenan”

Sai a lokacin yan rakisarsa suka saka baki domin sun lura a yanzu ya wuce gona da iri, su dai rakiya suka zo kuma sun kawo yarinyar a gidansu akan wace hujja zai nace dole sai ya shiga cikin garin.

“Am Malam Maleek ko? Akwai maganar da nake son yi da kai dan Allah dan zo ka ji”

Maleek baya son disga mutumen a cikin mutane hakan ya saka binsa gefe yana janye da hannun Nuwaira. A lokacin da suka koma gefen sai mutumen ya kasa cewa komai saboda ganin yana rike da hannun Nuwaira.

“Da ka dan sake ta sai mu yi magana”

Maleek ya kalleta ji yake kamar idan ya sake ta Eid ko wani daga cikin mutanen da suke tsaye bakin kofar garin zai iya yin tsafi ko kuma su ja Nuwaira da karfi su tafi da ita su bar shi a gurin.

“Zaka iya fadin maganarka”

Mutumen ta sake kallon Nuwaira sannan ya kalli Maleek.

“Wato ni abun da nake gani zai fi zame mana masalaha shi ne ka kyale yarinyar nan ta tafi gurin danginta, bukata dai a kawota gurinsu kuma gashi an yi, karka daukarka kanka abun da ba zaka iya ba, ni a yadda na fahimta shi wannan dan'uwanta ne ko kuma da dukan alamu ba shi da kyau hali”

“Haka ne office zaku iya tafiyarku daga nan, daman an dauko ku ne saboda ku rakomu ku tabbatar mun isa lafiya, ina ganin aikinku ya kare daga nan za su iya tafiya”

Office ya tsaya kallon Maleek baki sake da mamaki.
Chapter 148 · 0% Book details