Sashe 171
Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Kin auro yarinyar, ni da ke mutu ka raba talkamin kaza, kuma babu abun da za a fasa idan ma zaki daina wahalar da ni ki daina, tausayinki nake shiyasa kawai nake daga miki kafa, amman jiyan nan kika gama cika min baki akan kina son ki haifi yara da yawa”
“Na fasa haihuwar bana so”
Ta bata fuska sosai ita dai a bakin gaskiyar ba zata yarda da wasu dabi'u da hallaye da Maleek ya tsira mata ba tun bayan da aka daura aurensu abubuwan da kwakwalwarta suka kasa dauka.
“Ni da na san haka zaka zama ba zan yarda da auren ba, wannan abun Ummi ma idan ta ji sai ta yi masifa ai”
A take dariyar dake fuskarsa ta bace, ya hade mata fuska kamar be taba murmushi ba.
“Allah yasa idan muka je ki fada mata, ki ga yadda zan fasa bakinki ki jure stew din ki fito mu tafi”
Ya fice daga kitchen din, bacin ran da ta gani a fuskarsa ya saka ta ji babu dadi, har da yan hawayenta. Haka ta juye stew ta hade s7 guri daya a basket din ta dauko ta fito falo, sai ta same shi zaune yana rike da key. Mikewa yayi tsaye ya dauki basket din.
“Idan kin saka hijab dinki ki same ni a mota”
Ta bishi da kallo har ya fice, sai kawai ta ji bata bukatar yin komai sai kuka, ai ko fita zai yi janta yake har gurin motar yana rumgume da ita yana kissing dinta haka ma idan ya dawo, amman yau saboda ta ce ba zata yarda da wannan rashin imanin da yake son aikata mata ba sai yayi fushi. Kamar wata karamar yarinya haka ta shiga dakinta da komai na cikinsa fari ne tun daga kan Turkish furniture din har curtains, ta dauko hijabinta ta saka ta fito tana tafiya tana shura kafafuwanta har ta fito waje. Yana ganinta ta fito daga motar ya bude mata bangarenta, sannan ya iso garenta ya rumgumeta yana murmushi.
“Wannan fushin na minene?”
Sai ta fara kukan shagwaba kamar wata yar baby.
“Ba kai ne ba, daga kawai na ce ba zan yarda ka aikata min wannan rashin musuluncin ba sai ka yi fushi saboda ka san ina sonka sosai”
“Toh zaki yarda?”
Ta ki ce eh ko aa zuba masa kukan shagwaba take, irin shagwabar dake rikirkita namiji musamman wayaye wanda ya san me duniya take ciki. Kunnesa ya kai ya rada mata wata magana mai girma a kunneta a take ta daina kukan ta dago daga kirjinsa tana kallonsa sakaka, be yarda sun hada ido ba ya ja hannunta yana murmushi ya nufi motar da ita ya sakata a front seat ya rufe, ya zagaya dayan side din ya shiga ya murza key sai ta juyo tana kallonsa. Hannu ya mika ya kama hannunta ya kwanto da ita jikinsa ya fara tukin da hannu daya, sabon mai gadin na su ya bude masa gate yana daga masa hannu, Maleek yayi masa horn ya fice daga gidan. Sai da suka fara nisa sannan ya saki hannunta bude gurin da ya koyawa kansa aje sweet tun bayan aurensu ya dauko daya ya bude ya saka mata a baki, ya dauki daya ya sha.
“Laa ashe nan kake aje sweet din da kake shigowa da shi kullum?”
Ta san kullum idan zai dawo gida zai shigo yana shan sweet ne, idan ya kwatanta lokacin dawowarsa gida ko ya kama hanyar gidan sai ya bude ya saka a baki, bakinsa yayinta kamshi, wani sa'in shi da kansa zai bata ragowar idan yaje kissing dinta wani lokacin kuma da kanta take saka hannu a bakinsa ya ciro shi ta saka a bakinta, ranar da ya so su yi kurciya kuma sai ya hana mata har sai ta yi ta kokawa da shi har ta samu nasara ya karbe. Hannunsa ya kai yana taba bakinta kamin ya tura mata yatsana a baki ta cigaba da tsosa tare da sweet din dake cikin bakinta, cikin dabara ya zare minti tare da yatsansa yayi saurin jefawa bakinsa yana dariya.
“Ka shanye naka ne?”
Ta turo halshensa ya nuna mata duka mintin biyu da na shi da nata da ya karbe.
“Kin san gida fin karfi kike min ko? Sai ki danne ni ki karbe ko kuma idan muna kiss ki karbe min ko da ban yi niyar baki ba”
Ta mika masa bakinta.
“Toh ayi kiss din”
Ita a wayonta idan ya zo kissing dinta sai ta kwashe har nasa, sai da ya kalli titi da kyau sannan ya mika bakinsa ya mata kiss saman lips dinta be yarda ya shigar da bakinsa ba. Ya saka hannunsa ya lakaci hancinta.
“Anki ayi din ke sarkin wayo ko?”
Ta kyalkyale da dariya, shi ma dariyar yayi ya riko hannunta ya saka yatsunsa cikin nata ya cigaba da tukin da dayan hannunsa har suka isa gidan. Be fita motar ba sai da ya taune minti gaba daya ya hade domin be son ya shiga falon Ummi yana shan minti. Back seat ya bude ya dauko basket din abincin da Nuwaira ta girkawa Ummi for the first time in history, tana gaba yana bayanta suka shiga falo, a tsakar falon ta wulgar da talkaminta ta nufi stairs din da gudu tana marmarin ganin Ummi daman kullum sai ta yi masa maganar ya kawo ta amman ya ki sai dai ya kira mata ita a waya su gaisa, da gudu ta baki kofar dakin ta shiga Ummi dake kwance da Mahmood dake zaune yana matsa mata kafafuwanta suka kalli kofar ganin Nuwaira ce ya saka Ummi murmushi, Mahmood kuma ya ce.
“Sai ba ke ma”
Nuwaira na ganin yadda ciwo da rama suka samu muhalli a jikin Ummi sai ta fada jikinta ta fashe da kuka.
“Ya isa ya isa ba gani kin gani ba? Miye na kuka?”
“Ummi i miss you”
“I miss you too Baby Nuwaira, ya sabon gidanki”
“Babu dadi saboda babu ke a ciki Ummi”
“Zaki saba da sannu, mussamman idan kika gina naki iyalin”
A hankali Ummi take magana irin na masu ciwo yana shafa fuskar Nuwaira. Maleek ne ya shigo dakin ya aje basket din daga gefen gado Ummi ya zauna a kusa da matarsa yana kallon mahaifiyarsa zuciyarsa babu dadi.
“Maleek ya kake?”
“Lafiya kalau Ummi ya jikinki?”
“Alhamdulillah ina ta ibada”
“Allah ya baki lafiya”
“Ameen”
“Ga abinci nan Nuwaira ta girka miki”
Ummi ta dan daga kai ya kalli basket din tana murmushi irin na masu karfin hali.
“Tare kuka girka?”
Kamin ya bata amsa Nuwaira ta ce
“Ni kadai na girka Ummi saboda ke na yi, dan Allah ki ci”
“Zan ci mana dole na, Nuwaira ce yau ta girka abinci ta kawo min? Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani ikon ganin wannan ranar, Mahmood dauko plate da spoon na ci abincin yata”
Mahmood ya tashi ya fita tana murmushi, sai Ummi ta kama hannun Nuwaira ta kama na Maleek ta saka na Nuwaira ciki.
“Maleek ga Nuwaira na san an baka amanarta tun a ranar da aka daura muku aure, amman yau ina son na kara jadada maka Nuwaira bata da kowa a duniya sai ni da mahaifinka sai kuma kai da yan'uwanka, ita din amana ce a gurinmu, dan Allah karka cutar da ita, ka rike ta amana ka nuna mata soyayya da kauna kamar yadda ta nuna maka har burinka ya cika, karka yarda ta zubar da hawaye akan ka karka surfa mata bakinciki namiji, karka saka ta yi nadamar kasancewarta a cikin addinin nan karka saka ta ji kewata idan bana nan saboda wani mugun abu da zaka yi mata, ka je har garinsu ka ga gidansu da irin rayuwar da ta taso a cikin, yarinya ce da bata san gata ba, dan Allah Maleek ka zame mata gata rashin uwa da uba, karka yarda wani abu ya rabu sai mutuwa”
Maleek ya jinke hannun Nuwaira hawaye na sauko masa.
“Na miki alkawari matukar ina raye Nuwaira ba zata taba rashin wani abu ba, kuma ba zan taba cin amanarta ba, sannan na miki alkawari zan maye mata gurbin uwa da uba zan bata duk wani gata da ta rasa”
Ummi ta yi murmushi hawaye na sauka a idonta. Sannan ta dubi Nuwaira da tun da ta fara maganar take kuka.
“Nuwaira ki rike mijinki kinji? Karki yarda rudin shaidan ko duniya su saka ki juya masa baya, idan yace yana so ki fishi so, idan ya ce baya so ki fishi gujewa abun matukar ba sabon Allah ba ne, aljannar nan da kike jin ana yawan fada miki ta karkashin kafar mijinki ne, wannan hade hannun na ku da na yi ki rike shi har aljannah. Gobe zan koma asibiti kuma zamu tafi tare da Maleek da Namra da Ameer da Mahmood ban sani ba ko Allah zai amince min na dawo cikinku iyalina na sake wata rayuwar kuma ban sani ba ko mutuwata a kusa take, wannan dai wasiya ce nake bar miki ki rike addininki da kyau”
Cikin kuka Nuwaira ta ce.
“Ummi mi yasa ba za a tafi da ni ba?”
“Abiey ne yace be yarda Maleek ko Ameer su tafi da matan su ba, amman kar hakan ya saka ki ji komai a ranki kinji?”
Nuwaira ta daga kai ta kwantar da kanta jikin Ummi tana kuka. Mahmood dake tsaye jikin kofar rike da plate ya kasa shigowa kuka yake. Sai da ya ji motsin fitowar Maleek sannan ya bar jikin kofar kuma ya kasa sauka gaba daya. Maleek ya fito hawaye na masa zuba suna hada ido da Mahmood sai suka fashe da kuka marar sauti, Maleek ya rike karfen stairs din da karfi yana zubar da hawaye. Mahmood kuma ya ba shi baya shi ma yana hawayen. Sun dauki lokaci a haka kamin ya saka rigarsa ya share hawayensa ya koma dakin rike da plate din da spoon, har lokacin Nuwaira na jikin Ummi tana kuka Ummi na shafa bayanta tana murmushi. Mahmood ya aje plate din zai fara zubawa sai ta hana shi.
“No Allah ya maka albarka ya baka mata ta gari, amman bari Nuwaira ta zuba min da kanta”