← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 176

Sashe 48

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Karki ce min baki taba yin saurayi ba, or baki taba rike hannun namiji ba ko kissed even slept with him?”

“Subhanallahi Wallahi ban taba ko daya ba, ban taba saurayi ba balle har na kai ga aikata abun da kake tunani”

“So you're still Virgin? ”

Ta dauke idonta tana kallon wani gurin.

“You miss alot, babbar yarinya kamar ke? Baki da kawaye ne? Ina kika yi rayuwa?”

Ta bude motar.

“Ya kamata na tafi kar wani ya dawo be same ni a gidan ba”

Hannunsa ya mika ya juyo fuskarta ya matso da ta shi yana kallon bakinta sai ta juya ya sake juyawa da ita wannan karon gaf da ita yake, har tana shakar numfashinsa.

“Taya zan yarda baki taba kissed wani namiji ba?”

“Saboda ban taba yi ba, kuma ba zan yi karya ba”

“Can you swear?”

“Wallahi ban taba yi ba Ameer”

“Idan kuma kin taba yi kika min karya Allah ya halakaki kamin ki isa gida kin yarda?”

“Na yarda”

Tana rufe baki ya saka bakinsa cikin nata, abun ka da wanda be saba ba sai ta kasa komai har ya gama yawo da halshensa a bakinta ya cire, a nan kam tsoro ya bayyana a idonta sosai kamar yadda ya bayyana a jikinta take rawa har yana iya gani, wannan kadai ya isa ya yarda cewar bata taba tarayya da wani ba.

“Ki aje mana wannan sirrin, saka min number wayarki zan kira ki anjima amman zaki min wani alkawari a duk lokacin da na bukaci ganinki zan ganki?”

Ya dauko wayarsa ya mika mata, ta karba ta saka mashi number, sannan ta juya zata sauka ya sake riko hannunta.

“Baki min alkawari ba”

“Zan duba”

“Ba zan ce dubawa ba ne, zance ake na rayuwata i can not breathe when you're not near idan kuma kin fison na rika zuwa gidan ku kai tsaye then fine zan dauki ko wane risk just to see you Nimra...”

Kallonsa take, da gaske so take ta gane idan kalaman da suke fitowa a bakinsa har a zuciyarsa suke, miyasa zai sauya mata a iya yau kadai? Ya sumbace ya fada nata ba zai iya numfashi idan bata kusa ba, ya rika hannunta kuma yayi mata godiya da kawo masa sarewar da ta yi. Ganin irin kallon da take masa ya saka shi cewa.

“Na san fada muke, amman dukan abun da kika ba ni na karba na karba ne saboda na yarda dake, and now na bukaci ganinki kawai ba dan ina son sarewar ba, na san hakan kadai zan miki ki yarda mu hadu, zuciyata taan samawa kanta abun da take so ne Nimra ba tare da duba matsayi ko gaba ba”

Mutumen da ke ta rigima da ita ya ki yarda ba da hadin bakinta aka shirya masa komai ba, mutumen da girma kai kadai ya isa ya hana shi yin godiya a gareta. Da gaske abun da yake fada haka ne har zuciyarsa? Ta janye hannunta ta sauka a motar.

“Zamu rika haduwa wani gurin ba gidan mu ba”

“Okay take care of yourself”

Ta juyo ta kalleshi sai yayi mata murmushi, wata kalmar bata sake fitowa bakinta ya nufi motar da ta zo da ita ta bude ta shiga. Har ta yi ma motar key ta hau titi be bar gurin ba kuma be fasa kallonta ba har sai da ya daina hangota. Tana tukin tana tunanin yadda zuciyarsa ta karaya da wuri haka, ya yarda da ita kenan? Ta kai hannu ta taba bakinta amaimakon ta ji haushin abun da yayi mata domin bata taba aikatawa sai ta yi murmushi tana jin wani irin kimarsa na karuwa a idonta.

“Is this the sight of love?”

Ta tambaye kanta, domin wani irin yanayi take ji na dabam tun farkon haduwarta da shi har zuwa yau da wani abun ya shiga tsakaninsu? So ne ya saka take ganin abun da ba daidai ba a daidai har take iya karya dokar gidansu data mahaifinta? Take iya kyale wanda ba muharraminta ba ya rika hannunta har ya sumbance ta? Wata kila shi ma son ne ya saka shi saurin yarda da ita, daman ance wanda be taba yi ba idan ya fara masa baya masa da sauki. Kamar wanda aka yi ma albishir da yafiya haka Nimra ta wuni da farinciki da annashuwa a ranta ba ma kamar lokacin da ya kirata yana ta kashe ta da kalamai duk kuwa da be furta mata cewar yana sonta ba, gaba daya sai ta manta da wata damuwa ta tattara rayuwarta da duk wani tunani nata ta maida a gurin Ameer cikin wuni daya ta canja kamar ba ita ba. Tunanin yadda zata yi da iyayenta idan ta kulla alakar soyayya da Ameer sam be zo mata a rai ba a lokacin saboda farinciki ya dauke mata hankali.

AMEER POV.

Yana isa gida wanka ne abun da ya fara yi, ya wanke sarewar tas sannan ya zo gaban madubi yana kallon yadda Allah ya tsara halittarsa da mazantaka aka jera masa six pack kamar shi yayi kansa.

“Yaushe na yi arha haka, i kiss Nimra i hold her hands”

Shi kansa ba zai iya fadan yadda kyamarsa ta boye kanta har ya iya Sumbanta Nimra kai tsaye ba, duk kuwa da yanayinta da jikinta be nuna bata kula da kanta ba and the most abun da ya ja hankalinsa fada masa cewar bata taba yin kiss ba, ya kuma yarda domin ya lura da yanayinta macen da bata taba kebewa da namiji ba tana da banbanci da wacce ta saba yi ko ta taba, ita ce mace ta biyu da yawun bakinsa ya taba kaiwa a bakin wata bayan Angel, ita ma kuma Angel ribantarsa ta yi da tsabtarta da kuma aske gashin kanta da tayi kamar yadda ya bukata bayan ta daukar masa alkawarin tsare kanta, shi kuma shaidan ya rinjaye shi har ya saka rike kansa, a duk lokacin da bukatar hakan ga taso masa baya cilastawa kansa hakura da abun da yake ganin yana da iko da halin yinsa akan me zai cutar da kansa then?

Ya tsuke baki, tunanin daukar fansa da son lalata rayuwar kanwar makiyinsa ya mantar da shi wani abu kyama, wata kila kuma ita din bata da kazanta shiyasa be ji hakan a lokacin da yayi unkurin karya tarbiyar da iyayenta suka bata. And this fitinanniyar yarinyar ta ja hannunsa har cikin kazamin gidansu be mata komai ba. Ya tuna irin kalaman da kakarta ta yi masa cewar ita marainiya ce kuma ta dogara da abun da take samu a gurin aikin ne. Ya dan tabe baki zai kyale ta ne kawai saboda Kakarta da ta durkusa har kasa tana rokonsa ba dan haka ba sai ya koreta saboda ta masa tsiwa shi kuma baya son haka ya lura tana da zafin zuciya kamar shi. Tawul ya nufa ya dauka ya daura ya fada kan gado ya ya dauki wayarsa ya kira Nimra sai da ya fara tambayar ya ta isa gida da lafiyarta, sannan ya dora da wasu kalaman da zasu kashe mata jiki kuma ta yarda son ta yake ko da be furta ba.

UMMI POV.

Tana tsaye da mamaki take kallon matar dake goye da yaro a bayanta tana ta fada da Waira.

“Idan kika raba wannan auren ki yi yaya da ni? Ga yaya? Akan min zaki zo ki ce zaki shiga tsakanin masoya, a wace hujjar?”

Ganin Waira na kuka ta kasa cewa komai ya saka Ummi ta nufi matar ta fara bata hakuri.

“Dan Allah ki yi hakuri baiwar Allah bata sani ba ne”

Sai ta juyo ta yi kan Ummi da masifar.

“Ta sani mana, idan ta gani sai ta nuna? Haka kawai zan kyale ta? Hauka ake yi? Auren shekara da shekaru zata ce a rusa a rana daya? To ba zan dauki wannan ba, ni ina son mijina, yayanmu hudu da shi, ke ba auren kike ba da kike son shiga tsakanina da shi na aureshi tun da dadewa dan haka babu wanda ya isa ya raba wannan auren, ke da ake son a kashe ma komai ta dade sai sun kashe ki”

Jin matsifar ta yi yawa ya saka Ummi ta sake kallon babbar macen da zata yi sa'arta ta ce.

“Wai wayen wannan mijin na ki Baiwar Allah da kike ta wannan masifar?”

“Gashi can...”

Ta nuna bayan Ummi a tsawace tana zaro ido tsabar masifa, Ummi ta juya ta ga waye mijin kenan ta farka a firgice sakamakon taba ta da Mahmood yayi.

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un”

Ta fada tana mika sannan ta kalli Mahmood dake kallonta.

“Magana kike kina bachi lafiya?”

Juyawa ta yi ta karewa inda suke zaune kallo sai a yanzu ta yarda ba mafarki take ba, domin dan zaunawar da ta yi jiran a fito da Waira daga dakin hoto bachi mai nauyi ya dauke ta, kuma mafarki ya zo mata kamar a zahiri. Wacece wannan matar? Kuma waye mijin nata? Miyasa kuma take masifa da Waira shi ne abun da ya zo mata a rai.

“Are you okay ko kina jin wani ciwon ne?”

“Aa bana jin komai lafiyata kalau”

Ya sauke ajiyar zuciya domin ciwonta ne abun da ya fi damunsa a yanzu.

“Ummi har yanzu baki fada min yaushe ciwon nan ya sake ki ba, kuma me likitoci suka ce akai?”

Ta dubeshi.

“Ba nace wannan sirrinmu ba ne?”

“Ban fadawa kowa ba”

“Amman ka so ka yi maganar a gaban Namra ai, bana son kowa ya sani”

“Na ji, amman kina zuwa asibiti?”

“Na dade ban tafi ba, shakara biyu kenan da na gane cutar tana tare da ni”

“Amman Ummi kina shan magani? Kin san illar wannan cutar kuwa? Har kike cewa baki son kowa ya sani? Kin san abun da take janyowa”

“Likita ya min bayani, kuma yanzu zan duka da shan magani. Ina Waira?”

“Sun bata gado hoton ma daker ta yarda aka yi mata sai ihu take yarinyar bata da hankali”

Ummi ta mike tsaye tana tunanin mafarkin da ta yi wanda yayi kamanceceniya da abun da Waira ta yi a lokacin da ta so shiga dakin Maleek, suna tafiya Ummi ta juyo ta kalleshi.

“Kar dai ace aljana ta auri dan'uwanka Mahmood”
Chapter 48 · 0% Book details