← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 176

Sashe 110

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ameer ya bude ido yana murmushi.

“Mummy baki yarda ba kenan”

Kamin Mummy tace wani abu Fiyya ta fito da mayafinta.

“Zan bika mu tafi na ga gidan”

“Wa zai dawo da ke?”

“Yeah daman ina son naje da motata kuma gashi na zo da motar Ummi, so kija min motata zan shiga ta Ummi sai muje ki ga gidan, in ya so direba sai ya dawo da ita”

“Okay”

“Yeeeee Mummy sai na dawo”

Fiyya ta yi gaba abunta. Sai da Ameer ya shiga dakinsa ya dauko key din motar sannan ya fito ya bata key din shi kuma ya shiga motar Ummi. Waira ta juya ta kalli dan karamin akwaitin dake back seat ta kalli Ameer da ke juya kan motar ta ce.

“Sukenan kayan da zaka dauka daman?”

“Eh ai ba tufafi zan dauka ba, wasu abubuwan da nake son amfani da su zan dauka, idan mun je gida zan yi Order sabon tufafin da duk wani abu da zan yi amfanin da shi sai a kai min a can”

“Okay kana da kudi shiyasa amman kana aiki ko?”

“Aa bana aiki, ni zan zaman banza ne, shiyasa nake son zama a gurin Ummi saboda na samu kudin”

Ya fada yana murmushi da yafi kama da dariya saboda fitar sautin murmushin.

“Ummi zata baka mai yawa kuwa bata da rowa, tana da yawan kyauta”

“Haka addininmu ya koyar da mu....”

Muhimmanci kyauta da sadaka yayi ta fada mata, da kuma falalarsa har suka isa gidan Ummi. Kamin su shiga gidan gabanta ya soma faduwa tunawa da Maleek da ta yi. Horn yayi aka bude masa gate ya shiga ya faka a compound din gidan, Fiyya ta faka a gefensa tana karewa harabar gidan kallo daga cikin motar da take zaune. Maleek na zaune a one of set din kujerun da suke Entrance din rike da waya hannu, yana sanye da kananan kaya mug a center table. Kallo daya ya yi ma motarsu ya dauke ido be sake kallon inda suke ba, har iso gurin Ameer ya bude ma Waira kofar falon ta shiga tana matsar hannu kasa kasa take satar kallon Maleek har ta shiga, sannan shi ma ya shiga. Fiyya ta iso gurin tana kallon Maleek da be san ma da wanzuwarta a duniya ba, kallonsa kawai take har ta isa bakin kofar falon, kyaun nan nasa mai daukar hankali da kuma kamshin turarensa mai jan hankali ya hana ta wuce ba tare da mika masa gaisuwa ba.

“Sannu ina wuni”

Ya dago ya kalleta daga sama har kasa ba tare da amsa ba, ya maida kansa kasa ya cigaba da abun da yake. Ta dan bude ido.

“Shi kuma haka yake?”

Ta fada murya kasa kasa sannan ta tura kofar falon ta shiga da sallama Ummi ta dago tana amsa mata fuskarta da annashuwa.

“Lale marhabun da zuwa”

Ameer ya kalli Waira dake nunawa Ummi perfume din da Mummy ta bata ya ce.

“Waira kin san ma'anar Sallamu Alaikum da kuma Wa'alaikassalam?”

“Aa me yake nufi?”

“Peace be upon you, Wa'alaikussalam kuma peace be upon you too”

“To meyasa ake cewa haka?”

Ameer be amsa mata ba ya kalli Ummi ya ce.

“Ummi duk tsawon zaman da ta yi a gidan nan ne bata san komai akan addinin musulunci ba? Baki zaunar da ita kin fada mata matsayi da martaba ta addinin musulunci ba, da irin aminci da natsuwar da yake da shi?”

Kalmar Ummi da Ameer ya kira Ummi da ita tafi komai yi mata dadi, ba yau ne karon farko da ya taba kiran sunan ba, sai dai a yau ne ya fara kiran sunan cikin girmama sa karamci, ya kirata kai tsaye kamar yadda sauran yayanta suke kiranta sai kuma ya dora da bayanin abun da ya kara mata kaunarsa wato son addinin da kokarin ganin Waira ta koya.

“Ni uwace ina da abubuwa da yawa a gabana, shiyasa ban maida hankali akan haka ba”

“Cika uwa yana nufin kula da yaya har ta bangaren addininsu, nauyin Waira yana kanki a yanzu kamar yadda kika fada”

“Yana kam mu gaba daya”

Ta gyara masa zancensa na karshen, sannan ta kalli Fiyya ta ce.

“Ya Mamanki take?”

“Lafiya kalau, tace a gaisheki”

“Ina amsawa, Ameer na gyara maka dakinka da kaina, amman ban sani ba ko akwai abun da ba zai burgeka ba, zaka iya min magana a gyara”

“Bari na duba”

“Waira wuce ki kaishi dakin dake kusa da nawa”

Waira ta wuce gaba Ameer ya bi bayanta Fiyya ma ta rufa musu baya. Sun dauki lokaci a dakin yana duba abubuwa, be dauka sabon furniture Ummi zata zuba masa ba, amman ga mamakinsa sai ya ga har tawul da bathrobe duk sabin Ummi ta aje masa, hakan kuma ba karamin faranta ransa yayi ba. Ya sauko yana magana da Fiyya yayinda aka bar Waira a dakin tana kara duba wasu abubuwan.

“Ummi za a samu direban da zai kaita gida yanzu? Bana son na sake driving sai gobe idan zan fita duba Kakarsu Humairah daga nan na wuce office”

“Eh za a samu wanda zai kaita mana, drivers dai sun tafi gida yanzu amman Maleek ma zai iya sauketa”

Da gangan Ameer yayi murmushi saboda ya san waye Maleek ya san abun da yake soda kuma wanda baya so.

“Okay ki masa magana ya sauke ta, ga key din motarki na dauko tawa”

Ya mikawa Ummi sai ta karba cikin jindadi da farinciki marar misaltuwa. Sannan ta nufi wani karamin side table dake tsakanin kujerun falon ta dauki wayarta.

“Lemme call him”

Ta fara kiran Maleek tana fadar.

“Gobe tare zamu tafi na duba matar, sai na dawo kai kuma ka wuce gurin aikinka”

Ameer be ce mata komai ba, har Maleek ya amsa wayar.

“Hello”

“Maleek kana ina?”

Ta dayan bangaren Maleek ya juyawa ya kalli hagu da daman inda yake sannan ya amsa mata

“Entrance”

“Please zaka sauke...”

Ummi ta za last sentence din tana kallon Fiyya har sai da ta furta sunanta.

“Safiyya”

“Yauwa Safiyya gidansu”

Maleek yana daya daga cikin irin yaran nan da basa son musawa iyayensu wani umarni da suka musu, biyayya ce kawai zata saka ya yarda ya kai yarinyar gida domin ya gane wanda ta zo tare da Ameer Ummi take nufi, ba kuma dan ya san sunanta ba sai dan sanin ita kadaice bakuwa a gidan, wata kila ma Ameer ne zai saka Ummi ta bukaci ya kai yarinyar gida.

“Okay”

Ya amsa sannan ya sauke wayar zuciyarsa na mugun ƙuna, zafi kirjinsa yake masa ga bacin rai da be san na minene ba, ya busar da iskar bakinsa ya jingina jikin kujerar for some seconds sannan ya mike tsaye tare da mug din ya shiga falon, shigarsa ta yi daidai da saukowar Waira dake fadin.

“Dakin yayi kyau Ummi komai ya ji”

Kallon kawai yayi ya kawar da idonsa, yana kokarin danne abun da yake ji na bacin rai a zuciyarsa, to me zai saka ma ya damu bayan ya san ya daukarwa kansa alkawari ba zai sake damuwa da duk wani abu da zai shiga tsakaninta da Ameer ba.

“Lemme get my keys ta jira ni waje”

Yana fadar hakan ya nufi stairs, Ummi ta kalli Fiyya tana murmushi ta ce.

“Ki jira shi a waje zai zo ya kai ki yanzu nan”

“Toh na gode, sai da safenku”

Ta musu sallama ta fice, Ameer ya haur sama ya shiga dakinsa domin yin wanka, Waira kuma ta zauna a kusa da Ummi ta aje wayarta tana kallon Ummi wanda ta nufi kitchen. Maleek be dade ba ya sauko rike da keys din a lokacin Waira ce kawai zaune a falon tana ganinsa ta sha jinin jikinta ta sauke kai kasa. Yana saukowa gabanta na faduwa har ya iso inda take zaune, tsayawa yayi yana kallonta har ya bude baki yayi magana sai wata zuciyar ta tuna masa da alkawarin da ya dauka. Jin yana tsaye a kanta ya saka ta dago kanta ta kalleshi da idanuwanta masu daukar hankali, raunin dake cikin idonta ya baibaiye fuskarta ya dira zuciyar Maleek a madadin ya ji haushinta sai tausayinta ya dirar masa.

“Oh Ya Rabbi”

Kawai tausayinta yake, zuciyarta ta kasa natsuwa da alakar dake shiga tsakaninta da Ameer, ta dayan bangaren kuma yana jin damuwa ganinta da Ameer. Numfashi yaja ya sauke da karfi sannan ya dauke kai ya fice daga falon.
[7/18, 10:14 PM] My S Line: 57

Da hannu yayi ma Fiyya alama da ta shiga motar da yake nufota, sai ta isa gurin taja ta tsaya kwarjininsa na cikata, har sai da ya shiga motar sannan ta bude ta shiga. Ta natsu sosai fiye da yadda ta saba natsuwa idan tana tafiya da mutumen da bata sani ba, kwararran motsi sai ta kasa yi, tana son ya juya ta kalli inda yake ta kasa, daga ita har shi hankalinsu yana gurin titi har ya isa bakin gate din gidan. Son ya tabbatar ta sauka lafiya ya saka shi yin horn aka bude masa gate ya shiga har ciki ya faka motar harabar dake kusa da kofar falon, sai a lokacin ta samu damar kallonsa shi ma kuma saboda ta yi masa godiya ne.

“Thank you”

Be kawota arajin kansa ba, dan haka ba godiyarsa ce abun da yake bukata a gurinta ba a yanzu. Ko kallon inda take be yi ba balle ma ya amsa tana fita motar yayi gaba a makeken compound din gidan ya juya motarsa ya fice. Da gangan ya yi ta tafiyar da zata dauke shi lokaci be dawo gida ba, and he don't know why. Bayan kusan awa daya da rabi a titi finally ya iso bakin gate din gidansu yayi horn masu gadi suka bude masa gate. To his surprise sai ya samu Abiey tsaye yana lasa wayarsa hannunsa. Maleek na fakawa ya bude motar ya fito yana matsa key din hannunsa ya nufi gurin mahaifinsa.

“Abiey lafiya?”

Abiey ya dago ya kalleshi a karo na biyu bayan kallon da yayi masa a lokacin da yake shigowa cikin gidan.

“Me ka gani?”

“Kawai dai na ga kamar ba lafiya ba, fuskarka ta nuna akwai damuwa”

Abiey yaja dogon numfashi ya sauke.

“Damuwar gidan nan ba zata wuce ta mahaifiyarku ba...”
Chapter 110 · 0% Book details