← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 176

Sashe 117

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ummi ta ya za'a ce bata iya ruwa ba? Ruwan ba mai yawa ba kamar na gidan nan? Kuma idan har taimaka mata zai yi ai hannu ya kamata ya mika mata ta riko ya fito da ita ba wai su shiga ruwan ba?”

Ummi ta mike tsaye ta nufo inda suke tsaye.

“Ameer Waira ba a gidan ta tashi ba, ba lallai ne ace ta iya kalar rayuwar da kuka ba, zuwanta gidan nan ma if i can remember ko ruwa bata son ya taba jikinta, maybe shi ya saka bata iya ruwa ba”

“I hope so”

Ya fada sannan ya dauke kansa ya nufi stairs sai kuma ya juyo ya kalli Waira dake takowa a hankali.

“I'm sorry, let me go get my phone”

Kallonsa kawai ta yi ta sauke idonta kasa shi ya nufi kofar fita Waira kuma ta nufi stairs...

*** *** ***

Tun daga Ranar sai Ameer ya daukarwa kansa wani duty, kullum shi zai kai Waira School ya dawo da ita, hw use that opportunity yayi ta fada mata abubuwan da bata sani ba akan addinin musulumci, idan sun dawo kuma yayi ta dora mata da abubuwan da ya sani kasancewar mai yi mata lesson ya daina zuwa a yanzu, sai ya zamana da yamma bata aikin komai sai sauraren Ameer dake karantar da ita yana mata searching din wasu abubuwa, sannu sannu har ta kai Waira zata dauki remote da kanta ta kama peace tv ta zauna tana kallon program din da ake, idan kuma ta dauki wayar Ummi ko Ameer ta shiga ta tana kallon abubuwa, wani zubin kuma game take da wayar. A dan zaman da Ameer yayi a gidan na wata biyu da kwana goma sha uku shakuwa da kyakkyawar alaka mai karfi ta kara shiga tsakaninsa da Waira, idan bata cikin gidan har bata jindadi, ta kan dauke masa kai ne kawai idan Maleek yana zaune a inda suke zaune, kamar falo ko dinning, shi kan shi ya lura bata sakewa idan Maleek na gurin duk yadda yake mata magana ko ya tsokane ta iyakacinta murmushi. Duk tsawon lokacin nan babu daren da Maleek baya shigo dakinta Either ya rumgume ta ko kuma ta taba jikinta, tun abun na damuwarta har ta soma sabawa, some times zata jira ma har sai ya shigo ya fita sannan ta kwanta, domin bata jin ta jindadin sai ta yi bachi ya tasheta, a tsawon lokacin da yake shigo dakinta be taba ce mata komai ba, sai dai kamin ta saba ta gwada buge masa hannu da fada masa bata so, sai dai ganin ba zai daina ba ya saka dole ta hakura. A tsawon lokacin ta kame baki bata fadawa kowa ba, no matter how ta yi unkurin fadar sai ta kasa, some times tana tunanin Maleek yana mata haka ne saboda ya hurar da ita saboda biyewa Ameer da take shi kuma baya son haka domin kullum cikin yi mata gargadi yake, ta hanyar fada mata da baki ko kuma da ido.

Today is Sunday Waira na zaune gefen Ummi rumgume da baby Rabbit dinta sai shafa shi take tana wasa da kunnensa, Ummi kuma hankalinta yana gurin wayar da take da yar'uwarta Maryam.

“Ni dai ina tunanin kamar bata hakuri ba ne, shiyasa ta ce bata bukatar komai, ko abinci aka kai mata na lura indai daga gurina aka tafi da shi haka za a dawo da shi bata taba ba, idan kuma naje dubata da zarar mun gaisa na yi mata ya jiki ta amsa ba zata sake cewa komai ba, amsawar ma kamar an mata dole haka zata ta yi, sannan duk lokacin da Ameer ya dawo indai ya fara zuwa gidanta sannan ya dawo gidan nan ina ganin canji a fuskarsa”

“Zahra kin fi kowa san wacece Hajiya, tun kamin ki auri Deen har kika aure bayan rasuwar da auren da kika yi babu abun da baki gani ba na halinta. Dan haka ki saka mata ido a yanzu ki bita a yadda take son tafiya”

Ummi ta mike tsaye tana sauke ajiyar zuciya.

“Ina burin kyautatawa kowa Ya Maryam, ina son na kyautata mata, na san shi Baba ba zan iya samun yafiyarsa ba, amman ita ai tana raye yafiyarta nake son na nema a yanzu, ba zan iya da hakkin mutane da yawa ba”

“Idan kina son neman yafiyarta sai ki bi ta hanyar ďanki Ameer mana, tun da shi kun samu kyakkyawar fahimta da shi”

“Bana son na saka shi cikin matsala ta ne, burina kawai na kyautata mata irin kyautatawar da zata mantar da ita abun da na yi mata har ta furta cewar ta yafe min, amman ta ki ba ni wannan damar, yanzu kin ga sallamarta za ayi a asibiti na ce zan ba su gurin da za su zauna mai kyau, saboda Ameer ya fada min inda suke zaune ba shi da kyau kuma akwai mutane da yawa a gidan amman ta tsaya kai da fata ita bata bukatar komai daga gareni, dauren min fuska da take ma abun yana damuna sosai”

“Daman ba zai yiyu ta saurareki cikin kankanen lokaci kuma ya fahimce ki ba, dole na sai kin bata lokaci kuma kin yi hakuri, ki kwantar da hankalinki Zahra ke dai kina aikata hakan ne da zuciya daya, dan haka ki yi hakuri kuma kar hakan ya saka ki fasa kyautata musu, ai ita ma idan zata yi adalci kin yi musu duk yadda ake yi, kuma girma ya kama yanzu, ta san kuma karfi ba daya ba, ba zata iya ja dake ba idan ma ta ce zata yi shari'a ne, kuma silar wannan abun ba gashi Mr Bashir ya dauke mata nauyin komai ba? Wannan ma kawai jindadinta ne, dan Allah karki saka damuwa a ranki kin san dai yadda jikinki yake”

Ummi ta sauke ajiyar zuciya, zata sake maganar Waira ta mike tsaye tana fadin.

“Ummi assignment din ba'ayi min ba, kuma gobe school za su min fada idan ba ayi ba”

Ummi ta rage murya.

“Dauki assignment din ki tafi falo duk wanda kika tarar ki ce yayi miki assignment din”

“Toh”

Ta amsa sannan ta nufi kofar fita ta bar Ummi tana ta wayarta, tana fita dakin Namra ta shigo rike da waya a hannunta, can one seater ta zauna tana kallon Ummi dake waya.
Waira dakinta ta shiga ta dauko jakarta ta bude ta dauko littafin da aka bata assignment din ta dauki pen ta sauko kasa. Maleek ta tarar zaune a kasan carpet, ya rufe ko ina na jikinsa da jacket, kafarsa ma sanye da safa kansa ma na sanye da jar hular sanyi. Tea mai zafi na gabansa da kananan cincin a plate ya maida hankalinsa gurin Plasma dake kunne yana kallon wani documentary da ake a Al Jazeera. Zuwa ta yi ta tsaya kansa sai kuma ta ga kamar hakan be dace ba, a kokarin na yi tarbiyar da Ummi take dorata ta zauna gefensa tana kallon yadda dress din yayi masa kyau.

“Ya Maleek ga assignment da aka bani a school sun ce gobe za a kawo”

Juyowa yayi ya watsa mata wani banza kallo ya dauke kai. Bata damu ba ta fara bude littafin tana nuna masa.

“Ni kika maida kafiri kenan? Idan karatun Allah ne sai dai ki samu Ameer, yanzu kuma da yake na boko sai kika kawo min ga dan iska da duniya ko?”

Salon magana da yayi ya bude mata babi da ta yi masa fahimta ta dabam.

“Ni ban ce kai dan iska ba ne, iska ai ba shi da ďa, duniya ma bata da ďa”

Ya watsa mata harara ya dauke kai.

“Aka ce miki ni jahili ban san komai a addinin ba”

“Baka taba fada min ba, shi ma da farko ba tambayarsa na yi ba, shi yake fada min yanzu kuma da nake jin dadi shiyasa nake tambaya”

Ya kalleta ya dauke ido, ganin kamar ba zai mata ba ya saka ta mike tsaye tare da zomonta da littafin.

“Ummi ce ta ce idan na sauko duk wanda na gani na bashi assignment din yayi min”

Banza yayi mata har sai da ta fara taka stairs sannan ya kira sunanta.

“Waira”

Hausawa suka ce mai nema dole a biye yake, haka ta juyo ta dawo ta zauna a gabansa. Sai ya karbi littafin ya bude har ya kai gurin assignment din, ita dai kallonsa kawai take tana yana ta mata solving math, ta saka hannayenta ta rumgume jikinta saboda sanyin da ake a waje ga kuma na Ac da tun da ta zo gidan bata san wata rana da aka taba kashe shi ba, gwara ma daki akan rage ko a kashe amman a falo ba a taba shi komai sanyi komai zafi ko damina. Sai da ya gama solving din sannan ya cire jacket din dake ya rufa mata saman jiki, ya cire hular kansa ya mika mata, sai ta karba sannan ta karasa saka jacket din ta saka hular.

“Ki daina zama haka kina jin sanyi”

Murmushi ya bayyana a fuskarta ta kalli kanta tana fuskarta na kara fadada da annshuwa kallo daya zaka yi mata ka fahimci jindadin dake ranta na karramata da Maleek yayi ya bata rigarsa da hularsa saboda tana jin sanyi. Hannu biyu ta saka ta dauki tea cup din dake gabansa ta rike da hannu ta sha. Ya kalleta duba irin na mai rauni ta tarin damuwa a zuciya, ta sakar masa dara daran idonta tana murmushin ta ya fadar masa da gaba.

“Sanyi nake ji, kadan na sha”

Ta fada sannan ta aje cup din ta dauki cincin daya ta ci.

“Thank you Ya Maleek”

Kallonta kawai yake ya kasa cewa komai har ta mike tsaye ta dauki notebook din ta nufi stairs tana shinshina rigar dake ta kamshin turarenta, yau dai kam Maleek ya faranta mata rai. Dakinta ta shiga ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta sai dariya yake kamar sabuwar mahaukaciya, ranta fes ta farinciki kamar wadda aka yi ma gafara.

AMEER POV.

Ya kai hannu ya shafa fuskarsa yana kallon titin da motocin dake gabansa.

“Ina son idan Hajiya ta koma gida, zan yi magana da Daddy”

“Akan me?”
Chapter 117 · 0% Book details