← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 176

Sashe 162

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bar shi tsaye ya tura kofar falon, shi kam mamaki ne ya kama shi daman Namra ta iya sa'ido haka, da ma Nimra ce ta yi masa wannan maganar ba zai yi mamaki ba amman dai ita kam abun mamaki ne sosai a gurinsa. And she's right shi ma ya sam haka, ba tabbatar da yayi ma kansa babban gibi ba sai da ya bar kasar tare da Ummi da Abiey domin fita jinyarta, a lokacin ne ya gane ya kunna nawa kansa wutar kunar kansa da kansa, Kaunar Nuwaira ta azzara a ransa, ba shi da ikon kebewa shi kadai sai ya fara tunaninta idan kuma ya tambaya lafiyarta ko yayi waya da ita sai ya ji kamar an masa kyautar duniya. Sai dai ya san ba zai iya yin komai a kai ba domin ya riga ga sadaukar da kaunarsa ga dan'uwansa da kuma mahaifiyarsa, can da be dauka yana sonta ba sai a da yayi nisa da ita, a lokacin ne ya gane yana bukatar ganin kasansa a kusa da ita.

Da sallama ya shiga falon bayan ya tura kofar, Ameer da Abiey da Mahmood da tun da Abiey ya dawo yake bangarensa suka amsa masa, sai ya zauna a kusa da yar'uwarsa Namra, sai a lokacin gabansa ya soma faduwa domin ya ga yanayin damuwa a fuskarta Abiey, ko da yake kusan kullum haka Abiey yake tun da suka bar kasar yar hirar uba da ďa ma da suke da tsokanarsa da Abiey yake duk ya daina gaba daya hankalinsa da tunaninsa ya tattara ya koma gurin Ummi, shiyasa ya aje komai na sa ya bi matarsa zuwa asibitin da suke kyautata zaton zata fi samun kulawa, kusan kullum yana tare da ita idan ya bar asibitin sai idan zai je yayi wanka ko wani abun, yadda yake nuna mata kauna da kulawa sai ka rantse kananan masoya ne ba wadanda girma ya kama har suka yi yaya ba, domin shi ma ya rame sosai saboda tunani kamar a tare suke ciwo. Abiey ya sauke ajiyar zuciya ya gyara zamansa ya kalli Ameer sai kuma ya kalli Namra ya maida dubansa fa Mahmood sai kuma ya sauke kansa kasa.

“Abiey lafiya? Ko wani abu ya faru da Ummi”

Ameer ya tambaya gabansa na mugun bugawa da karfi, domin be natsu da damuwar da ya gani a fuskar Abiey ba. Abiey ya dago ya kalleshi cikin karfi hali irin na magidanci mai iyali.

“Wata magana ce da ya kamata na fada muku, kuma na yi muku nasiha na jan kunnenku daga karshe kuma na baku shawara. Maleek ya sani already kai da Namra ne da Mahmood ba ku sani ba”

Jin haka hankalin Ameer da Mahmood da kuma Namra ya tashi, Maleek ya saka hannu biyu ya rike kansa domin ya fahimci abun da Abiey zai fada, kalmar da baya son shi kalmar da tun a lokacin da likitoci suka fada musu haka hankalinsa ya tashi kuma ya rasa natsuwarsa.

“As you all know saboda neman lafiyar Ummi muka bar kasar nan, kuma muka nufi asibitin da duk duniya an yarda asibiti ce mai kyau dake duba marasa lafiya na cancer, tun kamin mu bar kasar nan daman likitoci sun nuna mana yana da kyau mu yi saurin kaita waje shiyasa within a week muka tafi tare da Maleek kusan shi ya jagoranci komai a can, Alhamdulillah jikin da sauki ta wani bangare kamar yadda duk suka gani kasancewarsa kuna video call da ita kuma kuna waya”

Yayi shiru tare da jan dogon numfashi ya sauke.

“Amman akwai abun da likitocin da suka duba ta a can suka fada mana, wanda ni da Maleek muka bar maganar a tsakaninmu muka yi shiru da bakinki saboda kar a tashi hankalinku musamman ma Ameer da take yawan magana, kana cikin ranta sosai Ameer”

Ameer da idonsa ya cika da hawaye har suka fara zuba yana kallon Abiey ya ce.

“Idan ma mutuwa ta yi ka fada min ban isa na hana Allah ikonsa ba, ni ma ban isa na tare mutuwa ta ba balle na tarewa wani”

“Bata mutu ba, jiya ma ai ka yi waya da ita da ta mutu ai da ba zaka gan ni a nan ba, amman dai likitocin sun tabbatar mana cewar Mahaifiyarka ba zata wuce wata biyar a duniya ba, domin tana 1 percent a yanzu, kuma last checking din da suka mata ciwon ya taba lungs spinal and liver dinta, infection din yayi mata over bata wuni bata yi tarin jini ba, she's feeling very weak ga yawan bachi numfashinta ma ya canja loss of bladder and bowel and unconsciousness...”

Namra ta fashe da kuka sosai jikinta har rawa yake, Ameer kuma ya rumtse idonsa sosai yana jin duniyar gaba daya ta juye masa, ina ma Abiey be fada masa haka ba, sai a yanzu ya gane dalilin da ya saka a duk lokacin da yayi unkurin zuwa sai ya dakatar da shi da cewar ya jira har su dawo, Mahmood ya saka hannu biyu ya rufe fuskarsa yana hawaye shi kam daman ya dade da katsewa tun a lokacin da ya ga gashin kanta na cirewa. Maleek ma hawaye ne ke masa zuba amman hakan be hana shi kwantar da kan Namra a kafadarsa ba yana jijjigata alamar rarrashi.

“Idan na rasa Ummi na shiga uku na rasa yar'uwa yanzu kuma zan rasa uwa wayyo”

Ameer ya dago ya kalleta hawaye na masa zuba kamar ba gobe.

“Ba ke kika shiga uku ba, ni na shiga uku domin ni na rasa kowa, na gane cewar ita ce mahaifiyata a kuraren lokaci a kuraren lokaci, komai ya canja min abubuwan da ban zata sun faru da ni ta hanyar da ban yi tsammani ba, you guys are lucky kun rayu da ita tun tashinku har girma, tun kuna jarirai har kuka girma kun san in and out na ta, ta kula da ku tarbiyarta da kulawarta ce kuke kai, kun yi babbar sa'a ni ban samu wannan ba, a yanzu da ya kamata na rabe ta mu san juna ta nuna min kauna na nuna mata kuma mutuwa na shirin yanke alaka...!”

“Haka take yawan fada, cewar ita kadai ta rage maka kuma zata tafi ta barka”

Abiey ya fada sai kallon Ameer yake cike da tausayinsa.

“Ina tunanin zan yi duk abun da ya kamata na bar kasar nan gobe, daman kullum ina son tafiya sai ka ce na jira sai ka dawo da na san abun da zaka dawo ka fada min kenan da ban jiraka ba”

Cewar Ameer yana jin zuciyarsa kamar zata fado saboda bakinciki.

“Ba tafiyar ce mai muhimmanci ma, cika mata burinta na son ganin aurenku ne mai himmanci, shi ne dalilin tara ku a nan da na yi, daga ke Namra har Maleek balle kuma Ameer har kai Mahmood dan Allah idan akwai wadanda kuke so ku gabatar mana da su ayi abun da ya kamata cikin lokaci, farincikin nan da take bukata ku saka mata shi, Ameer idan har zaka tafi gurinta to kaje mata da wannan albishir din na gabatar mata da aurenka cikin kankanen lokaci, Namra ke kuma ki yi magana da Shuraim ki fada masa gaskiya idan ya shirya ina son aurar da ki kasa da wata biyu, daman na san shi ni kawai yake jiran na ba shi umarni, toh ki fada masa ya turo da magabantansa”

Abiey ya saka yatsunsa ya tare hawayensa ya jefar, ya maida dubansa gurin Maleek da Mahmood.

“Maleek na san babu yarinyar da kake so a yanzu ba, amman please try ka samu yarinyar da ta kwanta maka a rai kuma ka ji ka natsu da ita ba ko da kadan ne, yar gidan mutunci Mahmood kai ma haka inda hali, Ameer na san ba shi da matsala zan yi magana da Nuwaira matukar ta amsa tana sonsa za ayi komai cikin sauki, ina son hade aurenku ne if possible, kuma ina fatar zan samu goyon baya da hadin kanku”

Duk suka yi shiru sai Maleek ne kawai ya iya magana.

“In Shaa Allah Abiey, Ummi ba zata mutu a yanzu ba, babu wanda ya san mutuwar wani sai Allah kuma sau da dama akan samu irin haka amman sai ka ga Allah ya arawa mutum rayuwa ya rayu fiye da yadda ake tsammani, kuma da yardar Allah Ummi har yayanmu sai ta gani”

“Haka ne, amman kai ma likita ne kasan duk abun da yake nan, so try your best please make her happy”

“I will”

Ameer ya mike tsaye ba tare da yace komai ba ya fice daga falon. Kai tsaye gurin motarsa ya nufa, sai da ya shiga sai kuma ya ji ba zai iya tukin ba. Sai kawai ya kifa kansa a ya rufe ido, wayarsa ya dauka sai kuma ya tuna ba shi da hotonta ko daya a wayarsa, wanda take ita kadai ma balle kuma ace wanda suka dauka tare. Fasa shiga Gallary yayi sai yayi dialing number Daddy, wayar na daf da katsewa Daddy yayi picking.

“Assalamu Alaikum”

“Daddy kana da gida?”

“Aa ina Villa akwai meeting din da muka fito yanzu tare da vice president me ya faru?”

“Daddy i need to see you”

“Daman gida zan je daga nan, kana ina kai?”

“Gidan Ummi”

“Ka same ni gida yanzu nan”

“Okay”

Yana aje wayar ya kunna motar ya fice daga gidan, tafiyar minti arba'in yayi ta cikin minti ashirin da biyar saboda gudun da yayi. A haka din ma sai da yayi jiran one hour a harabar gidan domin kasa shiga ciki yayi, gaba daya duniyar ta fice masa a rai ji yake kamar ya mutu ya mutu. Sai da ya ga motar Daddy ta kunno kai cikin gidan sannan ya bude motarsa ya fito yana kallon motar har Direban Daddy yayi parking ya budewa Daddy, Ameer be tsaya jiran Daddy ta iso inda yake ba ya nufe shi da sauri ya rumgume shi yana hawaye.

“You're my only love Daddy, kai kadai ka rage min a yanzu a duniya, i have one no one now”

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”
Chapter 162 · 0% Book details