← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 169 OF 176

Sashe 169

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya furta mata yana jin kamar ace tana kusa da shi yayi mata chakulkuli, a yanzu ya gane hikimar Mama wato Hajiya Maryam yayar Ummi na dauke Nuwaira daga gidan tare da Namra saboda yi musu duty da ya kamata ace Ummi ce zata yi, tun bayan dawowarta daga ganin Ummi ta mayarda Nuwaira da Namra Kano tare da ita gidan ya zama daga shi sai Mahmood. Duk a gurin mijinta Abiey da amininsa Sauban suka nema masa auren Nuwaira, kasancewar in months din ne Sauban ya dawo mahaifarsa da zama wato Kano, bayan kwashee shekara talatin a kasashen turawa saboda yanayin aikinsa, da kuma kasuwancin da ya yake gudanarwa. Yaya Maryam ta yi hakan ne ganin Ummi bata ma kasar kusan ita ta dauke dawainiyarsu da komai duk wani shirye shirye na Maleek ko Ameer da ya kamata Ummi ta yi ita ce take shiga ta fanshi Ummi musamman bangaren Maleek domin Ameer yana da da wasu iyayen da suke shigewa gaba ayi komai. Ita take kula da Nuwaira da Namra, kudi mai yawa Abiey ya zuba mata take siyayyyar kayan kitchen da wasu abubuwan kawata daki. Komai biyu take siya na Nuwaira da Namra duk kuws da ta san Nuwaira bata iya komai ba kuma bata san wasu abubuwan ba, hakan ya saka ta dage wajen ganin ta iya wasu kananan abubuwa manyan kam sai idan an sakata a catering school ko kuma an samu kwarariya mai juriya ta koya mata. Duk wani abu da Nuwaira ta gani sai ta tambaya ya ake amfani da wannan minene shi, hakan yana yawan tunawa Yaya Maryam da kanwarta Zahra a lokacin da take yan mata, sai dai ta ibda ta banbanta da Nuwaira ita har so take a sakata aiki jiki na rawa take yi, domin aikin burgeta yake, sabanin Zahra a lokacin kurciyarta kiriniya be barta ta koya ba kuma gashi bata son aiki, bata aikin kowa sai na gidan Ammy mahaifiyar Abiey shi ma saboda neman suna da kwadayi irin na kurciya. Banbancin Ummi da Yaya Maryam wadda Nuwaira take kiranta da Mama saboda yayanta da suke kiranta da Mama kadan ne a gurin Nuwaira. Ummi ta fita jan ta a jiki da kula da ita sosai, ita kuma bata da sake fuska kamar Umminta kuma ba komai take yi ma Nuwaira ba wani abun idan Nuwaira tana so sai da ta ce taje ta yi, girkin gidan ma da yake ba wani girki ba wani lokacin Nuwaira zata ce ta dora daga baya sai ta karasa ko kuma ta dora Nuwaira ta karasa tana nuna mata yadda zata zuba komai. Suna yawan hirar Ummi da ita tana ba su labarin abubuwan da Ummi ta yi wani abun su yi dariya wani kuma su ji tausayinta musamman a yanzu da halin ciwo ya hanata zama cikin gidan mijinta ta kula da komai yadda ya kamata.

Kusan rana daya aka saka auren Ameer da kanensa uku mata yayan Mommy, Daddy da kansa ya roki a bar daurin auren Humairah a Abuja kasancewar a nan take tare da mahaifiyarta kuma mahaifinta ma a nan ya rasu haka kuma yana son hade aurenta da na yayansa kamar yadda ya hade siyayyen kayan dakinta da komai tare da na yayansa. Babu wata wata suka amince daman ta ina babban mutum kamar Mr Bashir zai nemi bukata a gurinsu su ce masa aa ko da kuwa be yi musu komai ba balle yayi musu goma ta arziki gashi bayan ya dauke musu komai na auren.
Ta bangaren Abiey ma rana daya aka saka aurensu da Namra da Maleek domin Abiey ya gama magana da iyayen Shuraim tun a farkon dawowar da yayi, sun tambaya kuma an basu, sai aka saka ranar daurin auren daya gurin dauren auren ma daya gurin liyafar cin ne kawai aka banbanta kowa ya zabi inda yake son yayi nasa, Maleek da Ameer suka zabi place daya kasancewar friends dinsu ma kusan daya ne, kuma su din ma yan'uwa ne. Ana sauran Sati daya da fara shirye shiryen Yaya Maryam ta dawo Abuja gidan Ummi ta tare da zama, kasancewar anan za'ayi komai, ba yayanta kadai ba ita kanta yar'uwarta sai da ta ji gidan yayi mata wani iri saboda rashin Ummi, duk wani abun da za'ayi sai dai a sanar mata a waya wani abun kuma a dauki hoto ko video a tura mata. Hakan kuma ba karamin tashin hankalin Ummi yayi ba ta ji tana kewar iyalinta fiye da ko yaushe tana mamarin kowa. Damuwar da ta nuna ne ya saka Abiey ya yarda ta dawo gida duk kuwa da kasancewar likitoci ba su so haka ba kuma sun yi ta bashi shawarwari akan ciwon da kuma dawowar da zai yi da ita, sai dai be nuna musu gida zai je ya zauna da ita ba, sai ya nuna musu wata asibitin zai kaita dake India.
Haka suka dawo Nigeria babu wani canji a jikinta na kamin su tafi da kuma bayan tafiyarsu, ciwon yana nan yanayin jikinta na yana nan a yadda yake sai mai wasu abubuwa da suka karu. Hankalin Abiey ya tashi sosai irin tashin hankali da ko a lokacin da da Mai Martaba ya bar duniya be ji irin wannan tashin hankalin ba. Wani abun mamaki ganin iyalinta cikin farin ciki ya saka ta jindadi da farinciki a ranta musamman ma idan ta tuna aure ne za'ayi babu wanda za a bari a gidan sai Mahmood da har yanzu be gama ruwan idonsa ba. Haka dai aka yi ta hidimar bikin sai dai ciwon Ummi ya hanasu farinciki yadda ya kamata, ba ma kamar Ameer da tun da ta dawo kullum yana gidan sai idan zata yi magana da mutane ko kuma mata sun cika gidan yake fita, sai kuma idan Nuwara na tare da ita, domin duk son kasancewa kusa da Ummi da yake ba ya zama daki daya da Nuwaira iyakarsa da ita ta gaishe shi ya amsa kallonta ma wani lokacin sai ya ki yi, irin wasa da shakuwa dake tsakaninsu a baya yanzu duk ya zubar har daure mata fuska yake dan kar ta ga damarsa. Ita taba ganganci gwada yi masa wasa ko zama kusa da shi ba, tun a lokacin da yayi mata bankwana gaisuwar da take masa ma saboda Ummi da Yaya Maryam sun ce ta rika gaishe shi ne domin su din ba abokan gaba ba ne.

Ranar laraba aka fara gudanar da shagulgulam auren a event center daya, tun farkon fitar pre-wedding pictures mutane suka fara maganar auren mata shida maza shida, musamman ma yadda suka sha kyau da tufafi masu burgewa. Kowa da yanayin yadda yayi nasa hoton sai dai babu wadanda aka fi yabawa kamar Maleek da Nuwaira domin su ne kadai suka yi hoto ba tare da taba juna ba, Maleek ko hannun Nuwaira be yarda ya rike ba, gashi sun wanku fess kamar wasu labaraba musamnan a inda take saka lifaya da inda suke tsayuwa gurin doki shi da kuma gurin da ya saka alkibba ita ma ta saka sai kuma girin da ta saka farin lace shi kuma ya saka farar shadda, duk inda za a ace su kalli juna Nuwaira sai ta daga kai take kallon Maleek domin bata tsawo sosai kuma ba zaka ce mata gajera sosai ba, kana kallonta kasan ita kadai ce yarinya a cikin manyan yan mata. Ba kamar Humairah da Ameer ba domin shi kadan ya darata tsawo, wani gurin ya rika hannunta wani gurin kuma ya rike kunkurunta wani hoton kuma ya dora hancinsa a nata, babu kalar rigimar da Humairah bata yarda yi ba kamin ya shawo kanta daker ta yarda, wani hoto kuma ita da shi sun juya baya suna kallo mai daukar hoton dukansu sun yi murmushi kana ganinsa kasan yan'uwa ne domin suna kama da juna musamman a yanzu da Humairah ta kile wuyanta har wani zane yayi an mata dilka ta ci abinci mai kyau kuma hankali ya kwanta domin ta samu abun da take so.

Ummi ta girgiza kai bayab ta gama kallon video bikin da aka yi na yau thursday wato bride and groom Day, wani sabon event da ake yi kawayen Amarya kawai ke zuwa sai ango da friends dinsa ayi ta ruwan kudi ana chashewa. Maleek dai be yarda yayi rawa ba, daman shi irin ababen nan ba su cika burge shi ba, zuwan ma dan ya zame masa dole ne, Ameer ya daka rawa abunsa Humarah ce dai bata yi rawa ba domin ita ma tana da kunya, Namra da kanen Ameer ma sun yi rawa da yan matansu Shuraim ma ba da ba zaka ce zai aikata ba haka ya zage dantse yayi ta rawarsa friends dinsa suna ta masa ruwan kudi.

“Kin ga ďan nan naki be cika kunya ba Ummi”

“Kai wa san abun da zaka yi idan an tashi auren”

“Ni ma ai kin san rawa zan yi Ummi rana irin wannan ba ko da yaushe take dawowa ba, kuma idan ma ta dawo wata kila na yi girman da ba zan iya yin rawar ba”

Ummi ta gigiza kai tana kallonsa da murmushi.

“Ba mata daya zaka yi ba kenan?”

“Aa gaskiya ni ba irin Abiey ba ne, mata uku ma zan yi kin ga ina son na tara yara da yawa, kuma ni ina sha'awar auren mata biyu ko uku”

“Kai da har yanzu ma baka samu matar auren ba sai ruwan ido kake? Da yanzu an hade aurenka da yan'uwanka”

“Aa ni nafi son nawa ni kadai, kuma sai na zaba na darje kar na yi zaben tumun dare”

“Allah ya shirya ka kuma ya nuna mana yasa ina da rabon gani”

“Zaki gani Ummi In Shaa Allah”
Chapter 169 · 0% Book details