← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 176

Sashe 147

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana maganar tana hawaye ganin take ya kasa fahimtar manufar, bayan kuma ta san waye Sarkinsu kuma ta san su waye jama'ar garin, ko da ka kyautata musu idan kai ba dan garin ba ne za su iya cuta maka balle kuma ace ka munana musu ka karya dokokinsu.

“Idan ina ganin hawaye a idonki kina karya min guiwa ne kawai, ba zan ma dauki wayar ba mu tafi”

“Ya Maleek”

Ya aika mata da wani irin sihirtaccen kallo cikin kwayar idonta da ya hana ta karasa kiran sunansa ma balle kuma ta dora da abun da take da kudurin fada. Shi ya fara takawa ganin haka ya saka dole ta cira kafa suka fara nufar mutanen a tare, tawaga jama'ar Sarkin suka yi musu wasu a gabansu wasu baya wasu dama wasu hagu, jama'ar garin da suka fara hada hadar safiya suka fito sai kallonsu suke, wasu kuma daga cikin gida suke fitowa suna kallonsu, ita dai gabanta sai faduwa yake, Maleek kuma ya dagewa zuciyarsa duk wani tsoro ko fargaba ya bar shi a cikin zuciyarsa bakinsa na ta karanta addu'ah har suka isa fadar.

A zahiri ya san Sarautar domin shi ma jikan Sarki ne, hakan ya saka shi yin ladabi ya cire talkaminsa tun kamin su shiga fadar, sannan yayi bismillah ya nasa kafarsa cikin katuwar fadar da aka kawata da fatar farar daminsa, kujerar kuma aka yi da fatar zaki aka dora kan Zakin saman kan kujerar dama da hagu na kujerar kuma kanun manyan macizai ne daga inda Sarki zai dora kafarsa kuma kunamu ne da ka tsafe aka hade su guri daya aka busar da su aka yi ma Sarkin gurin dora kafa. Babu annuri babu far'a babu sakewa da walwala a fuskar Sarkin da ya kwana biyu har tsufa ya fara cin karfinsa, sandar sarauta ce a hannunsa wasu zaratan jarumai suna tsaye dama da hagu suna masa fita, kujeru da aka jesa a fadar suna cike da masu rike da Sarautu a garin, daya bayan daya Nuwaira ta bisu da kallo har idonta ya sauka a kujerar da ake aje mata ta tsafi abun da ta yi arba da shi ya bata mamaki matuka Eid ne zaune a kujerar shi ma fuskarsa a hade take babu alamar ya taba dariya babu imani da tausayi a idonsa Maleek kawai yake yi ma mugun kallo na fitina. Sai da suka iso tsakiyar fadar sannan suka tsaya mutanen da suka yi musu rakiya kuma suka matsa daga gefe aka bar Maleek da Nuwaira tsaye suna fuskantar Sarki.

Cikin halshensu Sarkin ya fara magana da Nuwaira.

“Kin karya dokar da muka saka miki, kika gudu kika bar garin Garuk, bayan kuma kin san hukuncin da muka shai'anta miki idan har kafarki ta bar garin Garuk me yasa kika gudu”

“Saboda na tsorata a wacan lokacin, kuma ban shirya karbar hukunci akan laifin da ban aikata ba, ba ni na kashe mutumen da kuka zargina da kashewa ba, haka kuma ban shirya karbar Sarautar da kuke cilasta dole sai kun ba ni ba”

“Kin gudu kin tafi a gurin mutanen da suka fi mu tsafi da iya sarrafa aljanu saboda su baki kariya daga garemu, kin watsar da al'adarki da addininki kika dauki ta su. hakan be wadatar da ke ba har sai da kika gayyato daya daga cikinsu zuwa cikin garinmu, ya karya mana dokoki ya ci mutumci yayi fada da jininmu akan wani dalili”

“Ku kuka kira ni, Eid kuka aika har cikin gidan da nake rayuwa tare da mutanen da na dauka a matsayin dangina, gashi nan be fada muku ba?”

“Mun tura shi ne kawai saboda shi kadai ne yake iya sarrafa kansa ya shiga cikin gidan da kike, babu kalar tsafin da ba mu aika miki ba, amman ya kasa samunki saboda kina cikin gidan da tsafinsu ya dara na mu, daga lokacin da kika gudu na kira taro na sanar da duk wanda ya kamata ya sani ya dauke mu kwana hudu kamin mun hanke shawarar abun da zamu yi, daga karshe muka cin ma matsaya akan kasheki, amman Eid ya tsaya kai da fata wajen ganin kin rayu, babu kalar azabar da ba mu yi masa ba a lokacin da yake ziyartarki a haka ya jure, muna daf da yafe ki ya bukaci a dawo da ke ko da ba za a baki Sarautar ba, sanadin guduwar da kika yi ya saka mun sauya sarautar tsafinmu ta shekara da shekaru, a dole muka yi mata garanbawul daga karshe aka cin ma matsayar baiwa Eid Sarautar, hakan ya kara masa kima da daraja a idonmu, shiyasa har ya roki mu dawo dake a cikin garinmu kuma muka saurareshi”

Cikin tsananin mamaki Nuwaira ta kalli Eid da har lokacin Maleek yake harara, sannan ta kalli Maleek da be san abun da take fada ba balle kuma abun da Sarkin yake tanbayarsa.

“Me kuke tattaunawa?”

“Wani abu mai ban mamaki Ya Maleek”

“Ku tambaye shi, me yake bukata daga garemu? Idan rakiya yayi toh zai iya komawa mun gode da zuwansa, amman ba zamu zauna da butulu irinki ba, idan muka yi kora ba ma bukatar dawowarta a cikin danginmu, a da mun yanke shawarar kasheki, sai dai Eid ya bauta miki ya jure duk wata kalar azabar mu saboda mu barki ki rayu, ta karkashin kasa mun yi ta aika miki da mutuwa har a daren jiya, abun mamaki kin aje al'adarmu da addininmu saboda kin ga na wadanda suka fi mu karfi. Tabbas yaro baka shigo garin mu ba sai da ka shirya, domin wani be taba gwada karya mana dokoki haka ya kwashe lafiya ba, ba mu tana tsarrafa tsafi irin wanda muka yi a daren jiya ba, amman komai ya kasa samunka a kusa da dakin ma aljannunmu ba su kusanta ba, a tare da kai mun ga aljanna mai irin tsafinka mun saka wadanda suka fita karfi da iko sub rabata da kai a tunaninmu ita take baka kariya, da muka sake aika tsafi sai ya dawo mana, tun farkon shigowar muke ta jefarka amman jifar ta kasa isa a inda kake, madubin tsafinmu ya kasa ganin fuskarka, jama'ar da ake turawa su kiraka kana saka musu fargaba da tsoro, a yanzu ba ma jayya da kai mu dai ba ma shiga gonar kowa kuma ba ma son a shiga gonar mu, Eid ya fada min tun jiya ka dage sai ka ga Sarki zaka tafi, fadi bukatarka Sarki zai sallame ka ka yi tafiyarka”

Sarkin ne da kansa yake fada Eid na fassara masa dan dolensa, mamaki da jindadi da kauna ya hana Nuwaira cewa komai sai kallon Maleek dake cike da burgewa.

“Alhamdulillah, hakika duk wanda ya dogara ga Allah shi kadai Allah ya isar masa, ni bana tsafi van tana tsafi ba, kuma ban taba sanin yadda ake yinsa ba kuma bana fatar yinsa, ni dai na san ina bautar Allah ba tare da shirka ba, sannan ina karanta ayoyi da addu'o'in kariya, a jiya ma na kwana ina karanta suratul Bakara, kuma duk wanda yake karanta iya da ayatul kursiyu Allah ya turo mala'ikunsa su yi gadin Mutum ne, a inda mala'ika yake kuma aljani be isa ya raba gurin ba, muka karanta ta a gidanmu shiyasa kuka aika tsafinku be isa a garemu, domin idan aka karanta sau daya a wata tana tsare gida ta hana duk wani abu mai cutarwa rabar gidan har wani wata, saboda wannan ni ba tsafi nake ba da za ku surfafa bincike da za ku fahimci wannan addini ne ba tsafi ba, kuma ina fatar wata rana za su aje na mu addinin da al'adar ku karbi cigaban da duniya ta zo da shi haka ma ku rumgumi musulunci ku watsar da tsafinku”

Cikin alfaharin da jindadi Maleek yake fada ana fassarawa Sarkin da yarensa, har sai da ya kai karshe sannan Eid ya ce.

“Ba mu bukaci ka tallata mana addininka ko al'adarka ba, ka bar mu da na mu, kai ma ka rike naka, Sarki yana tambayar dalilin ganinsa da kake son yi, kuma ina ganin ka samu abun da kake bukata zaka iya tafiya”

“Aa ban fadi bukatata ba tukuna, dan haka ba zan bar garin ba sai na isar da abun da ya kawo ni”

Eid yaja numfashi da karfi da bakinciki sannan ya fadawa Sarki abun da Maleek ya fada.

“Tuk rid jaur bhakar suuf hutk garfha ifftuk galink galink ket”

Eid ya juya ya fassarawa Maleek.

“Ya fadi bukatarsa ba ma son zamansa a cikin garinmu”

“Ina neman auren yarku Nuwaira ne, saboda a yanzu irin addini take yi, ta saba da irin al'adata da kuma dangina, ina tunanin bata da bukatar zama a cikin garin nan, domin ba zata canja addini ba ba zata sake komawa addininku ba, kuma ba zata karfi kujerar tsafin da kuke son bata ba, idan har kuka yarda kuka ba ni aurenta zan dauke ta mu bar garin nan da ita yau din nan ba sai gobe ba, kuma ba za su sake ganinmu ba, ina tunani bata da amfani a gareku a yanzu saboda ta karya dokokinku kuma kun yafe ta kamar yadda ka fada”

Eid ya mike tsaye ya bar kujerar da yake zaune ya nufo inda Maleek yake cikin zafin nama, kamin ya karasa Sarkin ya daka masa tsawa.

“Karka kuskura kai kanka ga halaka, kana ganin wannan matashin ka san sai da ya shirya sannan ya shigo garin nan, neman yake a taba shi ya janyo mana fitina, fassara min me yake da bukata”

Sai da Eid yayi da gaske ya yaki zuciyarsa sannan ya iya fadawa Sarki abun da Maleek yake da bukata, daga baya ya jadadda masa da cewar ba za su aminta da haka ba, domin wannan ya zama cin fuska, kuma saboda ta karya dokokinsu har sun yi fushi da ita sun yafe ta ba shi yake nufin a barta ta aure wani bare ba. Sarki ya daga masa hannu.
Chapter 147 · 0% Book details