← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 176

Sashe 60

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya daka mata tsawa, sai ta shiga motar da sauri ya rufe ya zagaya dayan side din ya shiga ya saka key, wani yanayi ya samu kansa a ciki na dabam, domin be taba kusanci da mace a mota kamar haka ba, be ma taba daukar mace a motarsa ba, sai wannan karon wanda ya tabbatar da acan da ne ba zai ma iya ba, ko da kallonta ne balle har ya dauketa.

“Waira bata son Abiey, Abiey ya kira waya yayi mata fada, Waira bata son Maleek, Maleek ya zo da mota yayi mata fada ta shiga Mota”

Ta fada tana takurewa gurin daya sai hawayen da suka fi kama da na shagwaba take. Ya kalli gefenta ya dauke ido.

“Baki son uba, baki son ďansa sai ki kashe su toh”

Tana jin hakan ta san bakar magana yayi mata sai kawai ta fashe da kuka, ta kama zoben dake wuyanta ta rike. For the first time ya ji kukan mace ya sauka a kunnensa daidai wa daida ya cika kwakwalwarsa.

“Ohhhhhhhhh miye wannan kuma? Zaji min kuka for sake i hate this crying, Abiey why zaka aiko nan? Kai”

Ya bude wani guri a motarsa ya dauko airpod ya saka a kunnesa ya kunna Bluetooth din wayarsa yayo connected ya kure karatun Qur'ane dan ya daina jin kukanta. Har aka isa gida bata daina kuka ba, shi kuma be bata hakuri ba ko kallon inda take be yi ba. Tana ganin ya cire abun kunne ya kashe motar sai ta bude muryarta mai kara ta kwala ihu just to annoy him tun da ta lura baya son kukan.

“Louder please”

Ta kara karawa tun da ya bukaci haka.

“Very good well done, to fitar min a mota please...”

Bata fita ba sai cigaba ta yi da kukan, shi kuma ya bude motar ya fita ya barta a ciki. Yana shiga cikin falon ya san ya lafiya ba, domin tun a downstairs yake jin kukan Nimra bama kamar da ya haura sama. Dakin mahaifiyarsa ya fara shiga sai ya same ta tsaye gaban madubi tana hawaye, kamar jiran take ya shigo sai kawai ta juyo ta fara bashi labarin abun da ya faru tana ta maimaita gurin da Abiey yake dora mata laifi, tun fara bashi labarin har ta gama hawaye take.

“Ba zai bar ni da abun da ya ishe ni ba, sai ya dauko wani laifin ya dora min?”

Maleek be ce komai ba ya juya a fusace ya fice daga dakin Ummi, be yada zango ko'ina ba sai ďakin Nimra, yana shiga ya maida kofar ďakin dakw bude ya rufe ya saka mata key.

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023

[6/17, 10:49 PM] My S Line: 31

“Nimra i thought mun rufe babin Ameer tun a lokacin da kika bashi aron motarki”

Maleek ya fada bayan rufe motar da yayi. Kuka kawai take ta kasa cewa komai.

“Tun a lokacin Abiey da ni da Ummi mun nuna miki ba mason wata alaka tsakaninki da shi, ko dan mu ya kamata ki nisanta kanki da shi, kin manta bacin ran da kika saka mu a wacan lokacin ne?”

“Ban manta ba, ban kuma fada soyayya da shi akaran kaina ba, ban yi soyayya da Ameer Saboda zuwan wannan ranar da zan bata muku rai ba, ban san miyasa kuka tsani Ameer da yawa ba, kamar wanda ya kashe muku wani”

“Baki san waye Ameer ba ne Nimra, duk mai kaunarki zai so ki auri mutumen kirki, I'm not saying Ameer ba shi da kirki no, mutum ne da wani be isa ya saka shi ko ya hana shi aikata abun da yake so ba, and i don't think ma yana kaunarki da gaske saboda mun hada jini da ke, and i know ya fi tsanata da kowa a yanzu”

Ya karasa bakin gadon ya zauna.

“Zai fi kyau ki hakura ki cire shi a ranki, saboda iyayenki basa so, kalli abun da ya ja miki a yanzu, and kin manta yadda ya batawa iyayenki rai lokacin da kika ba shi motarki? Da ace Abiey be yi nasarar rufe case din nan ba, ko kuma ace yarinyar nan gawa ce aka samu a motar baki san iya abun da hakan zai haifar miki ba”

“Ameer be ja min komai ba, shi kullum neman yake a bashi dama ya sanar da iyayena cewar yana kaunata, amman saboda tsoron abun da za ku fada ya saka na boye soyayyarmu, har hakan ya faru amman Ya Maleek ina son Ameer idan kuka raba ni da shi zan iya mutuwa...”

“Indai har baki mutu kamin ki sanshi ba, to ba zaki mutu saboda kin rabu da shi a yanzu ba, Ummi kuka take saboda abun da kika aikata Nimra, ta samu rashin fahimta da Abiey duk saboda ke baki ji kunya ba? Har kike iya fadar zaki mutu idan kika rabu da shi, da shi ne na tabbatar zai iya rabuwa da ke a take”

“Shi ma ba zai iya ba, yana so na tsakani da Allah ne, ya hade soyayyar masoyi da ta ďan'uwa da ya kasa nunawa yar'uwarsa shi ya nuna min, kana cewa na rabu da shi saboda baka taba so ba Ya Maleek wani digo be taba dirar maka a zuciya da sunan soyayya ko kauna ba, ba san miye a cikin shaukin son ba, saboda ka kasa rabar kanenka mata ma balle ka nuna musu so, baka taba yin budurwa ba, idonka be taba duba wata mace da rahma ko tausayi ba, balle kuma so! Wallahi Ya Maleek na shiryawa karbar ko wane kalar kalubale akan Ameer, idan ba har kuna da wani matsala da shi da dabam ba, be kamata fadanku ya taba soyayyar mu ba, idan har kasan zafin rabuwar uwa da ďa, to haka rabuwar masoya take, amman kai ba zaka gane ba saboda baka taba ďanďana zakinta ba, da gaske nake Ya Maleek idan kuka Ameer mutuwa”

“Ya ji wata yar iskar yarinya yaushe kika san Ameer din ma, da zaki fada min haka? Okay idan har Abiey zai yarda ki aureshi ko Ummi sai ki aureshi din, amman idan suka nuna basa so, ba zaki aureshi ba, ki rubuta wannan ki aje”

Ya mike tsaye ya juya.

“Saboda baka san me ye so ba Ya Maleek, aure zamu yi ba zaman banza ba”

A fusace ya juyo ya daka mata tsawa.

“Yanzu me kuke yi? Ke ce baki san waye Ameer ba Nimra amman ni na san Ameer in and out, na san abun da zai iya da wanda ba zai iya ba, da ace sonki yake da gaske, da ya sauke gabar da yake da ni dan shi ne ba shi da gaskiya, amman a halin yanzu Ameer ya bata da duka friends din mu saboda ni, idan na zauna a guri Ameer ba zai sake zamansa ba, idan na gaisa da wani Ameer ba zai sake magana da shi ba, taya zaki kalli idona ki fada min cewar Ameer da gaske yake son ki? idan ban soyayya ba ai na san hankali da tunani, don't you think yana amfani da ke ne kawai saboda ya bata min rai? Ameer baya yafiya, Ameer baya aje burinsa saboda wani, ba ya kashe kansa saboda wani ya rayu, ya sani duk ranar da na san yana soyayya da kanwata zan yi bakinciki wannan ma kadai abun farinciki a gurinsa, and i know one thing for sure Nimra, Ameer ba zai ajeki a gidansa for more than one year ba tare da ya taba ki ba, ko dan kasancewar ki kanwata zai aikata miki komai, and bari na fada miki wani abun da baki sani ba, Ameer yana da mistress ya ajeta a wani gidan na dabam you're not the only one wannan kadai be isheki abun kunya...?”

“Ameer ba shi da kowa sai ni, kuma ni Ameer ba taba min komai ba, saboda so na yake da aure, baka fahimce ba ne Ya Maleek, ka bude zuciyarka ka zuba mata tausayi da soyayya, ka zahilci so...”

Da mugun mamaki Maleek yake kallon.

“Ina fada miki gabas kina fada min yamma? Saboda an kyale ki?”

Baya son saka hannunsa dan haka ya nufi gurin Laptop dinta take ya fisgo carjar ya nufi Nimra da ita ya fara dukanta kamar an aiko shi, tun yana dukanta tana ihu har ta kai muryarta bata iya fita Ummi kuma ta saka fitowa ta ceceta sai nata kukam take a dakinta tana sauraren muryar Nimra. Waira ce ta hau sama ta tsaya bakin kofar ďakin Nimra tana buga kofar da karfi, ba dan ta san abun da yake faruwa ba, domin shigowar kenan bayan ta ga ji da zama a motar da Maleek ya barta. Kamar wanda aka cewa ka yi ta dukanta har sai bacin ranka ya fita haka Maleek ya rika zunawa Nimra wayar carjar laptop din a jiki ido a rufe har kafarsa ya saka ya shureta, abun da be taba ba, ya kan doke su amman acan baya lokacin da suke shige masa hanci da kududdufi sai dai ba kamar irin dukan da yayi mata a yau ba.

“Do you know what? Da ina tunanin idan Abiey da Ummi suka amince zan goya miki baya ki aureshi, but yanzu na yanke hukunci ba zaki aureshi ba, sai kuma na ga yadda zaki yi, ki mutum na gani”
Chapter 60 · 0% Book details