← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 176

Sashe 113

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Toh sai ya zama, jarabawa ta shiga, dan kasuwanci da yake abun be karbe shi, har ta kai ya bar garin Kano ya dawo Abuja da zama saboda ya biyo abokinsa nan suna sana'ar siyar da Nama, kuma a nan sai Allah ya amsa masa ya samu bude sosai har ma ya kama haya ya dawo da Bahijja a nan, kuma ita ma sai ta zama kamar ni haihuwar ba mai yawa ba ce, shi kuma mijin Allah be mishi tsawon rayuwa ba, yana zuwa kano duba iyaye da yan'uwa yana zaune a Abuja yana dan tana kasuwancinsa, sai gashi ya hadu da hatsarin mota lokaci yayi, a madadin ita Bahijja ta koma gida da zama sai Iyeyen mijin suka ce me zai hana na zo na zauna tare da ita tun da bata da kowa a nan zata ji sanyi, saboda an fi son mace ta yi takaba dakinta, ni kuma daman haya nake a Kano, tun bayan rasuwar Malam yan'uwansa suka siyar da komai har dan gidan da kika siya mana, aka raba gado aka ba ni na wanka na, kin san ba ni da namiji, tun da Margayi Zaharardeen ya rigashi Ratsuwar dole za su ci gadon dan'uwansu, ni da Bahijja abun be yi mana auki ba, daman gado ba shi da albarka sai wanda ya dauki bakin wuta”

Hajiya taja numfashi ta sauke sannan ta cigaba tana fadin.

“Shiyasa ban musa musu ba da suka ce dawo, sai na hada yan komatsaina na dawo, bayan ta gama wanka kuma sai muka cigaba da zama nan, kin san yadda zaman yadda zaman gidan wani yake idan ba gidanka ba, ko kuma gida mai wadata ba dadi kake ji, kuma da ma ace a cikin yaya akwai wani a can dole na kwasheta mu koma, ita kuma ta dan sabada nan din shiyasa tafi son zama a nan, saboda tana dan kasuwsncinta kamin abu ya zama yadda ya zama a yanzu, ga kuma karatun yara, kin ji yadda aka yi muka dawo nan da zama, amman ke ai na san tun da kika je mana bankwana nan da zama ko?”

Kai kawai Ummi ta iya dagawa sai kuka take kamar wata criminal. With confused and tunanin ta wani bangaren Ameer ya dubi mahaifiyarsa ya ce.

“Why are you crying?”

“Dole ta yi kuka, aba yau ba ne wata kila ta tuna baya”

Hajiya ta amsa masa itama nata idon na cika da hawaye. Sai Ummi ta tari numfashinta.

“Ba baya nake yi ma kuka ba Hajiya, kukan na yanzu ne, abun da na aikata nake tsoron yadda za ku kalli abun, nake tunanin yadda za ku karbi abun”

Hajiya da bata fahimci komai ba ta ce.

“Baki mana komai ba sai alheri Zahra, in ma bake ba wace matar ce zata siyawa iyayen tsohon mijinta gidan ta kai Ubansa makka ta bawa uwarsa jari? Ba ďa ba jika? Aikin mana ya ni ba abun da kika min Wallahi kin g....”

Zuwan wani tunanin ya tsayar da halshen Hajiya daga sarrafa kalmar da zata fito daga bakinta, sai ta yanke maganar tana kallon Ameer da yayi baya ya jingina da kofa, shi ma kallon Hajiyar yake cikin wani yanayi na tashin hankali. Ummi ta juya ta kalli Ameer da Hajiya ke kallo sannan ta juyo ta kalli Hajiya, sai wani sabon kuka ya kwankwaso mata kofa hawaye suka ce mata salamatu alaiki. Hajiya kam kallon Ameer kawai take babu dauke ido, surarta da zubin halittarsa suke tuna mata da ďanta Deen, yayinda wani bangare na zuciyarta ke raya mata abun da hankali da tunani ba zai dauka ba, balle har ta yarda. Ssi da Ummi ta yi da gaske sannan ta iya tsayar da kukanta, ta mikewa tsaye tana fadin.

“Hajiya Allah ya kara lafiya, zamu tafi daman na ce ya kawo ni ne na duba ki kawai”

“Ummi zauna”

Kamar saukar aradu haka ta ji maganar da Ameer yayi mata ta dira a kunnenta ta yi cikin kanta. Bata da kuzarin musa mass duk da kasancewar shi ne ďa ita kuma uwa, sai ta koma ta zauna gabanta ns bugawa da karfi, idonta kuma ta kafe shi gurin Ameer.

“Akwai abun da ya kamata ki warware ko ba haka ba? Zuciyata na hararon min wani abu, ni da Hajiyar da Humairah duk kin saka mana shakku. Warware maganar dake cikinki, fada min wani abun da ban sani ba, ba ni labarin yadda kika san tsohuwar nan”

Ummi na fargaba da tunanin kalmomin da zata hada ta fadi maganar ta sigar da Ameer da kuma Hajiya za su fahimceta. Ta tsinkayo Hajiya na karanta masa alakarsu.

“Ni uwar mijinta ce ta farko, mutumen da ta aura kamin ta auri mahaifinka, ni ce na haife shi, Bahijja da ka ji tana ambata ita ce kanwarsa, su biyu kawai Allah ya ba ni, sai kuma yanzu da na samu yan jikoki, wannan Humairah da ka sani yar Bahijja ce matar da ka ji tana tambaya, ita mahaifiyarka har ta haihu da Deen amman Allah be kawo abun da ta haifa da rai ba, shi ya tafi kuma shi ma abun da ta haifa ya tafi, ba dan ma mace ta haifa ba, Wallahi da na ce kai ďansa ne domin kamar ta yi yawa har ta bace, duk na kalleka sai na tuna da ďana...”

Ta kai karshe maganar, su kuma hawaye suka fara gudana a idon Ameer. Ummi na ganin haka ta mike tsaye da sauri tana kiran sunanshi.

“Ameer”

Sai ta sauke kansa kasa, duk yadda ya so gushewa ganin laifin Ummi ko daga mata kafa yayi mata uzuri a wannan babin sai abun ya gagara.

“Hajiya, ni ne ďan da kike zaton ya mutu, ba mace ba ce namiji ne, kuma ban mutu ba ina raye ni jikanki ne, ni ďan da aka haifawa ďanki ne”

Wani abu mai kama da mafarki kamar zahiri ne ya baibaiye Hajiya, ba dan hankalinta da yake tare da ita ba, da kuma kaifin tunani da Allah ya bata na gane komai ba tare da rikicewa ba, tabbas da babu abun da zai hana ba zata rikice a lokacin ba. Sai dai duk da haka sai ta ji kamar ba daidai ta ji abun da Ameer yake fada ba, dan haka ta sake fadar.

“Kasan abun da kake fadi ďan nan? Wacan jika da aka haifa min mace ce kuma bata zo da rai ba, kuma kuma an ba mu gawarta mu muka rufeta da kanmu, ko dai baka gane bayanin ba?”

“Ke ce dai abun zai miki wahalar fahimta a yanzu, wata gaskiya ce da zaki ganta kamar karya, wata kalar gaskiya ce mai wuyar karba, Ummi kin cutar da mu, ina jin kamar abun da kika fada be isa ya saka ki aikata abun da kika aikata ba, why Ummi why”

Wannan karon da kuka Ameer yake tambayarta, sannan ya karasa gurin Hajiya ya kai hannunsa ya taba kafarta mai lafiya, ya daga zanenta zuwa guiwarta ya shafa kafar ya kalli fuskarta mamaki da rashin yadda da karyar da suke kokarin mayar mata a matsayin gaskiya ya saka ta sakin baki da ido tana kallonsu, can kuma ta kalli Humairah ta ce.

“Humaira ke kin gane abun da kike nufi”

Hunairah da tun da ta fahimci abun da yake nan take kuka, ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana kara rushewa da wani sabon kukan.

“Dan Allah ku min bayani, kaina ya kasa dauka na kasa fahimta abun da kuke nufi”

Ummi ta koma ta zauna a kujerarta, yayinda Ameer ya kwantar da kansa a kafarta mai lafiyar hawaye dake fita a idonta suna zuba a kafar, ba tare da damuwa da tsabtar Hajiya ko kazantar ba, yau ya manta cewar kafar almajira mai yin bara a titi, mai zama a gidan da yake jin kyama da kazanta take rayuwa, shaukin son sanin mahaifinsa da kuma ganin kakarsa ya mantar da shi komai. Be taba tunanin haka ake ji idan aka hadu da uba ko dangi uba na kusa ba sai yau, lallai yau ya yarda shi ba ďan Mr Bashir ba ne, domin be taba jin shaukin da sarkewar zuciya dan gani ko tarayya da wani a cikin family Mr Bashir ma, amman gashi a yau yana yi, zuciyarsa har wani fisga take how he wish ace Mahaifinsa ma yana raye.

“Hajiya, ban yi zaton abun zai bayyana ta haka ba, ban yi zaton ta haka abun zai zo ba, ban san ta ina zan fara miki bayani ki fahimta ba, Ameer ji...ka... Kan...ki... Ne.... Ne.... Dan.... Da.... Na.... Na... Na... Na... Na....”

Sai numfashinta ya sarke da halshenta ta kasa karasa sentences din dake gaba.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un..... Ta ya? Ba yar ta mutu ba? Wa muka binne kenan?”

“Wadda kuka binne ba jikarku ba ce, ba ni na haifeta ba, ni ďa na haifa ba mace ba”

“Yanzu kuma kin kara rikita ni, toh da kika haife shi ina kika boye shi? A ina kika aje shi har ya girma? Idan ma gaskiya ne me zai saka ki aikata hakan?”

“Gaskiya ne Hajiya, Wallahi wannan yaron ďan Deen ne, jininsa ne ďan da na haifa ne”

Hajiya ta kalli Ameer tana bata fuska irin na tsofin dake kokarin ganin sun ci karfin kuka, amman ina sai da ta yi sai dai bata bari sautin kukan ya fito ba.

“Me yasa kika boye shi? Kamaninshi sak na Zaharardeen tun ranar da na fara ganinsa na ga kama yake da Deen, amman zuciyata bata raya min cewar shi jinina ba ne, me yasa kika boye shi? Me zaki yi tabbatar min da yaron nan jika ne? Ta ina zam gamsu?”

Ta inda Ummi ta ji zata iya, ta fara fede mata biri da wutsiya, ita kuka Humairah kuka Hajiya kuka Ameer hawaye.

Hajiya tayi kuri da ido sai hawaye take bayan gama kukan. Ummi ta share majina ta kalli Hajiya da yanayin da take ciki ta ce.

“Hajiya ki ce wani abu mana”

Hajiya ta kalleta ta kalli Ameer sai ta sauke dauke idonta.
Chapter 113 · 0% Book details