← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 176

Sashe 69

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sanin kamar ba zai maimaita mata furucin ba ya saka ta saki hannun Shuraim idonta na cika da kwalla.

“Sulem karka tafi...”

Shuraim da abokinsa sun dauke idonsu daga kallon Maleek, Shuraim ya kalli Waira yayi mata murmushi.

“Ba yanzu zan tafi ba, idan kuma zan tafi zan miki magana je ana kiranki”

“Aa ka zauna duka a nan please Sulem...”

“Shuraim...”

Ya gyara mata, a kokarinta na gyarawar sai ta sake furta sunan a yadda take fada.

“Sulem....”

Yadda ta kira sunan ma ya masa dadi, sai kawai yayi murmushi ya kalli Namra da har lokacin ta saka sakim fuska.

“She's my patient”

“Just...”

Ta tabe baki tana yatsina fuska kamar ta ga abun kazanta. Murmushi kawai yayi ya duba agogon hannunsa kamin ya kalli abokinsa da shi mamakin yake ya ce.

“Ma maybe ka manta ta amman na sha baka labarinta”

Abokin ya dan yi murmushi be ce komai ba sai kallon fuskar Namra yake yana karantarta. Ba dan kar yace ta wulakanta shi ba da a gurin zata barshi tsaye, for which reason zai rumgume wata a gabanta, at first ma ta dauka wata alaka can sai bayan sun gama murzar juna zai ba fada mata cewar patient dinsa ce.

“Bismillah....”

Ta masu ishara da hanyar part din Abiey.

“Na dauka wata alaka ce mai karfi a tsakaninku”

Suna tafiya ta fadi haka sai ya kalli yanayinta ta da ya canja ta kasa sake fuska har lokacin. Murmushi yayi ya juya ya kalli kofar part din Ummi inda Waira ta shiga ya sake juyo suka cigaba da tafiyar.

“Wata kila kina nufin alakar jini, amman a gurina alakar da zaciya zata samu samu kwanciyar hankali idan ta san wanda take tausayi yana cikin koshin lafiya ita ma wata alaka ce mai karfi, da kin san yadda na damu da aka dauko yarinyar aka ce za a zo da ita Abuja, da kin taiyani murnar ganinta da na yi a gidanku, ko ba komai na san zata samu kwanciyar hankali da tsoro a nan”

“Haka ne ina taya ka murna Congratulations Sulem”

Ta fada tana dariyar yake, a badini bakar naganar ce ta yi masa, sai dai shi kuma be fahimta ba domin be fashinci komai ba. Iyakar kokarin da ta yi na danne abun da take ji a zuciyarta ne ta kula da shi yadda ya kamata sai dai duk wani dauki da murnar da take na zuwansa ya ragu a ranta.

Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka Waira ta shigo falon da kofarsa take bude tun a fitar da ta yi da gudu bata tsaya rufe kofar ba, maida kofar ta yi ta rufe sai ta tsaya jikin kofar tana taba hannunta ganin fuskar Maleek a hade.

“Ba ki da hankali? Ta yi bako ya zo gurinta kije kina ruining abun da ta shirya, ji yadda kika fita da gudu kafafuwa tsil tsil kamar tsuntsuwa, ku a garinku ba ku da tarbiyar girmama bako ne? Haka ake tarbon bako?”

Yana mata fada tana turo baki daman tuni hawaye ya cika idonta domin bata so rabuwa da Sulem dinta ba, gashi kuma yanzu ya tsare ta da fada. Takawa ta fara yi ta bi ta gabansa zata sai ya daka mata tsawa.

“Ba magana nake miki ba shi ne zaki wuce”

Zabura ta yi ta hawayen dake makalle a idonta ya sauko saman kyakkyawan kumatunta, hakan kuma ba karamin kyau ya kara mata ba, dana da kwarjinin da har kuka kyau yake mata idan tana yi.

“Sulem ne ai”

“Ba Sulem ba sule, ina kika sanshi?”

Ta kai hannu ta rika sarkar wuyanta ta soma magana muryarta na karkarwa irin wanda kuka ke daf da subucewa.

“Ya bani wannan ya saka min”

“Miya faru?”

Mahmood dake saukowa stairs ya tambaya ganin hawaye na sauko mata wasu na bin wasu.

“Wallahi yarinyar nan bata da hankali yau na gani, wanda zai auri Namra ne ya zo sai kawai ta tafi ta rumgumeshi baka ga yadda Namra ta bata rai ba, idan ba hauka ba ina aka taba haka”

“Toh ai Sulem dina ne”

Ta fada tana kuka. Mahmood ta sauko gaba daya ta tsaya inda take.

“Wane Sulem”

“Sulem”

Ta nuna masa sarkar wuyanta.

“Oh na gane kai ta san shi fa, idan bata san shi ba ai ba zata je haka nan ta rumgume shi ba, ka gane Sulem din da take yawan magana, aiko ni ma zan so ganinsa ko dan na ji inda suka san juna tun da bata fada mana ba, waya sani ma ko ďan'uwanta ne”

“You miss the point ko yaya ne be kamatadaga ganin mutum an gayyato shi kije ki rumgume shi ba, wannan ai rashin tarbiya ne da sanin ciwon kai, she's so annoying sai ta rika yin abu kamar wata yar jaririya”

Mahmood ya zauna.

“Maybe daukin ganinsa take kuma ita ai ba musulma ba ce wata kila al'adarsu haka ake tarbon mutum”

Tsaki yayi ya nufi hanyar fita daga falon, Mahmood ya bishi da kallo baki saki, sai a yanzu shi ma yake mamakin sbun da Maleek yayi kamar ba shi ba, da can babu ruwansa da duk wani abun da ya shafi Waira, wata kila saboda kanennsa ba su taba rumgumar wani a gaban idonsa balle ace ya tsawata musu ita kuma ya ga ta yi dole yayi mata fada. Maleek be duba yiyuwar akwai alaka tsakaninsu ba, shi dai abun da idonsa ya gane masa ne be masa dadi ba, domin be ga dalilin rumgume mijin da kanwarsa zata aura Da Waira ta yi ba, yanayin yadda ya ga fuskar yar'uwarsa ta sauya baya tarin farincikin data wuce ta gabansa ta fita da shi ya sosa masa rai, wata kila yana taya yar'uwarsa kishi ne, ko kuma yana ganin rashin dacewar hakan da gaske. Bayan fitar Maleek Mahmood ya kalli Waira yayi murmushi

“Karki damu, haka yake takurawa kowa a gidan nan kin san halinsa ai ko?”

Ta daga kai.

“Ina son na tafi gurin Sulem”

“Yanzu ki bar shi ya huta tukuna, idan ya huta zamu tafi gaba daya har Ummi mu gaisa da shi sai ki sake ganinsa, yanzu zauna ki ba ni labarin i da kika san shi”

Ta zauna a kasa sai dai ta kasa labarta komai, sai tabin sarkar wuyanta take idan ta dago ta kalleshi sai ta yi murmushi kamar ba ita ce hawaye ya gama yi mata zuba ba.

“Toh shiga ki fadawa Ummi kin ga Sulem tun da ba zaki ba ni labari ba”

Ta mike tsaye da sauri daman abun da take nema kenan, da gudu ta hau stairs din kamar zata zame ta fado ta tura kofar dakin Ummi ta shiga sai ta samu bata cikin dakin, fitowa ta yi ta nufi dakin Nimra ta tura idan bata samu Ummi ba ai zata iya labarta Nimra sai dai tararda da ita da ta yi tana kuka ya saka jikinta yayi sanyi sai ta juyo ta fito ba tare da tace mata komai ba. Dakinta ta nufa tana shiga ta sami Ummi da Dr Zainab a dakin zaune Ummi tana hawaye.  Take kwarin guiwar data shigo da shi ya mutu sai ta tsaya jikin kofar tana kallon Ummi.

“Waira kin san shi ne?”

Ummi ta tambaya cikin karfin hali domin bata manta dazun data fita daga dakinta tana fadin Sulem ba. Wannan ne karo na farko da Waira bata damu da tambayar ko son jin dalilin Ummi na kuka ba, ta karasa cikin zumudi ta fara fada mata abun da zata iya tunawa a game da Shuraim. Sannan ta nufi gurin data aje tsofin kayanta na fata na ainahin garinsu ta bude ta dauko takardar da yayi mata rubutu a jiki ta nunawa Ummi.

“Ya ba ni wannan da babaken mutane za su kawo ni Habuja”

Ummi ta karbi takardar ta bude.

‘Ban san iya inda tafiya zata dauki be, ban san iya inda kaddara zata tsaya da ke ba, ban san yaushe Allah zai sake gadamu ba, a duk inda zaki karance ina fatar guri ne mai aminci da natsuwa. Ya kai wanda zai ci karo da wannan sakon ka ji tsoron Allah karka cutar da ita, fruits ne abun da ta fi ci, kuma ta tsoro da rashin sabo da mutane da wuri, Allah ya tsare ki

Dr Shuraim...’
Chapter 69 · 0% Book details