Sashe 114
Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Dan Allah Hajiya ki yi magana ko da tsunuwa zaki furta min na cancanta, kuma na shirya tarbonta da Ameen, amman ni ban aikata hakan a nufin na cutawa kowa a cikinku ba, ban aikata haka ba saboda na son zuciya ba”
“Toh me zan ce Zahra?”
“Ki fadi duk abun da kike son fada Hajiya, na cancanta, na shirya neman afuwarki sai dai ban yo zaton abun zai zo mana ta wannan sigar ba, tunanina da zatona kuna kano har yanzu, ina ta kokarin shirya zuwa kano na kai Ameer a gurinki na nuna masa ku da sauran dangi kuma na roki yafiyarku”
“Zaharadeen be miki komai ba sai alheri Zahra, talaka ne, amman tufafinki baya bari ki wanke, sai dai ya wanke miki ya goge, ko da ya aureki baki iya girki ba, amman haka yake zaune da ke, sai dai ya siyo muku abinci ko ya girka, kamin ki fadi kina son wani abu ya aikata miki, kowa yace be zon Zahra Deen be son shi, saboda ke babu halin da be shiga ba, akan me zaki saka masa da wannan? Me ya miki? Cewar dole ce ta saka kika aikata saboda kina tsoron rasa rayuwarsa shin kin kai ni ni uwarsa ne? Ba gashi kin yi aure kin cigaba da rayuwa ba? Ni ko fa? Ba ni da mai maye min gurbinsa, duk na tuna cewar Deen ya tafi be bar min jika ba sai na yi kamar na yi hauka, zuciyarki bata raya miki ina bukatar ba ki kawo min shi ko sau daya na gani? Malam ya har ya bar duniya be san yana da jika ba, ya zaki yi da hakkinsa? Wace Wahala ce taki Malam be sha ba, amman sai ki saka masa da wannan? Saboda muna talakawa ne ko kuma saboda kina ganin ba mu da hakki ne? Shim kaunar Deen ne baki yi har yanzu ko kuma son zuciya ne kawai irin an ďan adam?”
Gefen mayafi Ummi ta saka ta share hawayenta tana jin wani gwarin guiwar magana yana tunkarota.
“Hajiya zaki iya tuna, wani lokaci da Deen ya tirsasa Dr Zainab yayar Abiey yin karya ta yi min kazafi cewar ina dauke da cutar HIV? Saboda kawai a fasa aurena da Abiey? Kuma yayi nasara Ammy da yan'uwanta suka ce ba zai aureni ba? Mutumen da na fara so aka saka mana ranar aure? Kuma ba a fadi haka ba sai a ranar da za a daura min aure? Bayan tara mutane da shela? Zaki iya tunawa?”
“Ramuwa kika yi kenan? Amman shi Deen ai ya aikata miki haka ne saboda yana kaunarki, tun da kuka taso yaron nan yake kaunar, kawai saboda ya san ba za'a yarda ya aureki ba ne ya saka shi aikata haka, kuma a cikin wasiyar da ya bar miki ai ya fada komai”
Ummi ta daga kai
“Kwarai ya fada min saboda yana sona ne, saboda yana tsoron rasa ni ne? Saboda yana son rayuwa da ni ne? Saboda idan babu ni a rayuwarsa zai iya shiga wani hali, komai yana cikin kaina ban manta ba”
Ta mike tsaye.
“Toh ni ma na aikata kwatankwacin abunda Deen ya aikata, tunani be bani zai mutu ba, hankalina be kai gurin da zan fahimci kuskure ba, saboda idanuwana a rufe a wacan lokacin, fatana kawai na samu kudin aikin Deen, bayan aikatawa kuma sai tsoron abun da zaku jefe ni da shi ya saka dole na barwa Mr Bashir yaron, kamar dai yadda Deen ya kasa fada min cewar shi ya shirya a yi min gwajin karya ace ina da hiv, saboda Abiey ya fasa aurena, bayan aure kuma na yi gwaji yafi a karga ba a ga cutar ba, wannan sai ya saka na zargi Abiey da butulce min yaki aurena saboda ina talaka shi kuma dan sarauta dan masu arziki, ashe abun ba haka yake ba.... Kuma Deen ya kasa fada min saboda yana tunanin idan ya fada min gaskiya ba zan yarda na zauna a gidansa ba, ba zan yarda na so shi ba, yana tsoron kada kallon da nake masa a matsayin Jarumin da ya taimaki rayuwata ta ceto ni daga kunyar duniya a ranar daurin aurena ya tashi zuwa wani monster, ban san gaskiyar komai ba sai bayan ransa, sai da ya mutu Hajiya, amman a haka kike nemawa danki uzuri saboda yana naki, ni kuma kike son shiga tsakanina da ďana, kin san shekara nawa na yi wannan cutar tana cina? Kin san wutar da na kunnawa kaina take cin zuciyata da jikina? Kin san yaushe ne Ameer ya fara saurarena yana kallona a wata mace mai mutunci? Cikin watan nan ne? Amman a yanzu kokarin lalata alakar kike, ni ma rayuwata ba mai tsayi ba ce, kamar dai ďanki, abubuwa da yawa da ke kika samu gani a matsayinki na uwa kuma kaka ni ba zan samu ganinsu ba”
Tana magana hawaye bin wasu hawaye. Ta mikawa Ameer hannu.
“Ba ni makulli zan tafi gida”
Ameer ya dago ya kalleta sai kuma tausayinta ya kama shi, wasu abubuwan da ya ji ta fada da be san da wanzuwarsu rayuwarsa ba sun saka ya fahimci ita ma dai ta sha gwagwarmaya kamin ta samu salama.
[7/20, 10:36 PM] My S Line: 59
Humairah ta kara taku uku dake tsakaninta da Ummi ta duka har kasa ta ce.
“Ummi, dan Allah kar fushin zuciya ya jaki ki fita a wannan halin, ki zauna zuciyarki ta sauka, sai Ameer ya kaiki gida, mu bar abun da ya wuce ya zama tarihi, mu fuskanci gaba”
Ta fadi haka nan ne saboda Hajiya da mahaifiyarta Bahijja sun sha bata labarin abun da Deen ya aikata a baya, bata san Ummi ce macen da aka aikatawa haka ba, sai a yanzu hakan ya ninka tausayin da take mata a sanin da ta yi mata na sabuwar mahaifiyar Ameer. Ummi ta zauna a hankali domin ita ma tana bukatar zaman, Ameer ya dago daga kafar Hajiya ya kalli mahaifiyarsa dake kokarin tsai da hawayenta.
“We're not equal, kowa yana da good and bad side, I'm sorry for what I said earlier mu tafi na kaiki gida”
Ummi ta ki kallonsa wani kullin hawaye da ta kebe na zubo mata.
“Ka bani key kawai ni zan iya zuwa, idan ba zaka iya zama da ni ba, zaka iya tafiya gurin Mr Bashir ko wani guri inda ka zaba, ba zan cilasta kowa sai ya zauna da ni ba, ba dole ne kowa sai ya soka ba. Na gaji haka nan yanzu kuma, duk wanda ba zai fahimce ne, zai iya fassara ni da yaren da yafi fahimta da ganewa, zan hakura da komai nima na gwada rayuwa, kalubalen kuma ya isa haka, a yanzu ba ni da karfin dauka”
Mikewa yayi tsaye ya taka bayanta ya tsaya, ta yi tunanin ko wata maganar zai fada mata ko ya nuna mata wani abun sai dai ga mamakinta sai ta ji ya rumgumeta.
“Ina son a haka Ummi, yanzu na fara enjoying iyayena na gaskiya, no matter how you're, ko da kuwa ace kun fi kowa talauci duk yadda nake kyamar talauci zan zauna da ku, Humairah ta taba fada min na yi hankali da rayuwa, amman ban fahimce me take magana akai ba sai yanzu, i regret everything na sha wulakanta yarinyar nan, at the end gashi ta zama ashe yar'uwata ce ta jini, ni ma ban aikata abu mai kyau ba so you're not the only one”
Ummi ta rufe ido ta kai hannunta ta dafa hannun Ameee tana kuka. Hajiya kam har Ummi ta bar dakin bata sake furta komai ba sai hawaye take tana bin Ameer da kallo, duk wani reason da Ummi ta bata na abun da ya saka ta aikata abun da ta aikata da kuma neman a fahimce har ta kwatanta mata da ďanta Hajiya bata ji ta gamsu da shi a matsayin Hujja ba, zuciyarta da idonta na kallo Ummi da wata manufa da bakinciki marar misaltuwa. Ko sallama da Ummi ta yi ma Hajiya bata amsa ba sai Humairah ce ta amsa mata suka fita tare da Ameer yana gefenta suna tafiya har suka isa gurin motar, jiri ke dibanta sai dai bata yarda ta nunawa Ameer ba sai ta jingina da motar dake kusa da inda Ameer har sai da Ameer ya bude motarsa sannan ta yi hanzarin shiga ta zauna.