← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 176

Sashe 119

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Sun miki kyau, Ummi ta siya miki?”

Ta rika rigar ta kai masa a hanci.

“Kamshin waye yake yi?”

Perfume din yayi masa kama da wanda ya taba ji, but ba zai iya fadar wake kamshin irin perfume din kai tsaye ba.

“Ya Maleek mana, shi ya ba ni rigar da saka min hula saboda na ji sanyi, Ummi tace naje na kaiwa duk wanda na gani a falo yayi min assignment sai na kai masa shi ne ya ba ni”

Cikin zumudi da jindadi marar misaltuwa take fadawa Ameer haka, ita dai yau kam Maleek ya burge ta kuma ya biyata duk wani kallo na mugunta da take masa yau ya kau a idonta saboda ya bata riga ta saka, ara mata yayi ko kuma bata yayi duk bata da tabbacin ko daya, sai dai tana jin cewar ya nuna mata kulawa hakan kuma ya saka ta farinciki. Kamar an yi ruwa an dauke haka murmushi yayi batan dabo a fuskar Ameer.

“I'm just joking rigar bata miki kyau ba, wannan ma kayan maza ne ba na mata ba, kuma sun miki yawa be kamata ki saka ba, sannan kuma bana son ganin komai a jikinki ko a maganar matukar ya shafi wani namijin ba ni ba”

Yana maganar yana kicin-kicin cire mata rigar, ita dai hular tuni ya cireta ya jefar. Sai ta kamashi da kokawa tana son hana shi cire nata jacket din.

“Ni ina son abuna haka karka cire min Haba Ameer yana min kyau na gani, ina son kayan mazan haka, ya nuna min kulawa ne kawai fa, duk wani abun kyautatawa da Ya Maleek zai min ina so i like it”

Cak Ameer ya tsaya daga kokarin rabata da rigar da yake ya dauke hannayensa, ba dan kukan da take kawai ba har saboda furucin da ta yi masa a yanzu. Ita kuma bata fada da wata manufa ba sai dan abun da ta fahimta kuma ta dade tana jira, wato ranar da Maleek zai daina hantararta da yi mata fada.

‘Ba laifinki ba ne, na gane idan na yi wasa daga like it sai like him then love him, ina shuka wani zai girbe okay...’

Ya fada a ransa sannan ya juya ba tare da ya ce mata komai ba ya fice daga dakin, ita kuma ta tashi tana kuka ta nufi inda ya jefar da hular ta dauka tuna lokacin da ya cire nata zoben da Shuraim ya bata, shi kawai baya son ya ga an bata kyau. Yanayin yadda ya fito daga dakinta ya sauko kasa ya zauna a kusa da Humairah is something else, domin babu annuri a fuskarsa, ya hade rai kamar wanda aka yi ma bushara da bakin labari, zuciyarsa sai sake-sake take masa idan ta kwance masa wacan ta saka masa wannan. Duk wata hira da Ummi take da Humairah hankalinsa baya gurin, shi ya matsu ma Humairah ta yi sallama ya sanar da Ummi abun da yake ransa, domin ba zai iya jira sai gobe ko jibi ba, kawai ba zai iya jinkiri da jira ba, ba kuma ba zai iya hakuri da abun da Maleek yake masa na shiga hanci da kududdufi ba, ta ya zai kula Waira abun da ba muruminsa ba. Daga Ummi har Humairah sun kula da yanayinsa ba ma kamar Ummi da idan ransaya bace ko ta ga damuwa a fuskarsa take jin kamar an cire mata duk wani jindadi na duniya.

Ummi ta saka Hanne ta kawo ma Humairah abinci sannan ta dauki wayarta ta kira Namra ta sauko suka gaisa, kana ta shiga dakinta ta yi mata goma na arzki daga kan perfume body spray da atamfa mai kyau, Namra kuma ta bata Veils har biyu saboda Ummi ta yi mata maganar ta bata wani abu a kokarin Ummi na ganin kowa ya kawar da abun da ke zuciyarsa. Ummi ta fito har balcony ta rakota tare da Namra da Ummi ta yi mata dole. Humairah ta bude mota ta shiga kamin ta rufe Ameer ya kalleta ya ce.

“Bari na kira Waira ku ga juna, ita ce kadai ba ku gaisa ba”

Namra ta taba baki kamar zata ja tsaki sai kuma ta juya ta shige ciki saboda gudun bata ran Ummi.

“Ummi muje ciki akwai maganar da nake son na yi da ke kamin na tafi, Maybe ba zan kwana a gidan nan ba yau saboda Daddy yace yana son na yi dinner a can shi ma yana da maganar da zai yi da ni”

Ummi ta amsa masa.

“Okay”

Sannan ta kalli Humairah ta ce.

“Allah ya kiyaye Humairah na gode sosai ki gaida gida”

“Gida zai ji Ummi, ni ce da godiya Allah ya saka miki da alheri ya yaye miki damuwarki”

Ameer da Ummi suka hada baki gurin amsawa da Ameen. Sannan Ummi ta juyo suka shigo cikin falon, ganin Hanne na zaune a falon ya saka Ummi ta zarce dakinta kai tsaye yana biye da ita har suka hau sama. Idonsa sai ya koma gurin dakin Waira zuciyarsa ta raya masa yanzu tana can tana kuka ko kuma tana jin haushinsa. After sun shiga dakin Ummi ta zauna shi ma ya zauna sai shiru ya biyi baya, ita tana sauraren abun da zai fito daga bakinsa shi kuma ya samu kansa da jin nauyin furta mata kurinsa kai tsaye, wannan ne karon farko da yake jin haka, bayan kuma ya shigo da zimmar furta mata komai kai tsaye. Wata kila saboda tana ita ne ko kuma saboda Waira ce da ta banbanta da sauran mata a gurinsa, ya'allah kuma saboda wannan ne karon farko da zai gabatar da wata mace a matsayin wacce yake so da aure, amman zai iya ikirarin kunya ko jin nauyi akan komai ba halinsa ba ne.

A dan zaman da yayi a gida da kuma experience irin na uwa mai ƴaƴa maza da mata ya saka Ummi fahimtar yana jin nauyi ko shakkar furta mata abun da yayi niya ne, lura da ta yi da yadda ya rike hannunsa yana matsawa kuma ya kasa daga kai ya kalleta. Hakan ya sakata tasowa daga inda take zaune ta dawo saman kujerar da yake ta zauna ta fuskance shi.

“Ameer maganar tana da nauyi ne ko hatsari? Ko kuma tana da kunya ne? Wani abu zaka bukata? Ko kuma wani abu zaka gabatar? Kar tunanin yadda zan karbi abun ya saka ka yin nauyi ko jin kunya gabatar da bukatarka, fada duk abun da kake so a duniyar nan matukar be tsabawa Allah ba, na maka alkawari zan maka shi, wannan duty na na uwa, wata kila da nan ma zaka yarda ina kaunarka sosai, ko wani ka kashe ko wani abu ka aikata karka ji nauyi ko tsoro fuskance ka fada min saboda ni Mahaifiyya ce, uwa kuma mai tausayin ƴaƴa ce kuma mai kaunarsu, balle kuma ni da nake da kai a matsayin ďa, dole zan sama maka mafita a duk inda take”

Kalamanta sun karfafa masa guiwa kuma sun masa dadi, ta haka ne ya dago ya dubeta duba na tsanaki yana murmushi.

“Ummi”

Sai kuma yayi shiru ya sake maida kansa kasa.

“Ummi... Daman...”

Ya kasa dago kai, ganin hakan ya saka ita ta kai hannu ta riko fuskarta ta dago ya kalleta

“Fada min me kake so Ameer duk abun da kake so zan maka shi a duniyar nan karka ji nauyin komai”

Ya rausayar da kai.

“Ummi akan Waira ne”

Ummi ta gyara zamanta irin na ina saurarenka.

“Ummi Daddy ya dade yana min maganar aure, ke kanki a yanzu na san abun da kike bukata ganin kenan, and my life has changed now ina son na zama cikaken namiji kuma na faka ku farinciki, maybe ma maganar da Daddy zai min yau ba zata wuce ta aure ba ina tunani wata kila kuma zai min magana ne akanki ko Hajiya, to cut the story short, ban taba duba maganar da Daddy yake min ba, saboda ban taba faduwa da yarinyar da nake ganin ta dace da ni ba, but when i lay my eyes on Waira, she has everything da nake so a mace, i can't breathe when she is not near, Ummi ina son Waira so na gaskiya so na tsakani da Allah son da ban taba yi ma wata mace ba... And i want to marry her....”

Kana duban murmushin dake fuskarta kasan daga cikin zuciyarta yake fitowa, baki yayi kadan ya bayyana yadda zuciyarta ta cika da farincikin farucin Ameer da kuma kudirinsa, yau ita Ameer ya kalla ya fada mata yana son yayi aure, kuma yarinyar data rika yake son ya aura, me ya fi wannan dadi a gurinta, hawayen farinciki dake fita a fuskarta ne suka bayyana masa farincikin ruhinta, kasa cewa komai ta yi, sai ta mika hannu ta riko ta dan kwanto ta rumgumeshi.

“You have no idea how happy i am, ka kaddara a ranka kamar ka auri Waira ne Ameer domin na tabbatar ita ma tana sonka, kuma na jidadi da na zama first person da ka fadawa wannan maganar Allah ya maka albarka farinciki da ma saka ni a yanzu nan Allah ya ninka maka haka a rayuwarka”

Da dan mamaki ya dago daga jikinta ya kalleta.

“Na dauka ba zaki yi farinciki ba?”

“Why? Ai na fi kowa son farincikinka Ameer, kuma karka manta Waira a hannuna take yanzu, ko da ace baka sonta na gabatar maka da ita ka amince ka aureta abun farinciki ne a gurina balle kuma kai da kanka ka furta cewar kana sonta....Wow Alhamdulillah Allah all my thoughts zaka gabatar min da Humairah ne”

“Humairah ia just my friend kuma cousin a yanzu”

Ummi ta shafa fuskarta tana jin wani irin farinciki marar misaltuwa. Ya mike tsaye yana dariya

“Bari na je kar na bar Humairah tana ta jira”

“Okay”
Chapter 119 · 0% Book details