← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 176

Sashe 59

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tambaya yana zaunawa a kusa da ita cike da kulawa. A yanzu ba hawaye take ba bacin rai ne a tare da iya daya maye kukan da take a na bakinciki a dazun.

“Ba lafiya ba Abiey, wani nauyin ne ya fado wanda ba zan iya dauka ni kadai ba”

“Fito fili ki fada min abun da yake faruwa”

“Shawara ce na yanke, daga Nimra har Namra za su fito da miji cikin satin nan kuma aurensu ba zai wuce kasa da wata ďaya ba”

Yanzu ma kallonta yake, sai dai kallon mamaki ne yake mata wannan karon.

“Hiayatee ba zaki yanke wannan hukuncin mai zafi a cikin kankanen lokaci haka nan kawai ba, dole akwai abun da kika gani fada min meya ke faruwa ne?”

“Jiya.. Dare bayan na fito daga bangarenka na leka ďakin kowa har na kai ga na Nimra, sai na samu wayarta a kasa bachi ya sace ta, na duka na dauki wayar sai na yi arba da wani sabo daya daga min hankali, number bata da suna sai heart emoji, ya turo mata sako cewar ta san irin karyar da zata sake yi su hadu, yayi missing dinta, and he can't wait for her hug and kiss...”

Wani dim dim dim gaban Abiey yayi ba, ya kara tattara hankalinsa ya maida gurin Ummi.

“Ban mata magana ba, sai na kyaleta daman ta fada min cewar jiya ta tararda taro da yawa a gurin saloon din da taje bata samu ba, dan haka yau tana son ta koma, na bata dama saboda na gane da gaske can zata tafi ko wani gurin, bayan ta fita na bibiyi motarta ina cikin tawa motar har ta isa wani gida aka bude mata gate ta shiga...”

Ummi ta bashi labarin komai har zuwa yanzu da ya shigo cikin gidan. Abiey ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya aje har sai da Ummi ta ji tsoro ta tashi ta bi bayansa da sauri. Dakin Nimra ya nufa yana tabawa ya ji kofar a rufe sai ya banki kofar dakin da wani irin karfin zuciya da jiki.

“Nimra ki bude dakin nan, idan ba haka ba zan saka a balle kofar nan kuma idan aka balleta sai na rabaki biyu sai dai a buga ni a Jarida ki bude dakin nan na ce”

“Abiey calm down bari na yi magana da ita”

Ya dakawa Ummi tsawa.

“Ya zaki ce na kwantar da hankalina? Kamar baki san girman abun da ta aikata ba? Dole na yi magana da ita”

“Zata bude amman ka matsa jiki kofar zan mata magana zata bude”

Ya matsa gefe yana sauke numfashi da karfi, rabon da ya samu kansa a bacin rai irin haka tun a lokacin da Deen yake raye. Ummi ta matsa kusa da kofar ta ce.

“Nimra...”

“Na'am”

Sai ta amsa cikin kuka muryarta na rawa gwanin tausayi.

“Bude kofar nan, zamu yi magana da ke”

“Aa Ummi aa dan Allah”

“Ki bude na ce, so kike ki sake bata mana rai? Tambayarki zamu yi kuma dole ne ki amsa mana zamu yi magana ta fahimta ne ki bude kofar”

Ummi ma da kamar fada take mata maganar domin ita ma nata ran a bace yake. Sanin Abiey zai fi yi mata sassauci idan Ummi tana kusa ya aaka ta nufi kofar ta bude tana kuka sai ta matsa baya da sauri. Ummi ce ta fara shigowa sannan Abiey da sauri Nimra ta yi gefen Ummi sai Abiey ya daka mata tsawa.

“Karki kuskura taba min mata, dawo nan ki tsaya...!”

Wani irin dauke numfashi ta yi kamar zata shide, saboda tsawar ta ratsata kanta shiga har cikin jikinta, sai ta dawo ta tsaya a inda ya nuna mata jikinta na rawa.

“Tun yaushe kike aikata fasadin nan? Me ya saka baki bashi damar zuwa gidanku ba kika zabi kebewa da shi?”

“Saboda ba za su yarda ba Abiey, kuma ba mu aikata fasadi ba Abiey, Wallahi ban aikata zina ba”

“For how long kike tare da shi?”

Ummi ta tambaya.

“Anfi shekara.....”

“Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, waye ubansa a garin nan dan gidan uban waye? Akan wani dalili kike haduwa da shi a wajen gidanku?”

Abiey ya tambaya yana matsawa kusa da ita, muryarsa kuwa kamar zata tashi ďakin. Matsawa ta yi baya tana kallon Ummi kamar tace Ummi zo ki cece ni ba dama. Bata ankaro ba Abiey ya kai mata mugun naushi a fuska sai da hokoranta ďaya ta dago bakinta ya cika da jini, wani tsalle ta ta yi, ta yi baya da sauri ta rike bakin ta haura saman gadonta.

“Wayyo Allah na na shiga uku, Ummi ki taimake ni Abiey ka yi hakuri dan Allah”

“Waye shi na ce?”

Ya sake daka nata tsawa, a rike ce ta fara zazzago masa bayani.

“Ameer ne, Ameer dan gidan Alhaji Bashir, wanda suka yi faďa da Ya Maleek, Ameer din da na bawa Motata ta tafi da ita Katsina Ameer ďin...”

Bata karewa ba Abiey ya daga mata hannu ya rumtse ido, Ummi kuma ta fadi zaune tana kallon Nimra cikin matukar tashin hankalin da ba a saka masa rana.

“Bakar zuri'a, bakin jini, ubansa ya gama shi kuma yanzu na shuka min nashi, so yake ya lalata min zuri'a so yake ya ɗasa min bakincikin da ubanaa ya bari...”

Abiey ya fada cikin wani irin fusata da be san ma iya abun da zai fito daga bakinsa ba. Kamin ya juyo gurin Ummi.

“Duk laifinki ne, babu gargadin da ban miki ba akan yaron nan, ta ya za'ace yarinya tana fita waje ta hadu da wani sama da shekara ďaya baki sani ba a matsayinki na uwa sai bayan da ya gama lalata min ƴa?”

Ummi ta mike tsaye tana kallon mijinta cikin wani irin bacin rai ta amsa masa.

“Kwarai laifina ne Alhaji Aliyu sai ka hada ni da ita Nimra ka binne...!”

Ta daki kofar ďakin da karfi ta fice fuuu kamar zata tashi sama.....

MALEEK POV.

“Ohhhh”

Ya fada yana buga teburin dake gabansa, bayan Abiey ya fada masa ya tafi makarantar su Waira ya ji abun da yake faruwa saboda sun buga masa waya kan cewar ta yi fada, kuma ya kira wayar Mahmood be samu ba, ga Ummi ya ji yanayinta da matsala zai tafi gida. A dole dolensa ya tashi tare da wayarsa da key din motar ya fice daga office din, yana gwada kiran Mahmooda ya ji ko zai same shi ya fada masa Abiey yace ya tafi saboda shi ya fasa zuwan, be samu ba har ya shiga motarsa ya murza key ya dauki hanyar makarantar. Har ya isa cikin makarantar be daina karan Mahmood ba kuma be samu wayar ba.
Cikin makarantar ya shiga gurin principal din ya gabatar da kansa, sai suka isa da shi gurin vice principal, a nan ya samu Waira zaune rumgume da jakarta, tana ganinsa ta mike tsaye da sauri ta nufo inda yake wai ita ta ga wanda ta sani sai kuma ta ja ta tsaya tunawa da basa shan inuwa ďaya. Gurin ya samu a one of visitors chairs ya zauna yana kallon mutumen da ya mika masa hannu suka gaisa.

“Sunana Maleek na zo ne akan maganar wannan yarinyar”

Ya nuna Waira.

“Eh mahaifinka ya kira ai ya fada cewar ba zaka samu zuwa ba, amman ďansa zai zo”

“Lafiya me ya faru?”

“Fada suka yi da wata yarinyar, ita dai yarinyar tace Waira ta fara tsokanarta, sai suka fara fada shi ne ita Waira ta dauki dutse ta buga nata akai kanta har da jini yanzu haka ita ma mahaifinta yana hanya”

Maleek ya juya ya kalli Waira da ta rumgume jaka, sannan ya juyo ya kalli mutumen.

“Waira bata da fada gaskiya, sai dai ko idan ita yarinyar ta fara taba ta”

“Ba a gane gaskiyar kowa, ita ta kasa magana daidai yadda za a fahimce ta”

Maleek ya dauki takadar dake gaban teburin mutumen ta pen ya mika mata.

“Rubuta abun da ya faru”

Ta karba ta soma rubutawa tana hawaye.

“Kullum tana tsokanata tace min ni ban iya hausa ba, kuma bana magana da daidai, tana ce min kuma kafira ban san me hakan ke nufi ba, ko ta rika min dariya, shi ne yau da aka kai mu park ta tsokane ni kuma na buga mata dutse saboda ta fi ni girma ba zan iya fada da ita ba”

Ta mika masa sai ya karanta ya mikawa mutumen, mutumen ya karba yana tsaka da karantawa mahaifin yarinyar ya shigo tare da ita, har wani hakilo yake yana an taba masa ya.

“Wannan ne mahaifin yarinyar?”

“Aa yayanta ne bismillah zauna mana”

“Ba zan zauna ba, kuma sai na dauki mataki akan abun da aka yi ma yata matukar ba ku hukunta yarinyar nan ba sai kun ga abun da zai biyo baya domin ďa be fi ďa ba”

“Ka yi hakuri ka zauna muna tattauna ne a akan maganar?”

“Tattaunawar me? Ga ciwo kuna kallo ta ji wa yata kuma ku ce kuna tattaunawa karshenta a ba ni hakuri bayan an cucu yata”

“Toh me kake so ayi maka Malam? A fashe mata kan ita ma? Bayan kuma yar ka ce take tsokanarta?”

A take fada ya kaure a tsakaninsu, domin Maleek ya kasa jurewa da abun da mutumen yake yi ne, suka yi ta fadawa juna magana daker aka shigo tsakaninsu, Maleek ya saka Waira a gaba suka fito daga cikin makarantar zuwa gurin motarsa. A nan Waira ta nade hannayenta ba zata shiga mota ba, daman can bata kebewa daga ita sai shi a mota ba, fadan da ta ga yayi da wacan mutumen ya saka ta tsorata tana ganin kamar itama fadan zai mata idan ta shiga motar. Ya bude mata motar da kansa.

“Shiga mu tafi”

Ta lake kafada.

“Shiga ko na mareki yanzu nan”
Chapter 59 · 0% Book details