Sashe 135
Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya farka da farinciki da nishadin zuciya, ba na wanda ya samu biyan bukata ba, sai irin na wanda ya kusanci Sallah a lokacin da kowa yake bachi, Sallah kuma ta kusantar da shi ga Allah. Kusan wannan a bayyane yake duk wanda yake Sallah dare yana farkawa da farinciki da nishadi ko da bashi ko naira, fa kuma kusanci da yake karawa mutum ga Allah bayan hasken fuska da haiba da Allah ke sakawa bawa a fuskar duk wanda zai kalli mai Sallah dare.
Be tsaya jiran Daddy ko Mommy su fito ba, balle wani breakfast da ba damunsa yayi ba, zuciyarta bata bukatar arba da kowa sai abar kaunarsa Waira, dan haka ya shiga bathroom yayi wanka ya shirya cikin tufafin da suka fi yi masa kyau wato kananan kaya ya sanya turare mai kamshi, daman shi da turare 5&6 ne basa rabuwa da juna. Ya sauko da kuzarinsa ya fita harabar gidan, ko da be da abun fada mata shi dai yana bukatar ganinta, even if zaginshi zata yi ta fada masa magana marar dadi yana son jin duk abun da zai fito bakinta. Har ga Allah ya san yana son Waira irin son na mai fitar da mutun daga hankalinsa, mai saka namiji susucewa ya zama kamar wani soko, ba ita ce mace ta farko da ya fara gani ba, ya je gurare da yawa a duniya, tun yana da kurciyarsa har karatunsa zuwa yanzu da yake zaune a guri daya tare da familynsa amman be ga mace da ta dauke masa hankali ta birkita tunaninsa lokaci daya ba irin Waira. Yana tukin yana tuna duk wani moment na su na farinciki a baya, farkon fara haduwa da ita the way da take nuna farinciki idan suna tare, yadda take dagewa ta nuna ta san shi kuma tana son zama a kusa da shi, yadda yake iya tirsasa ta yi abun da bata so kamar cin abinci da bata saba ci ba, saka mata kaunar addinin musulunci da lurar da ida yadda addinin yake da kyau da gata, duk wannan ta tsaya ta saurareshi kuma ta fahimta ta gamsu, sai soyayyarsa ce kawai ta kasa samun muhallin a zuciyarta. It's because of abun da yayi ma Nimra or saboda abubuwan shaidanci da yayi ta aikatawa abaya ne. Har ya isa gidan aka bude masa gate ya faka motar be samu amsar tambayarsa. A ta inda zai ga windows din Waira ya faka yana hw spend time yana kallon gurin ji yake kanar zata leko tace masa Ameer darling good morning. Ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya bude ya fito daga cikin motar praying for her ya fara arba a idan idan ya shiga falon, sai dai hakan be saka hakonsa ya cin ma ruwa ba, domin ya shiga falon ya tararda Ummi da Maleek Mahmood Namra har ma da Abiey suna karyawa Waira bata tare da su, kamar wanda aka sarewa jiki haka ya shiga falon kallo daya zaka masa ka san ba su yake son gani ba, domin yawo yake da idonsa a inda ya san tana yawan zama ko zai ganta. Har yayi rabin falon sai kuma ya juya zai fita.
“Ameer”
Abiey ya kira shi sai ya juyo ba tare da ya amsa ba.
“Akwai abun da kake so ne?”
Yayi shiru, can kuma ya kalli upstairs.
“Ina son magana da Ummi ne”
“Ga Ummi ka a nan ai, bata upstairs”
Abiey ya nuna Ummi dake kallon Ameer cikin damuwa.
“Private”
Ameer ya fada yana dauke idonsa daga barin kallon stairs ya kalli Ummi.
“Ba privacy a nan gidan duk wanda zai yi magana sai dai yayi a gaban kowa dukanku daya ne ai, babu banbanci, idan har wani yana son kebewa sai dai ya kebe da ni, amman ban yarda ayi min yan ubanci ba a kebe da Ummi”
Kowa kallon Abiey yake da mamaki har shi Ameer da be gama fahimtar Abiey da wasa yake masa magabar ba ko kuma da gaske ne saboda ya ci fuskarsa.
“Go ahead gata nan zaune, zo ka fada mata”
Ameer ya matso yana kallon Abiey zuciyarsa da tunani kala kala.
“Akan Waira ne, ta min magana jiya da dare tace tana son ta musulunta ta hannuna saboda na samu wannan ladar, kuma na yi magana da Daddy ya ce zai yi magana da Imam dinsu, sai ya fada mana yadda za'ayi”
Kamin Ummi ta ce komai Abiey yayi murmushi.
“Maa Shaa Allah abu mai kyau, amman dai Ameer ai kasan ina cikin gidan nan ko? Kuma ina da hakki da Waira, kai da ita ina tunanin duk a karkashin ikona kuke, ya kamata ace ka fada min kamin ka aiwatar da komai, ko kuma an fada maka Daddynka ne ya fini son lada ko kuma ni ka raina capacity na ne?”
Ameer ya gagara cewa komai sai kallon rashin fahimta yake yi ma Abiey.
“Ka fada masa zan aiwatar da komai, ba sai yayi ba, yanzu ma muna tattaunawa ne akan maganar tafiyarta Umminka ta fada min cewar Waira tana son ta tafi, ni kuma na goyi bayan haka saboda na fara process din sanin danginta saboda hakan abu ne mai kyau ko dan sanin macen da za a gina iyali da ita, amman ina ganin ba zan barta ta tafi ita kadai ba, sai na sanar da police an ba mu police biyu ko uku, kuma a samu amincewar hukuma sannan kuma ku tafi tare da ita zai fi”
Maleek ya soke kai kasa gabansa sai bugawa yake da karfi. Ummi kuma tana kallon Abiey da wani irin burgewa ganin yana kokarin aiwatar da abun da bata tsammata ba a gurin Ameer. With confused Ameer ya dan ware hannunsa ya ce.
“Maybe ko zata tafi tare da Maleek saboda ta fi sakewa da shi for now ni ina da abubuwan yi da yawa”
“Amman kai zaka fi sanin hanya ai, kuma kai ka fi cewa ku tafi saboda kai kasan inda ka daukota”
Cewar Abiey yana nuna shi.
“Yeah amman Maleek zai fi”
Abiey ya daga kafadunsa
“Shikenan ba zan takura ka ba, duk yadda ka so haka za'ayi, shiga ka taso ta sai ku yi breakfast din a tare ita ma bata ci abinci ba”
“No... Zan yi... ”
Ameer ya so ya musa, sai dai ganin Abiey ya girgiza masa kai alamar aa ya saka dole ya fasa furta abun da zai fada ya nufi upstairs mamaki fal a zuciyarsa, Namra ma mamaki take, balle kuma Maleek da Mahmood da suke ganin kamar Abiey dinsu aka dauke aka kawo wani. Ummi kam jindadi ya hana ta cewa komai. A hankali ya tura kofar dakin Waira ya shiga tsoron kar tace ya mata ba daidai ba ya saka shi tsayawa bakin kofar dakin yana kallon yadda take shafa baby rabbit dinta da hannunta.
“Waira zan iya shigowa?”
Ta juyo ta kalleshi tare da daga masa kai, sai ya maida kofar a hankali ya rufe ya karasa inda take zaune a kasa, ya zauna ya hade kafafuwansa yana kallonta.
“Good morning”
Ya fada yana yafawa fuskarsa murmushi. Tunanin ita ya kamata ta fara gaishe shi ya hana ta amsawa, sai ma mika masa guiwarta da ta yi.
“Good Morning”
“How are you doing today? Beautiful Angel”
Ta sauke kanta kasa ganin irin kallon da yake mata kirin yake jira ya fada cikin idonta ya narke kamar ruwa.
“Abiey ya ce ki fito muje falo mu karya, kuma na yi magana da Daddy na akan musuluntar da zaki yi, yace zai yi magana da Imam dinsu, but then sai kuma Abiey a yanzu yake min maganar cewar zai yi komai ba sai Daddy ya shigo ba, i don't know ko haka din yayi miki?”
Bata ce komai ba, kanta na kasa har lokacin, shi kam a yanzu dai baya gajiya da kallon duk wani abu da ya shafe ta balle kuma ita din kanta.
“Ko kin fi son ki karya a nan?”
“Bari na wanke baki”
Ta tashi ta shiga bandaki, sai ya bita da kallo kamin ya dauki rabbit din ya fara shafawa yana laka shi da jikinsa jin yake kamar Waira yake tabawa saboda ta saka hannunta ta taba gurin. Tana fitowa daga bandakin ya maida idonsa a inda suka fi yi masa dadin kallo wato fuskar Waira, shigar da ta yi bandakin ta wanke baki da fuska sai ya ga kamar ta kara kyau da kwarji, sanyin ruwan dake fuskarta sai ya ji kamar ta tafi ya lashe su. Gaban madubi ta nufa ta dauki ribbon ta daure gashin kanta sannan ta nufi kofa kamin ta isa har ya riga ta bude mata kofar kamar wata sarauniya. Tana fara saukowa stairs din sai ta tsaya ta juyo ta kalleshi.
“Ba zan iya cin abinci a can ba kowa yana nan”
Wani iri take ji a yanzu, daman can tana ganin kanwarta da ta Abiey bata jika ba, a yanzu kuma tana ganin Ummi kamar tana tsoronta ne ko kuma ta tsaneta saboda abubuwan da suke faruwa.
“Na kawo miki daki?”
Kamin ta bawa Ameer amsawa suka hango Abiey na magana ba dan ya ji abun da suke fada ba sai dan ya fahimci damuwar Waira.
“Sauko mu tashi zamu yi mun gama ai, idan ganinmu ne zai hana ku ci a nan”
Ta kalli Ameer sai da ya karfafa mata guiwa ta hanyar daga mata kai, sannan ta sauka a hankali yana gefenta har suka isa dinning, kujera ce first abun da ya fara ja mata a zatonsa zata zauna a inda yaja, sai ya ga ta nufi kujerar da babu kowa kuma bata kusa da kowa ta zauna, tana sanda kai kasa alamar bata son kallon mutane. Ameer ya zauna a kujerar da ya ja, Namra ce ta fara mikewa tsaye sai Abiey ya kalleta ya ce.
“Baki gaishe da Yayanki ba?”
Ta kalli Abiey with shock, sai dai ba zata iya musawa mahaifinta ba, ko kuwa daga ita sai shi ne balle kuma a gaban yan'uwanta, saboda haka ta kalli Ameer ta ce.
“Good Morning”
Ya amsa mata kai, mamakin na gaf da kashe shi ganin Abiey ya dauko wata hanya da be san me yake nufi da haka ba.