← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 176

Sashe 34

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta bude idon kamar ta san abun da yake fada, a nan ma ta shiga bawa idonta abinci, tun daga kan kofar bathroom din take kallo har zuwa tube da karamin madubin da yake lake, kamin ta daga kanta sama, sakinta yayi a hankali ganin su biyu ne kawai a gurin babu wani ya saka bata yi yunkurin yin ihu ba ko roke shi, ya nufi durum ya bude ya zuba ruwa a bokiti sannan ya dauko soso da soap ya aje a gurin, ya bude gurin da kanwarsa take aje kayan amfaninta ya dauko sabon brush ya dauko brush and toothpaste ya zuba a kai ya mika mata, ta dade tana kallon abun sannan ta karba sai ta saka yatsanta ya kwashe toothpaste din da yake kai ta saka a baki ta lashe abun ta, ta hade sannan ta saka halshe ta lashe dan zaki zakin da take ji ya hana ta ji makakin da yake tare da toothpaste din, sai ta mika mata tana tande baki, abubuwa biyu suka zo masa a lokaci daya mamaki da kuma tausayinta a lokaci daya, ya mika hannu ya karbi brush din ya saka zuba mata wani sannan ya zuba wani a hannunsa yana nuna mata yadda zata yi, a maimakon ta saka brush din a bakinta sai ita ma ta saka yatsanta ya lakaci man ta saka a baki tana gogawa kamin ya goga yadda ya kamata har ya nuna mata ta zubar ita kan har ta hade nata, yana zubarwa sai ta tofar da yawu.

“Oh Allah”

Ya fada yana furzar da iskar bakinsa ya daga kansa sama, sai ita ma ta kwaikwayeshi sai dai ita bata ita furta abun da ya fada da kyau saboda ba yarenta ba ne.

“Oww Allah”

Ta furzar da iskan ta daga nata kan sama, zatonta yana nuna mata komai ne, be san lokacin da dariya ta subuce masa ba, sai ita ma ta yi murmushi, karbar brush din yayi ya aje sannan ya nuna mata ruwan dake cikin bokiti tana ganin ruwan sai ta bata fuska ta lake kafada domin ta yi arba da makiyinta. Sai ta matsa can baya ta rakube ta bata rai sosai. Ganin haka ya saka shi nufar kofar ya bude ya fito, a falo ya samu mahaifiyarsa a tsaye tana jiran fotowarsa.

“Ni kam ina cewa Allah yasa dai ba wanka zaka mata ba”

Yayi murmushi.

“Aa Maimoon zata taimaka mata ta yi wanka”

Maimoon ta nuna kanta cikin rashin jindadi.

“Ni kuma?”

“Haba ki tausaya mata mana, bakonka Annabinka kuma iya yau ne kawai tun da gobe wucewa za'ayi da ita”

Ba dan ranta ya so ba ta mike tsaye sai daj Mamanta ta saka baki kuma yayanta ya hade fuska.

“Ki wanke mata kanta sosai, kuma ki kula da ciwon dake hannunta”

“Yaya kamar wannan yarinyar za'ace ba zata iya yi ma kanta wanka ba?”

“Wanka na ce ki mata? Ki taimaka mata ta yi nake nufi, idan kin wanke mata kanta sai ki fito ki barta ta yi wankan, kina ganin yanayin yarinyar nan kin san bata saba irin rayuwarmu ba, yanzu ba Brush na bata da man wanke baki sai ta lashe man”

Cikin Mamaki Hajiya Hajara ta ce.

“Ni ai tun da ka fada min cewar tana tsoron mutane na san akwai matsala, anya ba memory kanta ya samu matsala ba”

“Bata yi yanayin da irin wadan nan mutanen ba, kuma ba su barta a asibitin ba balle a abincika kwakwalwarta ba, sai son tafiya suke da ita Abuja, ni tsorona daya idan ba tsafi za'ayi da ita ba, wata kila an ajeta a wani gurin ne aka koya mata rayuwar ta dabam, ko kuma an satota daga wani gurin ne, a yadda na fahimta su police din suna kokarin rufe maganar ne kawai, wata kila akwai manya a ciki, in ba haka ba mi zai saka a dauke ta a kaita can ba tare da ta ji sauki ba, idan har nema mata yan'uwa za'ayi ai sai a nema mata a inda yan'uwanta suke a nan ba tufafin jikinta ma irin na fata ne da aka ce a can da arna suna sakawa...”

Kamin Hajiya Hajara ta sake magana Maimoon ta fito tana fadin.

“Ihu take min kuma bata bari na taba kanta kuma Wallahi yayi datti da yawa sai an saka mata Clean”

Dr Shuraim ya juyo yana mata wani kallo mai kama da harara.

“Ina kika taba ganin an sakawa kan mutun clean? Sai kace kayan wanki”

Hajiya ta yi murmushi.

“Kar a taba mata kayana ko sai ka ce ke kike siya? Je bathroom dina ki dauko min shampoo and conditioner sai na rika miki mu wanke mata”

Ba musu ta juya ta koma sai Hajiya ta bi ta a baya, kamin ta kawo har Hajiya ta shiga Bathroom din ta tsaya tana mata kallon tausayi a kalaman Dr Shuraim cewar wata kila tsafi za'ayi da ita ya fi komai tsaya mata a rai, Maimoon ta kawo kayan sai Hajiya ta rikata ta yi mata irin na babba da yaro ta saka kanta a tsakankanin kafafuwanta Maimoon na zuba shampoo tana murza mata gashin dake a damke ana wankewa sau daya ta yi amfani da shampoo amman duk yawansa sai daya kare akan Waira, saboda dattin da kanta yake dauke da shi da kuma yawansa domin ya sauko har yama taba tile, duk yadda ta so ta kwaci kanta kasawa ta yi har sai da Hajiya Hajara ta wanke mata kan tass. Bata tsaya jiran komai ba ta kama rigar dake jikimta ta cire a nan suka tsaya kallon tufafin fatar dake a matsayin skirt dinta da kuma wanda ta yi riga da shi wacce ta tsaya mata iya kirji, da taimakon Hajiya Hajara Maimoon ta yi mata wanka wanka bana wasa ba, ba kuma daya ko biyu ba sau hudu suna murza mata jikinta soson yayin baki jikinta kuma yayi fari tass, hannunta mao ciwo ne kawai ba a wanke ba, shi ma iya bakin inda aka daure mata, kafafuwanta kuma Hajiya Hajara ce da kanta ta rike kafafuwan ta wankesu, ta saka abun gogewa ta goge mata dan abun da ba za'a rasa ba saboda rashin saka talkamin da take. Maimoon ta dauko tawul ta daura mata sannan ta janyo hannunta ta fito da ita, idonta yayi ja sosai saboda kukan da ci, ta yi ihu har ta gaji ta yi shiru dan kanta. Maimoon ta zaunar da ita saman gadonta a hankali sannan ta dauko baby oil din da take shafawa ta fara shafa mata a kafufuwa, babu yadda ta iya bayan mika wuya haka ta zauna kamar gumki Maimoon ta shafe mata jikinta ko'ina, sannan ta dauko hand dryer ta jona ta kunna, Waira na jin rurun abun sai ta zabura ta fashe da kuka.

“Ke ba jimi ciwo za'ayi ba”

Ina fa sai ta ki ta tsaya busar mata da kan yadda ya dace ganin haka ya saka ya mike tsaye ta bude akwatinta ta dauko mata doguwar riga ta karen miski ta saka mata sai ga Waira ta mike tsaye Maimoon ta ja mata rigar har kasa. Hannu ta saka tana tabawa, ta san karen misk domin suna saka irin wannan kayan a garinsu sai dai ba kowa ke sakawa ba sai mai wani mukami a garin. Girgiza kai ta yi bata damu da babu komai a jikinta ta cire rigar ta jefar ta dauki tawul din ta kare jikinta.

“Aiko akwai aiki, kina nufin saboda ya miki yawa ba zaki saka ba”

A zaton Maimoon saboda size dinsu ba daya ba ne ya saka ta guji rigar. Haka dai ta daure ta dauko mata wata rigar buba ta mika mata, sai ta karba ta rike tana kallon atamfar dake jikon Maimoon ta sauko har kasa, ita kan bata taba saka kaya har kasa ba, iyakar doguwar rigarta guiwa ne. Maimoon ta karbi rigar ta dauko mata riga da skirt sai ta karba ta rike rigar atamfar tana ta kallo musamman zip din dake jiki har da saka yatsanta ta taba ta ji yadda yake, Maimoon ta karba ta saka mata rigar, irin dinkin nan ne da ake kawo riga har gurin guiwa sannan ayi mata straight skirt, ta bude mata skirt din ta daga kafarta ta saka mata sai ta fisge kafar ta lake kafada.

“Ba zaki saka ba? To kina son wando?”

Bata da sabon panta hakan ya sakata dauko short na mata daga kafarta ta saka mata, shi kan wando ta saba shi domin suna saka na saki, hannu daya ta saka ta kama wando taja shi har saman mazaunan, Maimoon ta dauko turare ta saka mata sannan ta dauko mataji ta fara taje mata kan a nan fa aka fara sabon fada saboda zafi take ji sai ta ki yarda Maimoon ta taje mata kan da kyau, a dole ta bar mata shi haka ta saka mata mai a kan ta dauko ribbon dinta ta hade mata gashin guri daya ta yi mata parking sannan ta saka ribon din. Gashin ya sauko har rabin bayanta.

“Ji yadda kike da kyau dan Allah, amman kowa yayi miki wannan chabon kazanta a jiki ya ci amanarki, daman saboda ya boye kyauki yayi haka, ji ido har wani ruwan bula ya kwanta a ciki ga hanci gashi kamar na yar aljana, kai gaskiya Allah ya iya halitta”

Ita kam Waira bakin Maimoon kawai take kallon yarenta na sauka a kwakwalwarta idonta kuma na son tantance abun da bakinta yake furtawa. Kamin su dago kai a tare su kalli kofar dakin da aka bude, Waira na ganin fuskar da ta sani sai ta yi saurin ta nufi gurinshi tana wani kuka kamar na shagwana domin babu hawaye a idon sai dai ya kumbura saboda kukan da tayi, rike shi ta yi da dayan hannunta ta juyo ta kalli Maimoon tana jin wani irin tsanarta a ranta domin idan akwai abun da tana a rayuwarta bayan mutuwa to wanka ne, yau kuma anyi mata shi akan dole. Juyowa Dr Shuraim yayi ya kalleta sai ya ganta kamar ba ita ba, domin an wanke ta tass datti nan duk ya fita ga gashinta a mata farkin gwanin sha'awa.
Chapter 34 · 0% Book details