← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 176

Sashe 71

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta wuce fuuu ta koma ciki ta cire tufafin aikinta ta saka nata ta fice ba tare da ta yi ma kowa sallama ba. Yana kallonta ta fice sai ya mike tsaye yana amsa wayar Nimra.

“Hello”

Ta yi shiru sai hawaye take.

“Talk ba zan iya gane abun da kike nufi ba idan baki fada ba”

“Ameer zan tamvaye ka tsakaninka da Allah ka amsa min”

“What?”

“Ka taba son wata yarinya kamin ni? Kasan yadda Ciwon so yake? Ina daf da haukacewa Ameer”

“No ban taba soyayya ba, akwai dai wacce muka zauna a tare sunanta Angel, amman mun rabu kamin na hadu dake, sai dai daga ke har ita ban tana jin ina son kowa ba, ni a rayuwata ban taba son mace ba, but you lucky na ji jna tausayinki”

“Ba gaskiya ba ne Ameer ka ce duk soyayyar da ka nuna min ta karya ce, na san kana jin kwatankwacin abun da nake ji a raina, kawai kana bin cilastawar da iyayena suka maka ne cewar ka ce baka sona saboda su raba mu”

“Babu wanda ya isa ya cilasta ni, sau nawa zan fada miki wannan maganar ne?”

“Zaka iya rantse min Ameer?”

“Idan na rantse miki zaki yarda?”

Ta daga kai kamar yana gabanta.

“Wallahi tallahi ban taba sonki ba Nimra, ban tana jin ina kaunarki ba, ban tana jin soyayyarki a raina ba, duk wani kokarin kulla alaka da nake dake da kalaman da nake fada miki ko wani abun da nake nuna miki ina yi ne kawai saboda na samu nasarar yaudarar zuciyarki kuma na yi nasara sai dai ban yi amfani da damar kamar yadda na ayyana zan yi ba”

Wani abu ta ji ta soketa tun daga cikin kai har kasan kafafuwanta sai kuma ya dawo tsakiyar kahon zuciyarta ya tsaya, ta lumshe ido hawaye masu zafi suna sauko mata yawun bakinta ya canja dandano zuwa wani mai daci.

“Now I'm hurt... Thank you so much for everything, na gode Ameer”

Ta sauke wayar tana kamar ta hade zuciyata ta mutu gaba daya, gaskiyar da ya fada mata ta fi yi mata zafi siye da rabuwar da iyayenta suke son ta yi da shi. Maganar da Ummi ta fada mata cewar sun sha nono ďaya bata zauna mata a kai ba domin a tunaninta Ummi tana son raba tsakaninsu ba, sai dai a yanzu ta gamsu da maganar dan'uwanta Maleek cewar bata san waye Ameer ba. Ta saki wayar hannunta ta fadi kasa kafufuwanta suka fara rawa kamar ba za su dauke ta ba, tana kokarin mika hannu ta rike karfen windows din da take tsaye a kusa da shi ta kasa sai dai ta yi nasarar rikon curtains din windows din ta janyosu da karfi suka fado kanta ita kuma ta fadi kasa, nauyin kirji ya danne mata numfashi tana son ta daga murya ta kira akawo mata taimako amman ta kasa saboda numfashin baya barin muryarta fita, sai shakkuwa take kamar mai fitar rai.

“Hello...”

Jin shiru bata amsa ba kuma bata ce komai ba ya saka ya yanke kiran, ya cira kafa ya taka zuwa gurin motarsa ya shiga har ya murza key sai kuma ya fito koma ciki, sai dai wannan karon ba cikin yafa kai tsaye ba sai da ya tambaya ina kitchen din gurin yake aka fada masa sannan ya shiga kai tsaye ya doahi kitchen din wadanda suka san fuskarsa suna ta gaishe shi, be amsa musu ba domin ba gaisuwar ce ta kawo shi ba.

“Ina kuke aje kayan da kuke aiki?”

Ya tambayi wani namiji wanda daya ne daga cikin masu dafa a abinci a gurin, sai ya nuna masa hanyar da ake zube kayan da aka wanke, Ameer ya nufi gurin yana dubawa sai da idonsa suka sauka akan wukaken dake aje a gafe daya na aiki, ya isa gurin ya zari daya ya juyo sai duk suka ja baya da suna kallon juna irin kallon na gulma wasu na ala ala idan ba a cikinsu zai dabawa wani ba.

“Ranka ya dade wukar nan ta aikinmu ce”

Ameer ya juyo ya watsa masa harara sannan ya fice, kamar zai tashi sama haka ya isa gurin motarsa dake kunne yana ta sauri, ya bude ya shiga yayi reverse ya fice daga gurin. Left side ya fara bi yana tafiya yana duba gefen hanyar, ganin babu abun da yake nema bata isa barin unguwar ba domin hanya ce mai tsawo kuma guri ne da ba a cika zirga zirga da motoci, wannan dalilin ne ya saka mutane ke son restaurant din ne, unguwa ce dake nesa da mutane kuma guri ne da babu hayaniya da ganin mutane barkatai, wani ma har ya shiga yayi abun da zai yi ya fito ba za a san ya shigo ba, saboda yanayin gurin da kuma unguwar. Ya juya kan motar ya dawo right side yana gudu sai yana kallon gefen titin addu'a kawai yake a ransa Allah yasa ya ganta, kuma ya san zai ganta matukar ba wani gurin ta shiga ba, ko kuma wani ya rage mata hanya.

Humairah na tafiya gefen titi wata motar aka rage gudun motar ta dawo daidai ita ta tsaya, tsoro ta dan ji domin bata san waye cikin motar ba, tsayawa ta yi tana kallon bakin gilashin da aka sauke, ga mamakin Ameer ne matukin motar, da kai yayi mata alama da ta shigo ciki sai taja tsaki ta dauke kai ta cigaba da tafiyarta, tuka motar yake a hankalin yana binta ganin kamar bata fahimci abun da yake nufi ba ya saka shi mika hannu ya bude mata front seat. Sai ta tsaya kamar zata shiga sai da ta ga shi ma ya tsaya sannan ya kama murfin motar ta rufe da karfi har sai da yayi kara kamar zai cire, ta cigaba da tafiyarta ya sake binta ya bude mata gambun motar.

“Get in”

“Ba zan shiga ba, har ka isa me kake nufi da na shiga an fada maka ni yar iska ce? Ko kuma ni an fada maka ban san ciwon kaina ba? Ko an fada maka tsoronka nake? Ba zan shiga ba, aiki ne daga yau na zan sake yi ba, balle har ka wulakanta ni”

Jan motar yayi ya matsa gaba ya faka yana jiran ta karaso, ita kuma ta ayyana a ranta cewar ba zata shiga motar ba ko da kuwa hankata zai yi. Sai dai abun da bata sani ba ya shirya mata, tana isowa gurin ya bude motarsa ya fito ya zagayo gefen da take.

“Wai Ameer me ka dauki mutane ne? Bayinka? Ka rika juya su yadda kake so kana cilasta kowa yin abun da ka ga dama? Ni abun kunya ne a gareni a gan ni a motarka, domin ni ma zai ayi min daukar yar bariki...kuma... ”

Bata karasa ba ya dago wukar dake boye a hannunsa ya nunata saitin wuyanta.

“Ke idan kika fara zuba baki san ki tsaya ba, idonki yayi tsauri baki tsoron kowa”

“Ina tsoron wuka Ameer dan Allah karka kashe ni”

“Shiga mota or will cut your throat”

“Toh”

Jikinta na rawa ta bude motar tana ta kallon titin ko zata samu wanda zai taimake ta, motoci biyu da suka wice ba su damu da kula da abun da le gafen titi ba balle har a kawo mata dauki, haka ta shiga motar ya rufe sannan ya zagaya, wani bangare na zuciyarta na raya mata cewar ta fita ta gudu kamin ya shiga sai dai ina tsoro irin na masu bakin tsiwa ya hana ta aikata komai har ya shiga motar ya fara tuki fa hannu daya, dayan hannunsa kuma yana rike da zumgurariyar wukar ta yankan nama.

“Dan Allah karka cutar da ni Ameer? Me na maka?”

“Baki san abun da kika yi ba?”

“Toh ka yi hakuri ba zan sake ba, yaushe kuma ka koma yin dabanci ba a san yayan masu arziki da wannan dabi'ar ba”

“Yau na fara, kuma kina yin wasa zan yanka wuyanki ko na fada cikinki kin ga dai ba za ayi min komai ba ko? Idan na kashe ki an kashe banza dan haka ki bini a hankali”

“Toh... Yanzu gida zaka kai ni?”

“Saboda gani direban ki ba”

“Amman Wallahi tallahi na rantse da Allah ni ban taba iskanci ba, dan Allah karka lalata min rayuwa Ameer”

“Ni na taba iskancin, negative mind daman shi ne a ranki, you should be praised kin shiga motata ma ni me zan yi a jikinki?”

“To miyasa zaka dauke ni a motar kana ta tafiya me zaka yi min? Dan Allah karka yi tsafi da ni toh”

“Dodona baya son irin jininki”

Cikin dabara ta kai hannu ta murda gambun motar da zimmar ta bude sai ta ji shi a rufe.

“Na shiga uku na lalace”

Ta fara kuka, hankalinta ya tashi sosai domin bata san manufar Ameer na yi mata haka ba, kai ta zai yi wani gurin ya aje ko ya hukuntata akan abun da ta yi ko kuma wani abun zai mata.

“Ni zan iya baka hakuri a bainar jama'a idan dan abun da na yi maka ne, zai saka ka hukunta ni, dan Allah dan darajar iyayenka ka yi hakuri”

Kallonta kawai yayi ya dauke kai, yadda ta makure a cikin motar ta zama marainiyar gaske duk sanyin ac motar ita gumi take ga idonta ya zurma kamar zuru. Faka motarsa yayi gefe ya bude ya fita rike da wukar da kuma wayarsa da key motar da Daddy ke kira. Yana piciking kiran Daddy ya tambaye shi.

“Kana ina Ameer”

Ya juya kalli inda yake.

“Wani guri Daddy?”

“An fada min ka shiga har gurin da ake dafa abinci ka dauki wuka, me zaka yi da ita?”

“Wani zare na yanke a jikin tayar motata”

“Ameer ba ka min karya karka fara, ni nasan ko me zai faru ba zaka yanke zare a jikin motarka ba”

Yayi dariya.

“Daddy maganar gaskiya wata yarinya na yi ma barazana da ita”
Chapter 71 · 0% Book details