← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 176

Sashe 131

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Akwai abun da ya faru ne? Kamar kina cikin damuwa”

Ta dauke idonta daga barin kallonsa ta cigaba da cin abincinta. Sai ya leki fuskarta cike da damuwa

“Waira...”

Ta dago ta kalleshi.

“Na zo miki da labari mai dadi amman na ga kamar baki cikin yanayin da ya kamata na gabatar miki da shi, mw ya faru? Me yasa kike kallona da sad face? Wani yayi miki wani abu ne?”

“Na fada maka? Ka tashi ka yi fada da Ummi da Ya Maleek? Saboda ni? Har ka saka Ummi ta fara tunanin mayar da ni gida?”

“No Waira ba zan iya jure ganinki a cikin damuwa ba ne, shiyasa kuma suna son daukeki daga nan su kaiki waje na saboda su raba mu, and i promise you ba za a maida ke gida ba, idan ma an kaiki gida toh mun je neman gafararsu ne, duk abun da nake yi ko zan yi saboda ina sonki ne, bana son na ganki a cikin damuwa, hawayen da na gani a idonki su bata min rai shiyasa hankali ya gushe har na yi fada da Maleek amman ban yi da Ummi ba”

“Amman ka saka Ummi ta mari Ya Maleek”

“Ba ni na ce ta mareshi ba, ita ta mareshi dan ra'ayin kanta, waya fada miki duk wannan?”

Sai ta samu kanta da kasa furta cewar Maleek ne saboda kar ta haifar da wata fitinar a tsakaninsu.

“Tell me”

“Ba zaka sake yin fada da kowa ba saboda ni, tafiya zan yi”

“Ina? Ba zaki tafi ko'ina ba, kuma ba zan iya miki alkawarin ban sake fada da kowa saboda ke ba, domin ba zan jure ganinki da wani ba, Waira ina kashinki”

“Kishi? Me yasa Sulem ba ya kishina ko Ya Maleek ko Mahmood sai kai?”

“Saboda sonki nake yi, i love you Waira with all my heart”

“Su ma suna sona ai”

“Ba irin wannan son nake miki ba, nawa yana da banbanci da na su”

“Irin son da kake yi ma Ya Nimra?”

Gabansa ya harba da karfi a lokacin da ta ambato Nimra kuma ta kwatanta da kanta. Ya kama hannunta ya rike.

”No Waira ina son ki ne tsakani da Allah irin son da zamu gina wata kalar duniya mai dadi mu rayu a cikinta, so na aure wanda zamu kafa zuri'a mu yi yaya kamar Ummi”

Ta janye hannunta tana girgiza kai.

“Ba irin wannan ba dai, ni bana yi ma kowa irin wannan soyayyar”

“Amman kina so na ai”

“Ina sonka ina son Maleek ina son Sulem ina son Mahmood ina son Jabir ina son Nimra ina son Ummi ina son duk wani mai kyautata min”

Ya hade yawu da karfi tana ta tunanin ta inda zai iya sarrafa halshensa ya karkato da tunaninta ta fahimci inda ya dosa. Ta mike tsaye tana jan kujera baya sai shi ma ya mike da sauri

“Waira dan Allah karki kalli abun da ya faru Nimra ki saka shi a ranki, kuskure wanda kowa yana iya yi haka ne?”

“Amman kai ka shirya komai ai, kuma saboda kai Ummi ta mari Ya Maleek, ta yi fada da shi hakan yayi min ciwo duk saboda ni”

“Waira please understand me ina sonki tun a lokacin da na fara ganinki a school bus”

“Ba lokacin da ka fara ganina a daji ba?”

Kamar wanda ya firgita haka yake kallonta, sai kuma ya daga mata kai.

“Yeah tun a dajin”

“Ba auren yarenmu, balle kuma ni ko cewa aka yi ana so na mutuwa ake, kuma ba ma auren wanda ba kabilar mu ba”

Ya matsa daga jikin kujerar ya rumgumeta.

“Waira ina sonki a haka zan iya aurenki ko da zan mutu ne, i love ban taba son wata mace ba sai ke, ba ki san yadda nake ji a zuciyata ba please ki daina min haka”

Ta fara kokarin raba jikinta da shi.

“Ya Maleek ya fada min Addinin musulunci ya hana taba jikin mace da bata ka ba, amman kai kana yi shi kuma ko hannuna baya rikewa saboda yana da tsananin biyayya da taka tsantsan ga addininsa”

Ya sake ta a dolensa yana kallonta idonsa cike da tsoro kamar yaro da ubangidansa.

“Amman ke ai wannan hukuncin be hau kanki ba, har sai kin musulunta”

“Amman ai kai ka sani, kuma zaka samu zunubin haka ne?”

Ya daga mata kai kamar wani soko.

“Ameer kai ba mutumen kirki ba ne, mai cutar da wata har sai da ta rasa rayuwarta, mai fada da mahaifiyarsa, mai barin wata a daji har sai da ta kusa rasa rayuwarta, mai fada da dan'uwansa, mai aikata abun da addininsa ya hana, ni bana sonka, ni ba irin Ya Nimra ba ce, ba zaka min irin abun da ka yi mata ba”

Ta juya ta sauka daga dinning din, shi ma ya juyo yana kallonta jiki a mace kamar wanda aka zarewa kuzari. Hanne da bakuwarta suna satar kallonsa domin suna iya juyo wani abun da Waira take fada.
[7/31, 7:05 PM] My S Line: 68

Dakin Ummi ya nufa da tunani kala kala a ransa da kuma rudani na yadda Waira ta canja masa lokaci daya. Kamar wanda be san abun da yake ba haka ya tura kofar dakinta ya shiga idonsa cike da rauni, fuskarsa na bayyana karayarsa.
Sai da ya isa gaf da gadon Ummi sannan ya tuna be yi sallama ba.

“Salamu alaikum”

“Wa'alaikussalam”

Ummi ta amsa tana kallon cike da kulawa. Maleek dake tsaye jikin Mirror ya kalleshi sannan ya mike tsaye daidai da zimmar ficewa daga dakin, saboda shigowar da Ameer yayi.

“Maleek...”

Ya tsaya cak sakamakon kiransa da Ameer yayi, ya juyo ya kalli Ameer din dake kallon kasa cikin wani yanayi mai wuyar fassara.

“I know bana so na ko son wani abu nawa, na san ba zaka taba son abun da nake so ba, kuma ba zaka so na samu farinciki ba”

Ameer ya dago ya kalli Maleek.

“But Waira is different ita rayuwa ta ce, ina sonta irin son da kalamai sun yi kadan su bayyana alkali yayi kadan ya rubutu, ka bata a gurin kowa ka saka kowa ya tsane ne amman ban da Waira, kokarin bata alakarmu da nuna mata ni ba mutumen kirki ba ne, dan Allah ka bari, idan baka son zama a gidan nan zan iya tafiya na bar gidan, zan iya kaucewa duk wata hanya da zaka gan ni, amman please ka bar alaka ta da Waira, na san kana min kallon mutumen banza ko kuma makiyinka saboda abubuwa da suka faru, amman Waira da gaske nake, kai kasan idan ina son abu bana bashi baya, kuma idan na sakawa abu gaba ba zan saurara ba na maka magana ne saboda ina son abu ya samu ta masalaha. Kana da Abiey a raye, ka rayu da Ummi tun tashinka har yanzu baka rasa komai ba, so please ka bar min wannan ni na na samu farinciki, domin a yanzu farincikina yana tare da Waira...”

Yana gama fadar haka ya mike tsaye ya fice daga dakin ba tare da ya ce da Ummi komai ba. Ummi ta bishi da kallo kamin ta kalli Maleek dake tsaye.

“Me ka yi? Yaushe zaku fara son junanku Maleek? Akan me zaku raba hankalinku kirkiri kiyayya saboda Mace? Ba kasan zaka iya rasa Waira ka samu wata ba, amman ba zaka rasa dan'uwa ka sake samun wani ba, kar soyayya ko kiyayya ta rufe maka ido ka nemi cin amanar dan'uwanka, na san kana son Waira amman kokarin bata dan'uwanka a gurinta ba abu ne mai kyau ba”

Yana son yayi magana zuciyarsa na raya masa ko da ya bude baki yayi magana Ummi ba zata fahimce shi ba. Saboda haka yayi shiru ya kuma tsaya a gurin ya kasa tafiya.

“Baka tashi nuna kana sonta ba, sai a lokacin da shi ma ya ce yana sonta? Kuma ba za ku iya bari ta zaba a tsakanin kai da ita ba, sai ka soke dan'uwanka a gurinta”

“Ni ban soke shi a gurinta ba, ba zan hana ya sota ba, ba kuma za hana ita ma ta so shi ba, amman ba zan bari ya fitar da ita a gidan nan ba, bayan duk abun da yayi mata a baya”

“Yayi mata ko kuma yayi ma Nimra? Ina zaton saboda haka ne kake rike da shi a ranka, idan har wani zai rike wani da laifi ba za a zauna lafiya ba, kai ka manta irin abubuwan da ka yi min kuma ka yi ma kanenka, ka manta yadda kake nuna min kiyayya, ba dama na yi magana da kai ko na zauna a kusa da kai?”

Yayi shiru yana jin wani iri

“Da ace ban yafe maka na manta ba, kana tunanin zan zauna da kai kamar haka? Kowa yana laifi Maleek kamar yadda ni ma na yi, amman aka daga kafa, domin Allah ma yana yafe mana idan muka yi kuskure”

Ya sauke kansa kasa tare da ajiyar zuciya sannan ya yi walking out slowly kamar mai abun kunya. Yana janyo kofar dakin ya rufe Waira ta iso gurin tana rike da hannayenta idonta yayi ja sosai alamar ta yi kuka, suna hada ya sauke idonsa daga barin kallonta ya sauka kasa, binsa ta yi da kallo har sai da ya kusa sauka sannan ta kira sunansa.

“Ya Maleek”

Ya tsaya sai dai be juyo ba, ta kawa ta yi ta sauka kasa ta tsaya gabansa.

“Zaka kai ni gida Please”

Ya kasa ce mata komai kuma ya kasa dauke idonsa daga barin kallonta.

“Ina son na tafi gida ne, zan gane hanya yanzu”

Be ce mata komai ba ya dauke kai ya sauka kasa ta bishi da kallo kamar ta san zai waigo ya kalleta, kallonta sosai irin na tausayi tunaninsa na bashi cewar saboda shi ne zata bar gidan. Yana kokarin juyawa ya cigaba da tafiyarsa idonta ya fara zubar da ruwan jini, ba tare da ta sani ba, da sauri ta hauro yana kallonta.

“Idonki Waira jini”

Ta kai hannu ta taba hawayen da suka zubo mata ta duba sai ta ga jini.

“Wani abun zai faru, wani abu marar dadi”

“Kamar ya?”
Chapter 131 · 0% Book details