← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 176

Sashe 121

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

He don't want to argue with her because he don't has that energy now, jikinsa rawa yake kamar yadda zuciyarsa ma take ra rawa gaba daya tunaninsa ya rikice kuma ba zai iya fadar dalili ba, kawai dai shi dai ya san baya son Ameer ya kusanci Waira balle kuma aure ya hada su. Kamar wadda aka daurewa baki haka yayi shiru ya nufi kofar fita falon, Ummi dake ta kafa masa hujjoji ta bishi da kallo ganin kamar hankalinsa baya gurinta, kamin ya shiga motarsa har gumi mai zafi ya jika shaddar jikinsa ya shiga ya zauna ba tare da ya tashi motar ba, duk wani hanzari da yake na fita daga gidan zuwa gurin da yake ta uzuri sai ya kau hausawa suka ce sawun giwa ya take na rakumi. Ya kusan minti talatin a cikin motar zaune kamar ruwa sannan ya rufe motar ya saka key din ya tashi motar. Tukin kawai yake ya manta inda zai je, titin ya bi ya kai karshensa ya dawo ya sake kaiwa karshen ya sake dawowa haka yayi ta wuce gidansu yana zagayo kamar wanda aka yi ma sihiri. Can kuma ya faka motarsa kusa da gidansu ya ciro wayarsa ya kira Abiey domin shi kadai ne mutumen da yake jin zai iya fadawa wannan maganar au tattauna kuma ya fahimce shi. Ringing biyu kamin ta yi na uku Abiey ya daga.

“Son”

“Abiey akwai matsala”

“Kamar ta me?”

“Wai Ameer yau ya fadawa Ummi yana son ya auri Waira imagine?”

“What? Bayan duk abun da yayi? Ita kanta yarinyar ya manta yadda ya barta a wulakance yanzu an dauke an gyarata ta yi kyau shi ne zai ce zai aureta”

Maleek ya tashi zaune da kyau yana jin yadda Daddy ya tabo masa inda yake masa kaikaiyi.

“Yauwa Abiey dadina da kai kana da sauri fahimta, ni abun ya bani mamaki kuma ya ba ji tsoro jikina shaking kawai yake gaba daya tunanina ya jagule bana son na ga abun da zai cutar da yarinyar nan ko kadan, amman Ummi bata ganewa sai fadar take wai ba yadda nake tunani ba ne, gaba daya na rikice Wallahi na ma rasa kalar tunanin da zan yi, amman gaskiya ba zan jure ganin Ameer tare da Waira ba innocent soul like her”

Daga dayan bangaren Abiey yayi murmushi domin yana iya fahimtar abun da ke zuciyar dansa ba tare da shi dan ya sani ba, Abiey ya dade da karantar abun da ke zuciyar Maleek ba dan shi Maleek din ya fahimci zuciyarsa ba.

“Idan kuma mahaifiyarka da gaske take fa? Ameer ba zai cutar da Waira ba? Kuma idan muka yi bincika muka tabbatar da haka zaka yarda mu aura masa ita?”

Kamar an kashe mutu haka Maleek yayi shiru a wayar ko numfashinsa ba aji Abiey kuma yana testing dinsa ne domin gane ko daidai a ma'aunin da ya dora ďansa Maleek. Rasa yayi me zai ce idan yace ko a haka be be dace da aurenta miye hujjarsa? Saboda ya wulakanta ta could be enough? Idan kuma babu hujja zai iya yiyu ace ya tsani Ameer din ne.

“Abiey yarinyar nan bata dace da aure a yanzu ba, ni da zaka dauki shawara kuma ka amince ka saka Ummi ta amince zan fitar da ita waje ta yi karatu mai kyau kamin ta dawo ta yi hankali ta san kanta then by that time tana da yancin zabar abokin rayuwa, amman a yanzu ko ba Ameer ba ni bana son ganin kowa a tare da ita, ita fa bata san wa take so ba, kalli yadda ta rika waken tana son Shuraim a baya sai ka dauka saurayinta ne, idan wani ya samu irin haka ai sai iya amfani da weakness dinta ya cutar da ita, bayan duk abubuwan da ta yi going through”

“Maleek”

Abiey ya kira sunansa a natse.

“Na'am”

“Umminka ta san ka kira ni?”

“Okay don't tell her, karka ma nuna mata mun yi waya, maganar Ameer da Waira kuma ka barta a hannuna Waira tana karkashin iko na ne a yanzu, that's mean nine jagoranta a yanzu, and na manta ma ban fada maka ba, tun kwana baya na saka a bincika min garinsu ko za a samu danginta”

“Okay”

Maleek ya fada sannan ya sauke wayar yana dan jin sassauci a ransa, dazun kan jin yake kamar ya cire zuciyar daga kirjinsa ya jefar tsabar bakinciki da rudani. Gallary wayarsa ya shiga ya kama hoton Waira da ya dauke ta tana bachi ya sakar mata ido kamar wani maye, can kuma ya kai hannunsa yana shafa screen din.

“Yadda kike da kyau nan kika fada hannun Ameer ai kin shiga uku, yana gama abun da ke kudirinsa zai maida ke karamar bazawara, kara dai idan kika wayo a aura miki mutumen kirki wanda ya san mutumcinki, ba mamaki ma wannan kyau naki ne yake rudarsa”

Magana yake da kansa yana jin cewar Waira da wani mutum mai mutumcin da sanin ya kamata ta dace ba Ameer ba. (Ni kuma na ce Maleek har yanzu baka san ka fada ba? Hmmm muje dai zuwa mahauci ya hau kura)

AMEER POV.

After yayi dropping Humairah ya nufi gurin friends dinsa he spends time with them sai bayan Sallah Isha'i ya nufi gidan Daddy. A al'adar da ya daukarwa kansa a yanzu yana shiga gidan fuska a not like can baya da yake musu yadda yake so. Teema ce amsa nasa sallamat da yayi domin ita kadai ce a falon.. Tsabar farinciki da murnar da yake ciki sai ya isa har inda take zaune ya ja mayafinta.

“You know Daddy na yawan fadar na yi aure ko zaku bi sahu ko? To nidai am already dan haka sai ku fito da na ku”

Ta wara ido with full of surprised ta ce.

“Da gaske? When? Wace lucky girl ce wannan?”

“Za ku ji a gurin Daddy”

“Wow I'm so happy”

Ta mike tsaye cike da murna tana kiran Mummy.

“Mummy sauko ki ji Mummy Mummy”

Ameer yayi saurin rufe mata baki.

“Keee sirri ne wannan daga ni sai ke, bana son kowa ya ji, idan ma wani zai ji to zai fito daga bakin Daddy ne”

Ta daka tsalle tana murna.

“Okay shikenan ba zan fada ba”

Murmushi yayi ya nufi upstairs hakoransa basa rufuwa saboda farincikin da yake ciki, gaba daya a yau ji yake kamar an masa kyautar Waira. Ya shiga wanka yana murza sabulu a jikinsa yana rausayawa yadda zai rayu da Waira yake tunani, one day ace tare za su yi wanka, gata ta iya zuba shagwaba yadda zata narke masa a jiki tana kuka yake da raya a zuciyarsa. Ya fito wanka ya fada saman gado kamar wani karamin yaro ya saka tawul ya goge kansa. Ya gama shiryawa ya tsaya gaban madubi yana kallon kasan ya dauki wayarsa yana yi ma kansa selfie, a yanzu kam ya yarda son Waira ba kadan ya kama shi ba, domin soyayyarta na kokarin maida shi wani karamin yaro, shi da yake ganin ya fi karfin karamar yarinyar yar under 20yrs. A yanzu ya yarda soyayyar gaskiya bata bukatar ado, kuma babu ruwanta da kyau ko muni, haka ma babu ruwanta da talauci ko arziki matsayi ko asali, kamin son Waira ya kama shi babu irin dokokin da be gindayawa soyayyarsa ba amman a yanzu ya mantasu gaba daya babu ko sharadi daya da ya gindayawa kansa.
Ya shiga bangaren Daddy yana ta zuba kamshi kamar kullum, fuskarsa har annuri take saboda farinciki da yake ciki. Daddy ma kallo ďaya yayi masa ya fahimci haka, sai kuma ya jidadin daman baya son yin maganar da shi a cikin wani yanayi na bacin rai.

“Fuskarka sake kamar ka san Mummy ta maka favorite dinka”

“Kai kace ta yi min? Ko kuma ita ta yi da kanta”

Daddy ya daga hannunsa a kokarinsa na gyara hannun Egyptian Jallabiyar dake jikinsa saboda ya ji dadin cin abincin na dare da kyau.

“Ni na ce ta girka maka, saboda ina da special abu da zan fada maka kuma zan roka ka min, and i hope ba zaka ce min aa, na yanke shawara ne ba tare da saninka ba, sai dai ban yi hakan dan na bata maka ba, sai dan ina ganin zai taimaki rayuwarka, domin abu ne da na dade ina jira, kuma na ga kai kamar baya gabanka dan haka zan matukar farinciki idan ka amsa min, sai dai ban ce ka amsa a dole ba, domin ka san na fi kowa son abun da kake so, ina son farincikinka fiye da komai”

Ameer yaja kujera ya zauna gabansa ya soma faduwa zuciyarsa na raya masa kamar Daddy zai gabatar masa da wanda be zata ba ne a matsayin wanda zai aura, ba dan ya san wacece ba, sai dan ya fahimci kamar hakan din ne duba da kalaman da ke fitowa a bakin Daddy. A take yaji kamar an datse masa rabin jindadin da ya shigo da shi gidan, a kokarin na ganin ya kawar da tunani ko bukatar Daddy yayi yunkurin yin wani abu.

“Ina tunanin babu wani abun da zaka bukata ko ka gabatar min na ce maka aa ko da kuwa zai cutar da ni, balle kuma na san ba zaka so abun da zai cutar da ni ba, zan baka dama ka fara saboda ka gabatar da cewar kana son magana da ni tun a jiya da safe, amman nima ina da maganar da nake son na fada maka mai muhimmanci”

Daddy yayi masa alama da hannu.

“Go ahead you first..”

“No Daddy ai ka riga ni”

“No ina saurarenka ai kai ka fara”

“Amman ni ne babba dan haka na baka umarni ka fara fada min”

Ameer yayi murmushi, sannan ya dauki plate ya bude abincin ya fara zubawa.

“Daddy idan baka manta ba, last year da aka yi rigima da Maleek da kuma kanwarsa Nimra akan wata yarinya da aka gani bayan motarsa har na ce ban santa ba ka tuna?”

“Ai ban manta ba go ahead”
Chapter 121 · 0% Book details