← Book details Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 176

Sashe 112

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa sannan ta dauki kofin tea ta ta bar dinning din domin ta gama bata karin, a nan Waira tace waye tv na ba Maleek, kallonsa take kamar zafa fada cikin idonsa, duk dagowar da zai yi da wani motsi yana kan idonta ta ma kasa taba komai a abin karyawarwa da Ummi ta aje mata, tun be kula da kallon ba har jikinsa ya bashi cewar kallonsa take, dan haka ya dago idonta da nashi suka yi tarayya da juna, a madadin ta dauke idonsa sai ta cigaba da kallonsa. Zuciyarsa ce ta fara raya masa kallon da take masa ba na Allah da Annabi ba ne, dan haka ya sake kallonta.

“What?”

Ya tambaya da wata murya can ciki, sai ta dauke idonta domin bata da amsar bashi. Kadan ta sha tea ta mike tsaye tana duba agogo dakin dake nuna 7:30am.

“Ummi zamu wuce makaranta, Ameer be tashi ba?”

Maleek ya hade tea dake bakinsa da karfi, yana jin kamar an daka masa wani mashi a zuciya, why ma ya zauna yana karyawa at this early morning abun da ba halinsa, mikewa yayi tsaye yaja kujera baya ya fice daga dinning din.

“Be farka ba, ni kuma na kyale shi yayi bachinsa ne saboda shi ne first bachinsa a gidan nan, kuma idan ma ya farka this time around me zai yi? Ai kara yayi ta bachinsa, idan ya farka zamu tafi tare anjima na duba matar nan da ta yi accident, shiyasa na hada komai tun a yanzu kuma ina son kamin ya farka na gama shirya masa komai na karyawa even though ban san favorite dinsa ba”

Ummi ta fada tana dire flask din ruwan zafi daya banbanta da sauran Flask din da suke gurin. “Zan tafi na san school bus ta iso a yanzu”

Ummi ta zagayo bangare da Waira take tsaye ta sumbanci goshinta.

“Allah ya miki albarka a dawo lafiya, ki dauki lunch box dinki, na ga baki ci komai ba ma”

“Okay”

Ta amsa sannan ta dauko lunch box din, kiss din da Ummi ta yi mata yana tuna mata da irin kiss din da Maleek yayi mata a daren jiya. Ummi kuma ta yi tsaye tana kallon Waira fuskarta da murmushi har ta fice, ta juya zata koma kitchen sai ta ji jiri ya kwasheta, ko wane gaba na jikinta ya fara rasa kamar ana dukan kashinta, da sauri ta dafa dinning din ta zauna a hankali har sai da abun ya sake ta sannan ta mike tsaye cike da karfin hali ta nufi kitchen din domin karasa abubuwan da take son shiryawa Ameer.

****** ******** ******* *******

Ummi bata samu zuwa duba matar da Ameer ya fada mata tana asibiti da safe ba, sakamakon kiran da Mummy ta yi masa ta sanar masa ta yi aika musu da breakfast, shi kuma ya sanar da Ummi a lokacin da ya sauko kasa domin yin breakfast. Ganin Mahmood a dinning make him feel uncomfortable, but ga mamakinsa sai Mahmood ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya tashi daga dinning din yana fadin.

“Bari na baka guri ka karya kamin ka saba da mu”

Ameer dai be ce masa uffan ba, ya cigaba da kallon kalolin breakfast din da Ummi ta shirya masa tare da taimakon Hanne.

“Ban san favorite dinka ba, shiyasa na girka wadannan ina fatar za su maka dadi”

Ya mika hannu ya dauki plate sai ta rigashi ta dauka tana tambayar abun da yake so. Da haka ta yi feeding din yaronsa cikin farinciki da jindadi da ya kasa boya a zuciyarta har sai da ta zauna ta saka shi a gaba da kallo har ya gama cin abinci.
Dakin da zai iya kira da shi ya shiga ya yi wanka ya shirya sannan ya fito falon jiran Ummi, a kokarinsana rage zaman banza ya saka shi tashi ya fara zagayawa a falon yana duba kofafin da suke falon da kuma ta inda suke bullewa, ya leka Kitchen da kofar baya, tsakar gidan dake gefen hanyar dinning ma sai da ya duba sannan ya fito compound yana kallon tsarin gidan. Shi dai ya san zai daurewa kansa ne kawai ya koyawa zuciyarsa a zaman inda bata sani ba har ta saba, domin rayuwa a inda baka tashi ba, da kallon mutanen da baka sani ba a matsayin iyayenka abu ne da sai an jure. Isarsa gurin expensive car dinsa yayi daidai da fitowar Ummi ciki shiga ta alfarma. Kamin ta karaso gurin ya kawa motar key ya bude mata back seat yana jiran isowarta. A take murmushin ya fadada fuskarta wannan ne second joy dake samu a gurin Ameer bayan cin abincinta driving dinta ma wani abu ne mai muhimmanci a gurinta. Ta shiga motar ta zauna ya rufe ya bude side dinsa ya shiga yayi ma motar key.

“Mu tsaya a wani gurin ina son na siye musu wani abu”

“Karki damu suna da komai a asibitin”

Ya amsa mata daga haka bata sake magana ba, shi ma be sake yi ba, yana son ya tambayeta wani abu game da Waira kuma ya kasa. Tafiyar 40min ta iso da su Hikima Hospital, kamin ta bude ta fito ya bude mata sai ta sauko tana jin wani honour, bayan ta fito ya rufe motar ya wuce gaba tana binsa a abaya har suka shiga cikin asibitin. Shi ya fara tura kofar dakin da Tsohuwar take ya shiga sannan ya rikewa Ummi kofar ta shigo, ya maida kofar ya rufe a hankali sannan ya taka ya isa gurin gadon da tsohuwar take Humaira ta mike tsaye kamar yadda ta saba idan ya shigo bata zama balle kuma yau da ya zo da bakuwar fuska.

“Sannunku da zuwa”

Ta fada cikin girmamawa, Ameer ya amsa mata da hannu yana yi ma tsohuwar ya jiki, sai ta amsa masa hankalinta na tafiya gurin Ummi da ita ma kallon tsohuwar take tana kallon Humairah with shock and surprised. Akwai tsufa da sauyin yanayi na rayuwa a jikin tsohuwar da bata saka ran tana raye ba idan har ta tabbata ita din ce. Sai dai kammanin Bahijjah da Deen da suke a fuskar Humairah suna kokarin karfafa mata tunanin kwakwalwarta. Hannu ta kai ta rike karfen gadon dake gurin kafafuwan Tsohuwar ta runtse idonta gam. Tsohuwar ma kallonta take baki sake tana kokarin tantance abun da idanuwanta suke nuna mata madafar tunaninta take tariyo mata, Ameer ya dan karkarta kadan ya kalli Ummi ya kalli tsohuwar sannan ya kalli Humairah da ita ma kallon rashin fahimta take masa, domin sun rasa gane dalilin Ummi ya rike karfen gadon da karfi ta runtse ido, tausayin tsohuwar ne? Ko kuma na rasa saka ran ciwon ya kai haka ne? Duk ba su canki ko daya ba.
[7/20, 10:33 PM] My S Line: 58

“Ummi are you okay?”

Ameer ya tambaya yana kallonta, kamar wadda ta tsorata haka ta bude idon da sauri, hawayen dake makale a idanuwanta suka samu damar saukowa saman fuskarta.

“Bismillah zauna a nan Hajiya”

Hunairah ta fada tana kallonta domin ta fahimci ita ce matar da Ameer ke bata labarin tana ikirarin ita uwarsa cw ta hanyar sunan da ta ji ya ambata kuma ta ganta a lokacin da suka zo tafiya da Nimra. Ummi ta cira kafa ta taka sai jiri ya dibeta ta yi baya kamar zata fadi har sai da Ameer yayi hanzarin rikata.

“Are you okay”

Ta dan kallesa jin wani abu mai kamar yana a ido ya sska ta ganinsa dishe dishe-dishe.

“Taimaka min na zauna Ameer”

“Okay”

Ya rikata da kyau, Humairah ta dauko kujerar da sauri ta aje mata, Ameer ya taimaka mata ta zauna.

“Ummi lafiya? Ko ciwon ne ya tashi?”

Ta kalleshi a cikin halin da yake

“Waya fada maka ba ni da lafiya?”

“Waira ta fada min komai”

Ummi ta bude baki da dan mamaki sannan ta rufe ido ta bude ta kalli Tsohuwa ta karata da sunan da zai kara tabbatar mata idan ita din ce.

“Hajiya ina Bahijjah?”

Wacce aka kira da Hajiyar ta yi ma Ummi kallon neman sani da fahimta, ita dai ta ga kamar ta san Ummi sai dai kammanin ya canja gaba daya, sai dai mamakin tambayarta ta san Bahijja ya gagara boyuwa a fuskarta.

“Bahijja tana hanya bata karaso ba, amman tana nan zuwa ga yarta nan dai Humairah, Hajiya sai na ga kamar na san ki amman fuskar ta canja”

Humairah da aka nuna ta sakarwa Ummi ido jin an ambaci sunan mahaifiyarta, ga hawaye sai saukowa yake a idon Ummi kamar ba gobe.

“Kin san ni mana Hajiya...”

Kuka ya ci karfin Ummi ta kasa karashe maganar, Hajiya ma ta sake yi mata duba na tsanaki.

“Ko dai Zahra ce Zahra matar Abiey tsohuwar matar Zaharardeen? Na ga fuska amman tsufa ya kai kar na fadi ba daidai ba, shekara ashirin da biyar rabona da ganinta, wata kila ma har da doriya, tun akwai sauran kurciya”

Ummi ta saka hannu ta dafe fuskar tana mamakin yadda Ubangiji yake tsara al'amurransa, ya hadata da kowa ta inda bata yi tsammani ba, tun daga kan Ameer ga kuma Shuraim yanzu kuma ga Hajiya. Cikin kuka Ummi ta ce.

“Ni ce Hajiya, idonki be fada miki karya ba, shekaru sun ja na sani, tun yarana suna tasawa gashi yanzu har sun girma”

“Allahu Akbar ashe Allah zai sake sada fuskokinmu Allah da girma kake”

Fadar Hajiya tana girmama Ubangiji, Humairah da Ameer kam kallo kallo kawai suke domin ba su fahimci komai a cikin abun da Ummi da Hajiyar suke tattaunawa ba. Cikin kuka Ummi ta ce

“Yaushe kika bar Kano Hajiya?”

Hajiyar ta sauke ajiyar zuciya tana murmushin takaici.

“Labari ne mai tsowa Hajiya Zahra, rayuwa ta yi mana wahalar zama a kano, tun bayan rasuwar Malam, sai na zama bani da kowa na kusa ai dangi da yan'uwa, kuma ba abun ka dauko ďan wani ya zauna tare da kai ba, saboda kai talaka ne ba kowa ke son zama kusada talaka ba, ina tunanin ai kin san auren Bahijja”

Ummi ta daga kai tana kuka sosai.
Chapter 112 · 0% Book details