Sashe 173
Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaman Humairah a gidan Nuwaira ya taimaka mata sosai ta bangaren kara kwarewa a kana girki, da kuma sanin yadda zata kula da gidanta. Tun a washe garin ranar da Humairah ta je gidan Nuwaira ta tambaye minene Haila, kuma ita tana nan, a nan fa Humairah ta yi mata bayani dala dala cikin har da yar fahimtarta na lokutan da ake iya daukar ciki bayan gama Haila da kuma wahalar da wasu suke sha gurin ciwon mara duk wata. Hunairah ta sha mamaki sosai jin cewar Nuwaira bata taba yi ba, ta kam ji labarin ance wasu matan baza yi gaba daya, wasu kuma sai sun dade suke farawa wata kila Nuwaira tana daya daga cikinsu har take ce mata ta yi dace domin ance macen da ke dadewa ba ta yi haila ba, sadakinta dabam yake. Wasu mazan kuma basa son wadda bata yi domin wasu kan ce bata haihuwa ita da wadda bata da nono a kirji, sai dai ana samu ko da ba a haila a haihu domin haihuwa na Allah ne.
Ranar da Humairah ta cika sati a gidan tana nunawa Nuwaira yadda ake bude gmail account har a bude account a YouTube domin ta rika kallon karatunka malamai da kuma cigaba da koyon addininta. Humairah take zolayarta wai kila ma ta samu rabo.
“Rabo kamar ya?”
“Ciki mana”
Nuwaira ta wara ido ta shafa cikinta.
“Da gaske? Ya aka yi kika gane?”
“Yoh ni ba zolayarki na ke ba, kuma na ga kin yi fresh ne yau ai”
“Yanzu kenan akwai da a cikina? To kuma ba kin ce wadda bata haila bata haihuwa ba?”
“Ba lallai ne haka ya kasance ba, ana samu amman few kawai dai anfi samun saurin daukar ciki ne immediately after period da zarar miji da mata sun yi mu'amalar aure”
“Kamar ya?”
“Sorry ke ba bahaushiya ba ce to s** nake nufi”
Tana jin haka sai ta gane abun da Maleek yake ta kokarin ta fahimta kenan ta kasa yarda.
“Da gaske ne sai an yi haka ake samun ciki?”
“Eh mana toh a ruwa ake sha?”
“Ni ba zan yarda ba, bana so wannan abun ba shi da kyau”
Humarah ta fara da mamaki kamin ta bushe da dariya.
“Ban gane ba”
“Kawai bana so, ni ba zan yarda, Ya Maleek ma yayi haka ban yarda ba ai, har da fushi yake fa, ni a garin ma ba a haka”
Dariya sosai Humairah ta saka kamin ta gane akwai aiki babba a gabanta na wayar da kan Nuwaira ta wannan bangaren, domin duk mutumen da yayi rayuwa a guri na dabam ba tare da mutanen da za su nuna masa daidai da akasin haka ba dole ya samu kansa a cikin duhun kai, saboda haka bata ga laifin Nuwaira ba, kuma ta yabawa Maleek, tana ganin ta in Ameer zai iya wannan juriyar. Tun daga ranar Humairah bata da labari da Nuwaira sai na yadda zata fahimci hakokin da Maleek yake da su akanta kasancewarsa mijinta. Wannan ya haifar da shakuwa da kusanci a tsakaninsu sosai kuma ya hanasu kewar mazanjensu kamar yadda suka yi tsammani musamman ma Nuwaira da abun ya so hade mata biyu na Ummu da Maleek, gashi shekarunta da tunaninta ba kamar na Humairah da ace bata da wanda zai yi guiding dinta da ta wahala sosai a gidan. A kowane dare Ameer sai yayi waya da matarsa haka ma da dare, idanbe kira ba ita zata kira, kullum safiya sai ta gaisa da Ummi ta yi mata da jiki, da farko kam jikin nata yayi tsanani sosai hankalin iyalanta ya tashi matuka kamin sauki ya fara samuwa su kansu likitocin sai da suka yi mamaki, domin ikon Allah kadai ke iya tsallakar da mai irin ciwonta da ya kai stage dinta, mace da aka bawa kwanakin mutuwa kuma aka cire mata rai daga rayuwa sai gata tana hira da yaranta har da dariya. All zaman da ta yi asibitin na tsawon wata daya yaranta Maleek da Ameer suna tare da ita, Namra ce kawai ta koma gida after ta yi week a garin, farincikin gurin Abiey har ba a magana domin bashi da tashin hankali da tsoro kamar ciwon matarsa, gashi yanzu yana ganin samun saukinta ta hanyar da be zata ba, ya san ba komai ba ne sai addu'a da kuma karin tsayen rayuwar dake da sauran shan ruwa a gaba. Ciwonta is still there amman yayi kasa, date din da suka saka mata na mutuwa ya ce bata mutum ba sai ma karin samun sauki da ta yi. Aman jinin da ta fara yi da canji fata sai suka dauke mata. Nuwaira ma ta yi mamaki a lokacin da take video call da ita tana tambayar yaushe zata dawo.
“Soon sweetheart...”
“I need you Ummi ba zaki mutu yanzu ba”
Ummi ta yi murmushi ta kalli Maleek dake zaune gefenta yana saurarensu ya dago ya kalli wayar ta Abiey dake hannun Ummi. Suna hada ido da matarsa ya kashe mata ido daya sai da ya tabbatar Ummi ba zata gani ba ya leko halshensa ya lashe baki. Ta murguda masa baki ta dan juyar da fuska, hakan ya saka Ummi karkartawa ta kalli Maleek sai ta ga kansa ma a kasa yake ba ita yake kallo ba.
“Nuwaira kina son mala'iku su kona ki? So kike a daure bakinki sai yayi tsawo a ja shi a kasa?”
“Aa”
“Toh karki sake murgudawa mijinki baki, ko musu karki sake masa balle kuma harara da murguda baki na fada miki”
“Toh Ummi”
Maleek ya dago kamar be san abun da yake faruwa ba ya kalli matarsa.
“Me kika yi”
Ummi ta mika masa wayar gaba daya, sai ya karba ya mike tsaye ya fice daga dakin.
“Idan na dawo sai na cige wannan bakin naki”
Sai ko ta turo masa bakin.
“Gashi nan ka fara tun yanzu ma”
Ta fara dariya sannan ta masa gwalo.
“Ya Maleek”
“Na'am Nulik dita me kike so?”
“Na ji Humairah ta ce wai Ameer zai dawo cikin satin nan saboda jikin Ummi yayi sauki sosai”
“Haka ne gaskiya ta samu lafiya, kuma daman haka muke ta fata”
Ta dan marairaice fuska ta fara masa shagwaba.
“Ya Maleek kai yaushe zaka dawo?”
Ya shafa kansa ya dan daga kansa sama ya sauke sannan ya nufi wata kujera ya zauna.
“Ba rana maybe sai an sallami Ummi gaba daya, ba kin ce baki so na a kusa da ke?”
“When na ce haka when?”
“Toh abun da kike min ai kamar kina cewa haka ne a gurina, idan na matsa ki ce kin fasa aurenki haka nan ake so? Wadda kake so komai ba mallaka masa kake ba? Ki san yadda kika birkita tunanina ba na zo nan ina ta tunaninki”
“Toh ai ni ban sani ba ne amman Humairah ta ce... ”
Bata gama ba ya tambaya da karfi.
“Ta ce me? Fada mata kika yi? Nuwaira baki san mata da miji suna da sirri ba”
Wani sakaka ta yi tana kallonsa.
“Ba duka na fada ba”
“Kin kashe ni, ta san komai yanzu”
“Amman ta fahimtar da ni ai, kuma ta yi min karin haske akan period kuma she teach me yadda zan kula da gida na zama full house wife”
“Tana jna yanzu?”
“Bachi take fa, yanzu karfe sha biyu na dare ne”
“Oh Really okay ke ma ki tafi ki kwanta bana son ki gaji”
“I will amman yaushe zaka dawo i miss you kuma idan Humairah ta tafi ni kadai ce na gidan, wannan big house ba zan iya zama”
“Idan na dawo zaki yarda mu zauna lafiya komai na ce ki yi babu musu?”
Ta daga masa kai.
“Zan duba na gani, give me a kiss sai ki je ki kwanta”
Ya mika bakinta kamar yadda suka saba ta sumbanci wayar, shi ma ya kai bakinsa ya sumbanci screen din wayar sannan ya furta mata i love you cikin rada.
“I love you too good night”
“Sleep tight my princess my happiness”
Ya masa murmushi tare da daga masa hannu sannan ta kashe wayar. Sai da ta shiga Kitchen ta sha ruwa sannan ta nufi dayan dakin da suke kwana ita da Humairah domin Humairah ta fada mata dakin mai gida ba a shigar da kowa kuma ba a barin kowa ya kwanta daga ita sai shi, wannan ya saka suke using dayan dakin domin duka three bedrooms din sai da Abiey ya suka mata su da kaya. Ganin Ummi na ta kara samun sauki ya saka Abiey ya umarce Ameer da Maleek da su koma gida, idan ma suna son dawowa kamin Ummi ta bar asibitin sai su dawo tare da matansu. A tare suka yi booking flight kuma a tare suka iso Lagos sannan suka kama hanyar Abuja. Ranar da za su dawo Humairah da wuri ta bar gidan ta koma gidan mijinta domin gyara na su muhallin da kuma girka masa abun da zai ci, sai dai duk abun da ake Nuwaira bata san tare da Ameer Maleek zai dawo ba, ita kam tana zaune a nata gida bayan ta gyara iya inda zata iya ta dafa shimkafa da ganye ta ci, ta dawo falo ta zaune rike da kofinta na lemu, ta dauki remote ta canja channel can kuma ta ji kallon ya isheta sai ta kwanta saman kujera ta turo baki gaba, babu wanda take hangowa sai Humairah Ameer ya dawo ba zata kwana ita kadai a gida ba, amman ita zata kwana ita kadai a wannan babban gidan da bata gama sake jiki da shi. Tashi ta yi zaune ta nufi dakinta ta zauna saman gadonta ta dauki wayarta tana shirin kiran Maleek sai gashi ya kirata sai da yi picking da sauri tana share hawayenta.
“Toh kuma yanzu kukan me ye?”
“Ni ba zan iya kwana a gidan ni kadai ba?”
“Saboda me?”
“Tsoro nake ji”
Ya daga wayar hannunsa yana juyawa harabar gidan ta inda kofar falon take.
“Wannan gidan kike tsoro”