← Book details Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 69

Sashe 7

Tsaka Mai Wuya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ba yadda ba su yi su barmu mu shiga ba ammh Su ka ki, bayan kuma suna ta bin mu da mugayen mganganu, Har hankulan mutane ya fara dawowa kanmu. Kallon Ramatu kawai nayi ina Fadin"Ramatu ku taho mu tafi kawai. Allah ya bashi lafiya" Kasa min mgana ta yi, ta tsaya tana ce min"Hasiya wannan abun da nayo fa? Sai da na kalli kwandon hannunta sannan nace"Ki ba wa Musbahu in kuma zai zama matsala mu koma da shi" Ba ta yi musu ba taja Musbahu gefe ta mikamasa kwamdon hannunta bayan sun yi mgana, yana ta bata hakuri tace bakomai, su Adda fati tayi ma mgana yasa muka fito daga wajen da niyar Tafiya. Matan gidanmu suna baya suna ta Gulma daman abunda ya kawosu kenan. A haraban asibitin muka had'u da Sahura da yan gidansu kallo kallo akayi tsakanimmu an rasa mai mgana, ganin tare take da wata yar Dattajuwan Mata Ramatu ke shaidamin Innar Salisu ce. Ina kallonta suka gaisa da Inna talatu da su Adda Fati cikin sakewa daga yanayinta yasa na Fahimci zatayi saukin kai ba kamar sauran ba. Cikin Fara'arta tace"kun samu ganin Salisun? Inna talatu tace"A'a ba'a barmu mun ganshi ba" Cikin mamaki tace"ah kuma la'asar ai ta gota. Lafiya kuwa.? Adda Fati Zatayi mgana Inna Talatu ta rike mata hannu tana fadin"Gudun Fitine kawai. Ayi masa sannu Allah ya bashi lafiya" Ni dai sai na samu kaina da Jawo hijabina ta sama ina Rufe fuskata. Nima yanzu kunyar nuna Fuskata nake yi ga Mutane da gaske ni din Annaba ce ko kuma nace gobara Daga kogi mganinta sai Allah. Inaga ta Fahimci mganar Inna Talatu yasa tayi ajiyan zuciya kafin tace"Rayuwar ne sai hakuri. Abubuwwn duk sun rikice ni na rasa ina zan kama. Ku yi hakuri don Allah gobe ma za'a wuce da Salisu kano ayi masa Daurin asibiti. Ku yi hakuri da duk abunda zai biyo baya don Allah" Inna talatu tace"Bakomai Allah yasa ayi a sa'a" Ta amsa da Ameen sannan muka wuce itama ta wuce, Tunda Sahura da gayyarta sun yi gaba suna harare harare da yada mganganu. Har muka isa gida ban tofa komai ba duk da ana ta maida zence a cikin motar. Amma ma Adda fati ta zayyanemata komai ta sauke numfashi kafin tace"Allah ya kyauta" Kowa jiki ba Dadi' haka Ramatu ta tafi tana kara bani baki nace mata bakomai Inna Talatu ne sai dare ta tafi gida Adda Fati kuma mijinta yazo Daukanta bayan ya shigo ya gaida Amma. Har ya bata dubu daya. Washegari wajen misalin karfe sha daya na Safe sai ga Musbahu abokin Salisu ya yi sallama da ni a kofar gida. Daman tunda naji ance Musabahu na kira na na saka faruwar abubuwa Biyu zuwa gareni. Ina fita kuwa dayan da na saka ne ya faru Takarda ya mikomin cikin sanyin jiki na saka hannu na karb'a tunkafin na Bude na san me ke ciki ba wannan ne karo na farko, da na taba amsar irin ta ba. Karfin halina Musbahu ya gani yasa ya ce"Kiyi hakuri Hasiya..Kiyi hakuri iya shi kawai zan iya ce miki. Ammh ki sani Salisu ba shi da laifi har ga Allah fin karfinsa akayi" Mirmishi nayi mai ciwo kafin nace"Bakomai Musabahu. Ka gaishe shi Allah ya bashi lafiya" Ya amsa da Ameen kafin yace"Yanzu zamu dauki hanyar kano." Na jinjina kai ina musu fatan Sauka lafiya. Har na shiga Dakin Amma bata Fahimci yanayina ba, ko bud'e takardan ban yi ba. Na turata cikin jakata ta ajiyan karikitai. Na fita tsakar gida na samu Habiba na Hura gawayi zata Damama Amma koko. Sai na Leka dakin Maman Boy nace ta aramin wayarta. Ta dauka ta bani chan wajen bayi naje na saka lambar Adda Fati da na riga na Haddace na kirata ta na Dauka nace"Adda fati Hasiya ce! Ban jira cewarta ba na cigaba da fadin"ki kira Inna talatu kuje ku yi mganar kwaso kayana gidan Salisu. Saboda ya sake ni d'aazu" Ina jin ta fara salati na yanke kiran. Lambar Ramatu na saka na kirata sai kudin suka kare ashe ya shiga sai ga shi ta biyo bayan kiran. Ina Dauka ko cewarta ban jira ba nace"Ramatu shima Salisu ya sake ni" Cikin Firgici Ramatu tace"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Kina ina ne? Ina danne kukan da naji ya tasomin nace"Ina gida. Wayar maman boy ce" Kashe wayar nayi saboda Duhu naji yana mamaye ganina. Ina juyowa muka had'a ido da Kaltume itama matar gidanmu ce tana kallona da alamu ta gama labemin taji duka mganata. Cikin son gulma tace"Ba dai shima Salisun sakin ki ya yi ba? Da kai na amsa mata. Ba na son kwakwazonta yasa na wuce ko kafin na kai Dakin ta fasa kururuwa tana Fadin"Shikenan shima Salisun ya saki Hasiya" Salisu ya saki Hasiya" Wancan ta karba wanchan ta karb'a har kunnen Amma. Ina shiga Dakin tace"Zo nan Hasiya" Ina kauce ma kallonta na zo na zauna agabanta. Cikin kallona tace"Salisu ya sake ki? Kai na gyad'a mata ban yi mgana kawai sai ta ce"Saki nawa ne? Ba musu na mike naje na Dauko Takardan na mikamata Ammi,tayi karatun boko da na addini. Kai tsaye ta warware takardan ta karanta kafin ta ninketa yadda take. Ni ta kallah cikin nazarina kafin tace"Allah yasa haka shi yafi zama alheri gareki damu gabad'aya Hasiya" Ciki ciki na amsa mata da Ameen kafin nace"Na kira Adda Fati,da Ramatu na fad'a musu" Kai Amma ta jinjina min kawai ni kuma sai ma mike na fice. Duk suna Tsakar gida kamar jimamin gaske suke yi na mikama Maman Boy wayarta na juya na koma Daki. Sai na tsiri gyara jakar kayana ina jin abunda ke sukan raina ya na tab'a har kashin bayana. Da gaske kenan abunda mutane ke fad'a a kaina ya tabbata? Tabbas ina da Farar kafa. Sannan zamana ko rab'ar mutane ba alheri ba ne. Salisu da Abubakar sun shud'e daga Duniyata gab'adaya, sun zama Tarihi kamar ma ba'a yi su ba. Sun shud'e saboda ba su ne daman Mahadin kaddaran ki ba HASIYA.!
Chapter 7 · 0% Book details